Na nemi mafaka ne a Fadar Bidda daga babana – A’isha Uzoechina
Musuluntar da wata budurwa mai shekara 25 mai suna A’isha Uzoechina da ake kira Charity a baya ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairun bana ya tayar da kura a kasar nan, sakamakon kasancewarta ’yar wani Fasto mai suna Raymond Uzoechina. Uban na A’isha na daya daga cikin jagororin majami’ar Redeem Christain Church of […]

Musuluntar da wata budurwa mai shekara 25 mai suna A’isha Uzoechina da ake kira Charity a baya ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairun bana ya tayar da kura a kasar nan, sakamakon kasancewarta ’yar wani Fasto mai suna Raymond Uzoechina. Uban na A’isha na daya daga cikin jagororin majami’ar Redeem Christain Church of God da ke Madalla a karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Mahaifin ya zargi Mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, da tilasta wa ’yarsa ta musulunta tare da ya boye ta a gidansa domin ya aure ta daga bisani. Wakilinmu ya zanta da budurwar kan lamarin kamar haka:
Aminiya: Za mu so ki gabatar da kanki a takaice.
A’isha: Sunana A’isha Uzoechina wadda a da ake kira Charity Uzoechina. Ni ’yar asalin Jihar Delta ce, shekaruna 25, kuma ni daliba ce a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Bidda.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa kika musulunta?
A’isha: Ina da dalilai masu karfi da suka sa na musulunta, na farko a lokacin da nake Kirista, na fahimci mu da Musulmi muna bautar Allah daya ne. Na biyu tsarin rayuwarsu ta ja hankalina matuka, don kuwa na lura Musulmi mutane ne masu sha’awar taimaka wa ’yan uwansu a kowane hali . Bugu da kari, can in da nake zaune a Abuja ina da kawaye Musulmi da yawa wadanda na dade ina mu’amala da su. Wadannan suna daga cikin hujjojin da suka sa na musulunta.
Aminiya: Da kika musulunta kin sanar da iyayenki?
A’isha: A’a, ban sanar da su ba, saboda ina tsoron mahaifina kan matakin da zai dauka idan ya ji na canja addini. A ranar 15 ga Fabrairun bana na musulunta. Da na zama Musulma, na ji matukar tsoron shaida wa mahaifina.
Aminiya: Wane lokaci ne kika zo fadar Mai martaba Etsu Nupe, kuma mene ne dalilinki na zuwa?
A’isha: Na zo ranar 1 ga watan Maris, kuma babban dalilina na zuwa fadar, shi ne domin Mai martaba ya taimaka mini ya shaida wa mahaifina cewa na canja addini da kuma neman kariya daga duk abin da zai iya samuna sakamakon haka.
Aminiya: Wace hanya kika bi, kika ga Etsu Nupe?
A’isha: Na yi yunkurin ganinsa har sau biyu, amma Allah bai sa na dace ba, sai a karo na uku. Da na samu ganinsa, na yi masa bayani ya ki amincewa da bukatata. Sai ya ce in ba shi lambar wayar babana, na ba shi, ya kira shi, washegari babana ya zo fadar.
Aminiya: Ina babanki yake da zama, kuma mene ne sana’a ko aikinsa?
A’isha: Yana zaune a garin Suleja, amma yana aiki a Madalla, shi Fasto ne a Mijami’ar Christ Chapel Redeem Christian Church.
Aminiya: Da babanki ya zo fadar Etsu Nupe me ya faru?
A’isha: Da farko yayin da suke waya, Etsu Nupe ya shaida masa cewa ’yarka ta musulunta, don haka akwai bukatar ganawa da kai. Da ya zo, sai ya ce ya zo ne yana so ya gan ni. Sai muka kebe wuri daya a ofishin Wambai inda muka gana na wani lokaci. Bayan da muka gama ne aka ce mu tafi gida tare, ni kuma na ce ba zan bi shi ba, saboda ya yi mini barazana yayin da muka kebe cewa zai kai ni wani wuri inda babu wanda zai gan ni, balle in ci gaba da sabon addinina na Musulunci.
Aminiya: Akwai zargin cewa Etsu Nupe ya sa aka kai ki wurinsa da karfin tsiya, gaskiya ne?
A’isha: Na gaya maka cewa babu wanda ya kawo ni nan fadar, ni na zo da kaina. Babu ruwan Etsu Nupe.
Aminiya: To me ya sa kika shigar da kara a Kotun Musulunci?
A’isha: Na je kotun ne saboda na farko babana ba ya son in ci gaba da wannan addini na Musulunci. Na biyu,ya yi wa rayuwata barazana. Don yadda ya yi ta maganganu yana iya kashe ni. Don haka na je kotun neman kariya daga kowace barazanar da zan iya fuskanta. Sannan in samu damar ci gaba da gudanar da harkokin addinina na Musulunci yadda ya kamata.
Aminiya: Idan mahaifinki ya sassauto daga matsayinsa, ya ce zai bari ki gudanar da addininki na Musulunci za ki bi shi?
A’isha: Ba zan bi shi ba.
Aminiya: Me ya sa?
A’isha: Har yanzu ina koyon sabon addinina ne. Idan na koma wurinsa, ba zai bari in ci gaba da Musulunci ba, kuma ba zan sake a cikinsu ba.
Aminiya: Me za ki ce game da azumin Ramadan?
A’isha: A gaskiya ina jin dadin wannan nau’i na ibada da farko na tsorata amma da na fara sai na fahimci babu wahala, na samu komai cikin sauki. Babban abin da ya burge ni shi ne, ’yan uwa suna kara mini gwiwar aikata ayyukan ibada a wannan wata.
Aminiya: Ko kina da wani karin bayanin da za ki yi?
A’isha: kwarai kuwa ina da magana ta gaskiya, ba ni ce Kirista ta farko da ta canza addini zuwa Musulunci ba. Kiristoci na zama Musulmi, Musulmi ma na zama Kiristoci. Ina son mahaifina ya san cewa Etsu Nupe bai cutar da ni ba, kuma ba ya da niyyar hakan. Dalili duk matakan da ya dauka a bayyane suke. Bugu da kari ya dauke ni tamkar ’yarsa da ya haifa. Bai ba ni magani ba, balle ya juya mini kwakwalwa. Ba wanda ya tilasta mini shiga Musulunci, sannan babu wanda ya tilasta mini zuwa fadar Etsu Nupe. Wannan matsalar bai kamata a ce ta kai ga wannan matsayin ba. A gaskiya ban ji dadin yadda aka kururuta lamarin ba, aka hada gaskiya da karya a ciki.
…..Wannan gaskiya ce – Sakataren Masarautar Bidda
Daga Muhammad danladi Ibrahim, Minna
Malam Abdul–Malik Usman shi ne Sakataren Masarautar Bidda. Aminiya ta zanta da shi kan wainar da ake toyawa game da musuluntar A’isha Uzoechina, kamar haka:
Aminiya: Yallabai, ana ta maganganu cewa Mai martaba Etsu Nupe ya boye wata budurwa a gidansa mai suna A’isha, mene ne ke faruwa?
Malam Abdul-Malik: Wannan magana da ake yayatawa karya ce. Abin da ya faru, a ranar 1 ga Maris na bana, A’isha ta je da kawayenta ta ce ta zo ganin Etsu Nupe. Daga baya mun samu bayani daga wurinta cewa ta zo sau biyu, ba ta samu Sarki ba.Ta sanar da Sarki cewar ita daliba ce a Makarantar Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Bidda, an sallame ta daga makarantar, bayan haka ta musulunta. Sai Sarki ya tambaye ta, iyayenta sun sani? Ta ce, a’a ba su sani ba.Ya tambaye ta dalili, sai ta ce tana tsoro, don babanta Fasto ne, ba ta san yadda zai dauki maganar ba, shi ya sa ta zo wurinsa. Ya tambaye ta lambar wayarsa da inda suke zaune ta ce, suna Suleja ne.Ya ba Wambai lambar tare da ba shi umarnin cewa yana bukatar ganinsa. Ranar Juma’a abin ya faru.
Washegari sai baban ya zo wurin Sarki, ya tambaye shi ko ya san A’isha? Ya ce eh, ’yarsa ce. Ya tambaye shi ko tana da matsalar tabin hankali? Ya ce, a’a. Sai ya gaya masa abin da ya faru, ya shaida masa cewa ya tambaye ta, ko ta shaida musu ta musulunta, ta ce a’a. Ta ce tana tsoron matakin da za ka dauka a kanta. Dalilin da ya sa aka kira ka ke nan.
Maganar makaranta, Sarki ya ce zai taimaka don ya ga mene ne dalilin janye ta, saboda haka ya nemi uban ya ba shi mako daya zai tuntubi shugaban makarantar ya ji ta hanyar da zai iya taimakawa, amma maganar canja addini, wannan shi da ita ne, su je su gana. A nan ne uban ya ce, a ba su wuri su gana. Sarki ya ba su izinin ganawa a ofishin Wambai. Da suka dawo, sai Sarki ya ce A’isha ki yi harama ki bi babanki, bayan mako daya ku dawo bisa maganar makaranta. Nan take yarinya ta ce ba za ta bi shi ba. Aka yi ta ba ta magana, ta ce sam. A nan Sarki ya ce masa tunda abin ya zama haka, ya hakura ya dawo bayan mako daya, zai ci gaba da yi mata magana ya ji abin da ake ciki in ya zo maganar makaranta sai ya tafi da ita.Ya ce, to, ya tafi.
Ranar Litinin sai ya dawo, maimakon ranar Juma’a da aka ajiye. Ya zarce kai-tsaye zuwa ofishin Wambai, ya ce ya zo ne ya tafi da A’isha. Sai aka tuna masa maganar da suka yi da Sarki kan makarantar yarinyarsa, ya ce shi fa ’yarsa yake so. Sai Wambai ya aika a je a kira ta. Da aka je sai ta ce su wane ne suka zo nemanta? Aka shaida mata babanta ne. Sai ta ce, a shaida wa baban za ta kwaso kayanta tana nan zuwa. Nan ta saci jiki ta je kotu ta shigar da kara don neman kariya, bayan da ta bayyana halin da ta samu kanta. Kotu ta yarda za ta ba ta kariya. Aka tambaye ta inda babanta yake ta ce yana fada.
Sai aka hada ta da Akawun Kotu da wani mutum ya yi masa rakiya zuwa fada don ba baban sammaci. Daga lokacin ne al’amarin ya fara rikicewa. Baban ya yi fushi, bai karbii takardar sammacin ba. Sai ya rubuta takarda zuwa jami’an tsaro na SSS cewa an sato ’yarsa kuma an kawo wa Sarki, shi kuma ya tilasta ta shiga Musulunci. Kuma ya je ganinta an hana shi.
Muna zaune sai Daraktan SSS na karamar Hukumar Bidda ya zo wurina kan maganar, abin ya daure mini kai don ban san da al’amarin ba. Na tambaya aka ce akwai magana mai kama da haka. Sai na shaida wa Darakta ya je ya ga Sarki. Sarki ya ce ya dawo washegari lokacin yarinyar ba a fada take ba. Kotu ta ba Babban Limamin Bidda Sheikh Adamu Ya Katun kula da ita. Kafin Darakta ya dawo, aka kawo ta fada. Da ya dawo Sarki ya ce da Darakta su je su gana da ita. Bayan sun gana Darakta ya shaida wa Sarki cewa sun gama, yarinya ta koma gidan Limamin Bidda. Tsakanin ranar Alhamis ko Juma’a aka yi wannan. Ranar Litinin, sai ga kira daga daya daga cikin mutanenmu da ke Abuja cewa wani mutum yana magana a wata tashar FM inda yake zargin Etsu Nupe da musuluntar da ’yarsa, kuma ya je ganinta an hana shi, kuma an kira wani a fada ana so a yi masa tambaya, ya kashe wayar kuma an ce Sakatare ne. Me ya sa ka yi haka? Na ce wannan maganar ba da ni ake yi ba da Wambai ne. Haka aka yi ta juya magana, ta yau daban da ta gobe, har zuwa wannan lokaci. Jami’an SSS sun zo sun bayar da bayanai da yarinyar da ma’aikatan tashar FM din sun zo sun ji gaskiyar maganar, duk da haka ba ta canja zane ba. Sai ma aka ce ana ganin Mai Martaba yana son ya aure ta ne. Wannan ya sa muka shiga tsaka mai-wuya. Ganin haka, muka fitar da takardar da ta yi bayanin gaskiyar lamarin a watan Mayu. Bayan nan ne ma’aikatan gidan talabijin na kasa (NTA) suka zo aka yi bayanan da suke bukata. Ba su tsaya a nan ba, suka dangana da makarantar da take aka gano gaskiyar lamarin. Mai Martaba bai da hannu a janye ta daga makarantar. Da aka ji ta bakin yarinyar ta ce a ranar 15 ga watan Fabrairu ne ta zama Musulma, kuma ta zo fada ne don kashin kanta saboda Sarki ya shiga cikin lamarin.
To amma da yake sun dauki matsaya kan lamarin, ganin tsakanin addinin Musulunci da na Kirista ne, ya sa suka kafa hujja da cewa Mai martaba ne ya musuluntar da yarinyar.
Aminiya: An ce kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta shigo cikin lamarin, yaya aka yi?
Malam Abdul-Malik: Mai martaba yana hutu a Landan, Shugaban kungiyar CAN ta kasa, Fasto Ayo Oritsajefor ya kira shi ta waya, ya ce ba ya gida yana hutu. Ya ce masa in ya dawo yana son ganinsa. Sarki na dawowa sai ya nemi shi. Sai ya ce yana Legas. Sarki ya ce na san kana nemana ne a kan maganar A’isha. Ya ce kwarai kuwa, ya yi masa bayanin abin da ya sani har karshe. Bayan haka, Sarki ya gayyaci reshen Jihar Neja na kungiyar zuwa fada, ya sake yi musu bayani. Shugabansu ya yi godiya da karimcin da Sarki ya yi musu, ya ce faduwa ce ta zo daidai da zama, don suna niyyar tuntubarsa game da lamarin. Duk da haka, Sarki ya ce ba zai yi fushi da abin da uban ya yi ta yi ba, zai sake gayyatarsa a ci gaba da magana. Ya ba su lambar uban suka yi alkawarin nemansa. Ranar Litinin suka bugo mini waya cewa sun same shi kuma za su zo ranar Laraba. Mun ji labarin cewa sun shigar da kara kotu inda suke karar Sarki da masarautar, har da tawaga daga hedkwatarsu su ma sun ce suna nan zuwa. Muka ce Allah Ya kawo su lafiya. Suka zo ranar Laraba muka zauna tare da jami’an hukumomin tsaro da na kungiyar Lauyoyi Musulmai ta Najeriya reshen Jihar Neja da wakilan kungiyar Jama’atu Nasril Islam da wakilan kungiyar CAN reshen karamar Hukumar Bidda. Da aka hadu ne Sarki ya yi bayanin komai. Da ya gama kungiyar Kiristoci daga Abuja ta nemi ya bayar da yarinyar. Ya ce ba a hannunsa take ba, kotu ce ta ba shi amanar kula da ita, don haka su je kotu. A karshe suka nemi Sarki ya sa baki yarinya ta bi iyayenta. Da haka aka tashi.
Muna cikin wannan hali sai fadar Shugaban kasa ta tuntubi Gwamnan Neja a kan maganar, saboda kungiyar CAN ta kai maganar cewa Sarki na tsare da ’yar wani Fasto. Shugaban kasa ya tuntubi Gwamna, Gwamna ya tuntubi Sarki, muka tattara bayanai da hujjojin da muke da su muka gabatar wa Gwamna. Ya aika fadar Shugaban kasa.
….. Babu abin da zan ce a yanzu – Fasto Raymond Uzoechina
Daga Adam Umar, Abuja
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Fasto Raymond Uzoechina, mahaifin A’isha Uzoechina kuma limamin cocin Christ Chapel Redeem Christian Church da ke Kwankwashe a karamar Hukumar Suleja. A lokacin da wakilinmu ya isa harabar cocin da ke kusa da otel din Agenda Hotel, a garin Kwankwashe a ranar Lahadin da ta gabata, wasu jami’an cocin sun bukaci ya saurara na dan lokaci kasancewar limamin na gabatar da bishara a lokacin da ya je. Bayan sun kare sai ya karbe shi a gaban wasu daga cikin mabiyansa.
Fasto Raymond Uzoechina, wanda da farko ya nuna haba-haba da wakilinmu, ya nuna matukar bacin ransa tare da bayanai masu zafi, bayan ya fahimci cewa wakilin namu ya fito ne daga kamfanin Media Trust, wanda kwana daya kafin nan jaridar Weekly Trust Ta kamfanin ta buga hirar da ta yi da ’yar Faston, inda a karo na farko ta sanar da duniya cewa ta musulunta ne bisa radin kanta, sabanin bayanin da ke cewa tursasa mata akai kamar yadda wasu kafofin watsa labarai suka nuna.
Mahaifin ya zargi jaridar da yi masa ba daidai ba, inda ya yi barazanar cewa ba zai dauki al’amarin da wasa ba.
Fasto Uzoechina ya ce, tuni ya tuntubi Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) na kasa da Gwamnan Jihar Neja, ya kuma ce ya gana da Shugaban kasa Goodluck Jonathan a kan al’amarin. Haka nan ya ce ya tuntubi lauyoyinsa kan su dauki tsattsauran mataki a kan kamfanin jaridar.
Duk kokarin da wakilinmu ya yi, don shawo kansa don jin ta bakinsa ga bayanan da ’yarsa ta yi, ya ci tura, inda ya ce “Ai a baya, bayan kun yi labarinta na gargade ku da kada ku sake. Ba abin da zan ce a yanzu, sai dai na hada ku da lauyana.”