Na koyar da sama da mutum 300 fasahar kyankyasar kaji  – Injiniya Maiwada

Malam Abubakar Danjuma Maiwada, matashi ne da ya kware a kere-keren na’urori masu amfani da hasken rana, kuma malami ne a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano, a zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilansa na yin bincike da nazari a fannin samar da na’urori masu amfani da hasken rana domin kawo sauyi da ci gaba: […]

Na koyar da sama da mutum 300 fasahar kyankyasar kaji  – Injiniya Maiwada

Malam Abubakar Danjuma Maiwada, matashi ne da ya kware a kere-keren na’urori masu amfani da hasken rana, kuma malami ne a Jami’ar Maitama Sule da ke Kano, a zantawarsa da Aminiya ya bayyana dalilansa na yin bincike da nazari a fannin samar da na’urori masu amfani da hasken rana domin kawo sauyi da ci gaba:

Wane ne Abubakar Maiwada?

Sunana Abubakar Danjuma Maiwada,  ni dan asalin Jihar Katsina ne mazaunin Jihar Kano. Na yi karatun firamare a firamaren BUK , daga nan na tafi Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano na yi karatun karamar sakandare, bayan na gama sai na tafi Makarantar Sakandaren Kimiyya da  ke Dutsinma a Jihar Katsina na kammala sakandare. Na yi digirina na farko a fannin Injiniyan sinadarai (Mechanical Engineering), sannan na yi digiri na biyu a fannin makamashi (Energy Engineering) duk a Jami’ar Bayero da ke Kano. Yanzu haka ni malami ne a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano a Tsangayar Tsare-Tsare da Ci gaban Al’umma (Physical Planning Debelopment and Maintenance Department).

Zuwa yanzu wasu na’urori ka kera?

Na yi kere-kere da dama, kuma ni ma’abocin bincike ne da ci gaban kimiyya a kullum domin in samar da abubuwan ci gaba na zamani. Abubuwan da za su kawo wa al’ummata maslaha da mafita domin su samu saukin rayuwa da ci gaba. A irin haka ne na kera na’urorin da suka hada da akwati mai samar da wutar lantarki ta hasken rana wato sola fawa bos na kuma hada injin kyankyasar kwayaye mai aiki da hasken rana da ake kira sola fawa inkibato, sannan na hada wani abu mai samar da iskar gas na girki daga kashin dabbobi da tsuntsaye wanda ake kira bayogas dajasta, na kuma samar da hanyar noma na zamani wanda ake amfani da makamashi na kimiyya domin sarrafa kansa wanda ake kira noman haidrofonik, sannan na kera wata na’ura da ke samar da tsutsotsi domin su zamo abinci ga kifaye da kaji, wannan na yi ta ce domin amfanin manoma masu kiwon kaji da kifaye, kuma koyaushe ina ci gaba da yin nazari domin kirkiro kayayyaki ko na’urorin da za su kawo ci gaba ga al’ummata da kasa baki daya.

Yaya na’urorin da ka zayyana ke aiki?

Ana jona su da batura, sai ta zuko wuta daga faifan sola da aka daura a saman rufin gida, sannan ta ajiye makamashin lantarkin wutar a cikin batiran sannan ta bada wutar lantarki a lokacin da ake bukata.

Nakan jona talabijin da kwayayen fitila, fanka da na’urar kwamfuta Laptop da wayoyin salula, ita kuma na’urar da ke samar da iskar gas na girki ana samun mazubin kashin mai duhu, saboda ba a son iskar ‘Odygen’ a cikinsa, za a zuba kashin shanu ko kaji ko na mutum a ciki a kulle, a tabbatar an kula da yanayin zafi ko sanyi, a haka zai samar da sinadarin iskar gas na girki da ake kira ‘Methane’ bayan wasu kwanaki.

Sannan na’urar  kyankyasa kuma, ana kiyaye yanayin zafin da za a samar  da yanayin zagayewar iska da yanayin iska mai danshi da kuma motsa kwai, kowane kwai zai kyankyashe a kwanakin da ya dace kwan ya fito da da, ana kula da injin kyankyasar da kada abubuwan da na zayyana su wuce bukata, ana kula da haka ne ta na’urar da na hada da batir ko wutar lantarki ya danganta da yadda ake bukata. Sai kuma ita na’urar da na kirkirara wacce ake shuka iri a cikinta wato ‘Hydroponics’ ana shirya bututu ne a yi shuka, ba tare da kasa ba, wato ba a bukatar kasa, saboda ana samar da abinci ga shukar ta hanyar samarwa shukar abinci daga sinadari.

A nawa da na hada kullum da safe na’urar za ta kunna kanta ta aika ruwa daga tanki zuwa wajen, kuma in ta gama ta kashe kanta. A karshe na’urar da ke samar da tsutsotsi domin abinci ga tsuntsaye da kifi wato ‘maggot debice’ ana saka nama da hodar tsami a girbi tsutsar bayan wasu kwanaki, ana ba kifi da kaji da sauran tsuntsaye saboda tana kunshe da nau’in abinci mai gina jiki da ake bukata domin gina jikin tsuntsaye da kifaye.

Lura da wannan fasaha taka, ka taba koyar da ita ga matasa ’yan uwanka?

Tabbas an taba kirana a Jihar Katsina sau daya na koyar da matasa kyankyasar kwayaye, sannan a Kano mutane kusan 300 sun amfana da ilimin kyankyasar da harkar kiwon zamani. In da gwamnati za ta shigo lamarin da dubban matasa ne za su amfana. Wannan hanya ce da za ta samar wa matasa ayyukan dogaro da kai ta kuma kawo mana ci gaba a zamanance domin samar da wurin koyarwa da kayan aiki zai yi tasiri kwarai saboda a koyar da matasanmu. Sannan idan sun iya a samar musu da kayan sana’a a ba su a kuma tabbatar ba su lalata ko sayar da kayan ba.