Na kuduri warware matsalolin rayuwar iyali da labarina – Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC

Da farko wace ce Maimuna Idris Sani Beli? An haife ni a shekarar 1983, a Unguwar Galadanchi ta cikin birnin Kano. Na fara karatun zamani a Makarantar Firamare ta Jarƙasa, Kano. Sannan na fara karatun sakandare GGSS kwa, aka cire ni, aka yi mani aure; lokacin ina ’yar shekara 14 a duniya. Daga bisani na […]

Na kuduri warware matsalolin rayuwar iyali da labarina – Gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC

Da farko wace ce Maimuna Idris Sani Beli?

An haife ni a shekarar 1983, a Unguwar Galadanchi ta cikin birnin Kano. Na fara karatun zamani a Makarantar Firamare ta Jarƙasa, Kano. Sannan na fara karatun sakandare GGSS kwa, aka cire ni, aka yi mani aure; lokacin ina ’yar shekara 14 a duniya. Daga bisani na ƙarasa Babbar Sakandare a Makarantar Annur, duk a Kano. Na yi karatun Difiloma a fannin Kimiyyar Wallafe-Wallafe, kamar kuma yadda na haraci wasu kwasa-kwasai daban-daban duk a ɓangaren kwamfuta. Na yi aikin koyarwa na wasu shekaru. A halin yanzu ina da aure da ’ya’ya.

Yaya aka yi kika zama marubuciya? Yaushe kika fara rubutu kuma me ya ja ra’ayinki ga harkar rubutu?

A shekarun ƙuruciyata ni makaranciya ce. Ma’ana, ina yawan karatu iri daban-daban na littattafai da sauransu. To amma bayan na yi aure sai na watsar. Wata rana na halarci Tafsir a lokacin Azumi, bayani ya zo kan lalacewar tarbiyyar yara ta dalilin fina-finan Hausa da littattafan da ake rubutawa na zamani, har aka buga misali da wasu littattafan. Bisa wannan dalilin na nemi littattafan da ke fita a wannan lokaci, sai na tarar da cewa tabbas akwai sakin baki mara dalili a cikinsu. Sai na raya cewa marubuci zai iya aika saƙo ba tare da sakin bakin ba, don haka na gwada. Na fara da littafina mai taken ‘Tun Daga Tushe’ a 2003. Littafin ya shiga kasuwa amma ya sha kashi wajen makaranta, don haka na bai wa kaina aikin tunanin yadda zan yi rubutu wanda zai ja hankali.

A wannan shekarar dai ta 2003 na sake fitar da wani littafin mai suna ‘Uwar ’Ya’ya.’ Daga kansa kuwa na dakata har sai da na shirya sannan na koma duniyar rubutu a shekarar 2009.

Ya zuwa yanzu littattafai nawa kika rubuta kuma wanne ne kika xauka a matsayin gagarabadau cikinsu, wato wanda kika fi ji da shi kuma me ya sa kika zabi wannan littafi?

Na rubuta littattafai guda goma sha ɗaya, kamar haka:

1-Tun Daga Tushe. 2-Uwar ’Ya’ya. 3-Tasirin Sihiri. 4-kyalli Huɗu. 5-Kishina. 6-Zuciya Da kwanji. 7-Goran Duma. 8-Mafarkin Khadija. 9-Na Shiga Aljanna. 10-Rigar Siliki. 11-Gwanin Na Iya.

Kafin na rubuta littafin ‘Gwanin Na Iya’ ina matuƙar alfahari da littafin ‘Goran Duma’ saboda ya yi amo ga wata larura da jama’a ba su mai da hankali kanta ba, wato cutar Sikila (Sickle Cell). Amon nasa kuma ya yi tasiri, ya kuma amfanar. Wato saƙon ya kai fiye da rabin inda nake so ya kai, wannan ya sa na yi alfahari da littafin tun da fage ne da rubutu ne kawai ya kai ni kansa, alhalin da ba ni da masaniya ko kaɗan.

Amma bayan na rubuta ‘Gwanin Na Iya, sai na ji shi ne na yi bajinta a matsayin marubuciya fiye da ‘Goran Duma.’ Dalili, na ɗauki salon marubuci cikin fage, sannan jarumin labarin namiji ne, kuma wanda ya sha gwagwarmya nesa ba kusa ba. Labarin na ɗauke da kalmomi dubu 200 kuma tun daga shafin farko yake riƙe mai karatu har zuwa ƙarshe. Bayan nan yanayina na mace bai fito a cikin labarin ba. Ma’ana, duk da ni maca ce ba a ga ɗabi’un mata tare da tauraron ba, wato rayuwata ta mace ba ta yi tasiri ba a cikin labarin. Wannan ya sa nake jin lallai a littafin ‘Gwanin Na Iya’ na fi yin abin-a-zo-a-gani.

Baya ga rubutun zube, ko kin taba rubuta littattafan waka ko wasan kwaikwayo ko fim?

Waƙa! Idan na ce ban iya waƙa ba, ’yan uwana marubuta sunana zuga ni da cewa don ban gwada ba ne, ai yawanci marubuci na iya rubuta waƙa. Ni kuma na dinga zuguwa, nake ƙoƙarin gwadawa amma ƙarshe sai dai na tsira da zafin kai. Akwai wasan kwaikwayo da nake rubutawa a halin yanzu. Sannan na rubuta daftarin labarin fim da dama, musamman na talabijin da ake tsinkawa yau da kullum amma dai yanzu suke hanyar fita.

Ga shi kin lashe gasar Hikayata ta BBC Hausa, shin yaya haka ta faru? Ko kin taba shiga gasar rubutu ban da wannan?

Na taɓa shiga gasar rubutu ta Makarantar Malam Bambaɗiya, amma wallahi na manta ko ta nawa na zo, na dai haura goma. Amma game da wannan gasar ta Hikayata, a tsorace na shiga, don na kasance cikin wasiwasin in shiga ko in bari? Musamman dayake ni ba ma’abociyar ƙirƙirar gajerun labarai ba ce, amma dai dayake na taɓa wani halartar wani taron kara wa juna sani 2013, na yadda ake rubuta gajeren labarai, wanda kungiyar Mace Mutum ta ɗauki nauyi, sai na ɗauko wancan karatun na yi kasadar gwadawa. Cikin hukuncin Ubangiji kuma aka dace.

Lokacin da aka sanar da ke cewa ke ce kika yi nasarar lashe gasar, yaya kika ji?

Ranar biyu ga wannan watan, kwatsam na sami kiran waya daga BBC. Suka yi mani albishir ɗin cewa na ci gasa kuma wai ni ce ta ɗaya! Duk da cewa na dake mun yi magana da su a natse amma tsakani da Allah dauriya ce kawai. Ko motsi zan yi sai in rika jin idan na yi zan zama ba ni ba, ko kuma a sake kirana a ce mantuwa aka yi, ba ni Maimunar ce ake nufi ba. Haka mamaki da wasi-wasi suka dinga jibgata, har sai da suka sake kirana bisa wani bayanin, sannan na fara farfaɗowa; na yarda ni ɗin ce! Allah na ji farin cikin da ya shiga layin irin wanda ake cewa ban taɓa ji ba. Amma daga bisani na sassauta mamaki, kaɗan ne daga cikin hukuncin Allah. Sai kawai na gode masa na kuma yi farin ciki tare da cewa lokaci ne ya zo da burikan da ke cikin raina zai zama murya ya yi amo mai tasirin da zai kauraye duniya. Domin jigon labarina da ya yi nasarar lashe gasar, yana daga na farkon abin da ke ci mani tuwo a ƙwarya a matsalolin da ke doron duniyar nan.

A takaice ko za ki yi mana bayani game da labarin naki da ya yi nasara a gasar. Me ya ba ki tunanin rubuta shi? Waxanne darussa da sakonni kike son aikawa ga al’umma ta labarin?

Sunan labarin nawa ‘Bai Kai Zuci Ba.’ Labarin yana ƙalubalantar ƙudurin nan da ke cewa ‘ciwon ’ya mace na ’ya mace ne.’ Ba wai rushe ƙudurin ya yi kai tsaye ba amma akwai lauje cikin naɗi. Rubutu ya ba ni aikin warware matsalolin al’umma ba ta hanyar littattafaina ba kawai, har ta hanyar kiran waya da tattaki gidana da ƙaramin sanina ma ya yi yawa kan warware matsalolin, dole na tashi tsaye yawon bincike, wanda ya kai ni ga binciko cewa yawanci matsalolin rayuwa, tarbiya na da tasiri a ciki. Shi ne silar taɓa jigon yadda matan da kishiyoyinsu suka mutu suka bar wa ’ya’ya ko kuma suka fita, suke wasarere da yaran har su yi masu sanadin gurɓacewar tarbiyya.

Yanzu mene ne burinki na gaba dangane da wannan gasa? Ko kina da burin faxaxa labarin zuwa littafi ko fim?

Ban ƙirƙiri wani buri a kan labarin ba, dole sai na ji daga su BBC cewa ina da ‘yancin sarrafa labarin zuwa wani abu daban. Idan ya zama mallakinsu, sai in bar masu abinsu, Allah basshi idan ina da buƙatar sake cewa wani abu a kan jigon sai na ƙirƙiri wani sabon labarin.

Waxanne kalubale kika taba fuskanta ko kuma kike kan fuskanta game da rubutu kuma ta yaya kika fita daga cikinsu ko kike kan shawo kansu a yanzu?

Ni ban cika riƙe abubuwan wahala ba wallahi, don ina fita daga cikinsu sai in manta da su. Amma dai na san littattafaina na farko da suka ƙi kasuwa saboda sun zama kamar wani kaset ɗin wa’azi, sai na fara tunanin yadda zan yi a karanta littattafan nawa ba tare da sakin harshe ba. Shi ne na samo dabarar cika su da azancin sarrafa harshe sannan ina zurfafa bincike idan zan yi rubutun don gudun yawan rubutu kan matsala guda. Dabarata kuwa ta kai ga ci. Bayan haka sai dai matsalar kasuwa, wadda a yanzu muke fuskanta.

Daga karshe ko kina da wasu sakonni ga al’umma ko gwamnati dangane da harkar rubutu?

Gwamnati da al’umma, mu taru mu farfaɗo wa al’ummarmu ɗabi’ar karatu wadda ba su da ita. Su sai dai su yi ta rainawa, rainawar ma na neman ɓacewa. Mutanen gari za su iya bayar da gudunmowarsu wajen ƙarfafa wa ’ya’yansu gwiwa ta hanyar ƙarfafa masu gwiwa kan karance-karance. Masu hali suna iya ɗaukar nauyin sayen littattafan karatu irin na wasan kwaikwayo, rubutun zube da sauransu, su kai makarantunmu a matsayin tasu gudunmowar. Gwamnati kuma ta bayar da nata tallafin ga marubuta ta hanyar shirya gasa irin wannan ko ɗaukar nauyin rubutu mai ma’ana ko ma shirya karrama marubutan da suke yin abin a-zo-a-gani ko kuma shirya masu taron sanin makamar aiki da dai sauransu.