‘Na koyi sana’a ne don dogaro da kai’

Aminiya ta zanta da wata mata wadda ta yi fice wajen kirkire-kirkiren kayan kayata daki da kuma adon jiki. Edar Shettima Mustafa wadda ta yi karatun boko har zuwa matakin difiloma, ta yi bayanin dalilinta na ajiye aikin gwamnati da kuma bunkasa fasaharta na kirkira da ta fara tun tana karama. Ga yadda hirar ta […]

‘Na koyi sana’a ne don dogaro da kai’
‘Na koyi sana’a ne don dogaro da kai’

Aminiya ta zanta da wata mata wadda ta yi fice wajen kirkire-kirkiren kayan kayata daki da kuma adon jiki. Edar Shettima Mustafa wadda ta yi karatun boko har zuwa matakin difiloma, ta yi bayanin dalilinta na ajiye aikin gwamnati da kuma bunkasa fasaharta na kirkira da ta fara tun tana karama. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so ki gabatar da kanki?
Sunana Edar Shettima Mustafa, ni ’yar asalin karamar hukumar birnin Maiduguri ce a Jihar Barno, mahaifina Babarbare ne mahaifiyata kuma Shuwa-Arab. A garin Maiduguri na yi karatun firamare da sakandare da kuma difloma. Na yi aiki da ma’aikatar bunkasa ayyukan noma ta jihar, kafin daga bisani na ajiye aiki. Ina da ’ya’ya hudu a yanzu haka biyu sun kammala karatu su na jiran aiki, biyu kuma su na makaranta har yanzu.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa kike yi a wannan sana’a?
Akwai suwaita irinta ’yan sanda da kuma ’yan makaranta wadda nake yin su da keken dinkin saka, akwai kuma suwaita ta musamman mai kauri wanda ke kare jiki kwarai daga sanyi. Za ta yi amfani kwarai a wurare masu yanayin sanyi sosai da kuma mutane da ke da cututtuka irinsu ciwon amosanin jini, da asma, da kuma kansa wadannan rukunnin masu cututtuka ne da ke jin sanyi fiye da mara daya daga cikin cututtukan. Amfani da suwaitar zai samar masu da dumi a jiki kuma an yi shi da inganci na yin hannu fiye da wanda a ke yi da keken saka. Saka suwaita da keken dinki bai da bukatar sai mutum yana da kwarewar dinki saboda ba yanka yadi a ke yi ba, illa dai mutum zai yi setin din karafan keken ne ne gwargwadon girma da yake son kayan ya kasance, a kan kuma yi shi bari biyu ne daga bisani sai a hadesu. Kamar rigan dan sanda da kake gani ya kunshi ’yar karamar jaka da zai sa wani abu a ciki, da safar hannu da kuma hularsa ta sanyi.
Ina kuma yin jakar mata da kuma ribbon wanda mata ke sawa a kai bayan tsifa kafin a yi kitso, nakan yi shi ne da keken dinki sannan sai kuma wajen hade bakinsa sai na yi da hannu. Akwai manyansa da ake yi wa lakabin kariyar gyale, a kan sanya shi ne a kai kafin a yafa gyale yana hana gyalen ya rika sabulewa, na fara yinsu ne bayan kula da rashin ingancin na kasuwa wanda a wani zubin idan ka saye shi daga sawan farko sai ya tsinke, wannan ya sa na fara yinsa.
A bangaren kayan kayata daki kuma akwai kore da ludayi da ake yi musu kawa da duwatsu masu sheki, ga kuma rigunan filo da tumakasa na sawa a farantin abinci da iyayenmu mata suka yi amfani da su tun a da can, wanda zai taimakawa abincin mai gida ya ci gaba da kasancewa da duminsa sannan kuma ya hana zubowar kura ko wani a kan tire din. A kawi  kuma kyalle da a ke shimfidawa a kan teburan alfarma a gida ko a wuraren taro. Nakan yi kuma narkakke da kuma daskararren sabulu gwargwadon irin karfi da ake bukatansa kamar a bangaren wanki, ko wanke-wanke kwanuka na abinci, sai kuma Air Freshener, wato turaren daki na zamani.
Aminiya: Yaushe ki ka fara wannan sana’a?
Na fara wannan sana’a kamar shekara shida da suka gabata don sha’awar kasancewa mai yin  wani abu a gida a maimakon zama haka nan, kodayake, tun ina yarinta a lokacin ina gaban iyayena nake da sha’awar wannan aiki, nakan yi abubuwa kamar su tumakasa da zane-zane haka. Idan mahaifinmu ya  mana dinkin sutura ni sai na bukaci ragowar kyallen na dinka jaka da takalma da shi, wani zubin wasu kan yi sha’awa su bukaci da na musu su biya, amma sai na ce da su bana sayarwa ba ne, daga baya na daina yi bayan na yi nisa a makaranta.
A baya-bayan nan ne ina nan Abuja sai na ga wasu kawayena da ire-iren kayan nan wanda yawanci daga kasar waje suke sayosu kamar daga Ghana da kuma wasu kasashen ketare. Ba ni da wani horo na musamman a kan sana’ar illa dai kirkire-kirkire ne da nake yi kawai, sai na ce masu za mu iya yin wadannan abubuwan a nan ba sai an sawosu daga waje ba. Hakan ya sa na yanke shawarar yin wadannan abubuwa a matsayin sana’a wanda idan na yi amfani da kayanmu na nan gida farashin kayan ba zai kai na wanda suke saya a waje ba.
Aminiya: Kamar wane tsawon lokaci kike yi kafin ki kammala aiki guda?
Kamar wannan kwarya da ke dauke da sunan Allah nakan yi kamar guda biyu a yini saboda yakan zo ne da duwatsunsa a jikin kallen, sai a dauki kyallen gaba daya a lika sauran aikin kuma da ka gani da shi ne ake farawa a na yanka kyallen ne a tsarin rubutu da ake son shi da shi kamar wannan da ke dauke da “Allahu”. Shi ko dayan ana lika duwatsun ne daya bayan daya, wanda a sakamakon hakan yakan dauke ni kamar yi ni uku zuwa hudu kafin na hada guda.
Aminiya: Ya batun farashi kamar kwaryan nan tana kai nawa?
Kamar a kwarya a kwai ta dubu uku, akwai ta dubu uku da dari biyar, akwai ta dubu biyar, akwai ma ta dubu goma, farashinta ya danganci gwargwadon girman kwariyan ne da kuma kimar kayan da aka yi aikinta. Amma dai idan aka sayi kaya da yawa a na rangwame.
Aminiya: Wane irin ci gaba za ki ce wannan sana’a ta kawo miki?
Ni a kashin kaina ya ba ni kwanciyar hankali saboda ya sa na fi karfin bukatuna da na iyali har ma na taimaki dangi, Alhamdulillahi sai godiya. Akwai kuma mutum biyu zuwa uku da nake tare da su wadanda a wasu lokutan idan na samu odar aiki mai yawa nakan gayyace su su zo su sa mini hannu.
Aminiya: Wane buri kike son ki cimma a wannan sana’a?
Ina da burin na ga na bude wata cibiya da zan rika koya wa mata wannan sana’a a matsayin gudunmawata ga al’umma, saboda a bangarenmu na arewa ne ake samun matan aure da suke zaune a gidajensu na aure ba tare da wani abin yi ba musamman ma dai mata wadanda suke Musulmi. A nan arewa ake da tarin mata masu rauni da suka rabu da mazajensu, ko wadanda mazansu suka rasu musamman ma dai a wannan lokaci da aka fuskanci rigingimu iri-iri a baya wanda a sakamakon haka sai ka ga nauyin kula da iyali ya koma a kan mace alhali a wani zubin, sai ta wayi gari ko na magi ba ta da shi.
Aminiya: Shin a yanzu da gwamnati ko wata kungiya mai zaman kanta za ta bukaci ta hada gwiwa da ke wajen cika wannan buri  na ki na horar da mata, za ki amince?
kwarai kuwa, ai ka ga gudunma da nake so na bayar ga al’umma zai samu cika sauki ke nan, ta yadda za a samu waje a zuba kayan aiki da za a rike bai wa mata horo a yayesu, a kuma dau wasu.
Aminiya: Wata matsala da masu sana’o’i irin wannan ke fuskanta shi ne hanyar sayar da kayan bayan an yi, ya al’amarin yake a bangarenki?
A gaskiya ba na samun matsala a wannan fuska saboda duk wadda ta sayi kayana kara tallata mini shi take yi saboda wani zai gani ya yi sha’awa sai a sada ta da ni. Akwai kuma manyan kantuna a nan Abuja da ke sa in yi masu aiki gwargwadon bukatarsu don kayata wurarensu ko kuma sayarwa.
Aminiya: Ya batun kalubale wadanne matsaloli ne kike fuskanta a sana’ar?
kalubale da zan ce na fuskanta shi ne a farko-farkon sana’ar a lokacin da wasu kwawaye za su nemi raunana maka gwiwa su ce ai wannan kayan Fulani ne kaza da kaza, da na bi ta na su da ban kai ga haka ba. Sai kuma a yanzu na matsalar jari mai karfi don bunkasa sana’ar zuwa koyar da wasu kamar yadda nake da buri, wanda a yanzu haka ba zan iya ba.
Aminiya: Ko kina da wani kira ga gwamnati?
Kirana ga gwamnati shi ne ta tallafa mini a wannan al’amarin ta hanyar sama mini babban waje da kayan aiki don ba da horo ga al’umma sannan kuma ta taimaka ta wajen sada mu da kasuwanni duniya, inda za a bukaci kayayyakin da za mu samar sannan a saye su da daraja.