Na rasa matata da ’ya’ya 5 a Ambaliyar Maiduguri —Goni

Fatima ta ce ba ta yi zaton ita da ’ya’yanta shida za su tsira a ambaliyar ba

Na rasa matata da ’ya’ya 5 a Ambaliyar Maiduguri —Goni

Wani magidanci, Goni Ba Usman, wanda da aka ceto bayan ambaliyar Maiduguri ya bayyana cewa matarsa da ’ya’yansa biyar sun ɓace.

Mutanen da suka aka ceto sun bayyana irin tashin hankalin da suka shiga a sakamakon ambaliyar wadda ita ce muni a shekaru 30 da suka gabata a Maiduguri.

Goni Ba Usman, wanda ke kuka saboda rashin ganin iyalin nasa ya ce zagaye sansanin ’yan gudun hijira kuma ya ga wasu maƙwabtansa, amma bai iyalinsa  ba.

Ya shaida wa ma’ikatan jinƙai a wani sansanin ’yan gudun hijira cewa, “Rabona da ganin matata da ’ya’yana tun 6.30 na safe ranar Talata.

“Da kuje ba ni ruwa, ta yaya zan iya sha, alhali tun da ambaliyar ta taso ban ga iyalina ba?

“Na shiga uku. Mun je Sansanin Babagana Wakil, amma ba mu gan su ba. Na ga wasu maƙwabtana, amma ban ga iyalina ba.

“Innalillahi Wa’inna Ilaihi Rajiun,” yana ta maimaitawa, da fatan zai ga iyalin nasa a raye.

A halin da ake ciki dai ana ci gaba da aikin ceto, bayan ambaliyar wadda ita ta mamaye kashi uku cikin hudu na garin Maiduguri, ta shanye gidaje da asibitoci da kasuwanni da gadoji da makarantu da wuraren inda da cibiyoyin gwamnati da sauransu.

Mutanen da aka yi nasarar cetowa daga wuraren da suka maƙale sun bayyana godiyarsu ga Allah.

Sai dai sun bayyana cewa akwai ragowar mutane da suka maƙale a wasu wurare da ke buƙatar ɗauki.

‘Maƙwabtana na cikin mawuyacin hali’

Malam Abubakar Tijjani, wanda sojoji suka yi nasarar cetowa bayan ya maƙale ya shaida wa wakilinmu cewa ya bar mutane da dama cikin tashin hankali

“Yanzu haka, akwai mutane sama da 50, maza da mata da yara da tsofaffi, da ke zaman mafaka a gidan da na dawo.

“Yawan mutane sai ƙaruwa yake a yayin da akw ci gaba aikin ceto.

“Muna fata da ƙoƙarin da sojoji da sauran mutane ke yi za a ceto ƙarin mutane da ransu.

“Yanzu duk abubuwan amfaninmu da iyalina sun yi mana kaɗan saboda yawan jama’a,” in ji shi.

Ban yi zaton zan rayu ba —Jallo

Shi kuma Ahmed Jallo, ya ce ya bar mutane suna fama da yunwa da ƙishirwa.

“Ban taba tunanin za tsira da raina ba, saboda ruwa ya shanye gidana gaba daya.

“Mun kasa samun ruwan sha. A ƙarshe shagona muka fasa muka cinye duk abin da muka samu a ciki. Har ta kai ga lokacin da babu abin da za mu ci.

“Mutane da dabbobi da yawa sun mutu, gawarsu ke yawo a kan ruwa, tsawon kwanaki ba a taba su ba.

“Na gode wa Allah da Ya kuɓutar da mu, sannan waɗanda , suka kawo mana ɗauki,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ruwan ya yi sauki a unguwannin wazari da Ali Goshe, amma duk da haka ba za a iya zama a cikinsu ba.

Mutane na cikin tashin hankali

Wata malamar makaranta mai suna Jummai, ta cewa sai bayan ambaliyar da kwana uku aka samu ceto iyayenta daga unguwar Gamboru.

“Saukinta shi ne gidanmu bene ne, saboda haka duk ’yan gida suka koma sama. Sai bayan kwanaki biyu aka ceto su,” in ji Malama Jummai.

Na ɗauka mutuwa zan yi da ’ya’yana shida

Fatima Yakubu ta ce ta yi zaton ita da ’ya’yanta shida za su rayu ba bayan dam din  Alau ya rufta sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Fatima sa ke zaune a Maiduguri kusa da madatsar ruwan Alau, ta ce suna barci ne a lokacin da gidansu ya fara cika da ruwa da sanyin safiyar Talata.

“Na farka da karfe 1 na dare lokacin da na ji ruwa a kafafuna.

“Yana karuwa da sauri, kuma na tsorata sosai, na ɗauka mutuwa sa mu yi tare da ’ya’yana, in ji ta.

Ta shaida wa BBC cewa: “Wasu maza suka ji na yi kururuwa kuma suka zo su cece mu. Ina godiya ga Allah.”

yanzu ita da  ’ya’yanta sun samu mafaka a sansanin Bakassi, daya daga cikin cibiyoyi hudu da aka tanada domin dubban daruruwan mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa da su daga gidajensu a wannan makon.

Har zuwa shekarar da ta gabata, wadanda suka tsere daga mayakan Boko Haram ne suka mamaye sansanin.

Mutane na cikin tashin hankali

Wata malamar makaranta mai suna Jummai, ta cewa sai bayan ambaliyar da kwana uku aka samu ceto iyayenta daga unguwar Gamboru.

“Saukinta shi ne gidanmu bene ne, saboda haka duk ’yan gida suka koma sama. Sai bayan kwanaki biyu aka ceto su,” in ji Malama Jummai.

A halin yanzu ana cikin fargabar ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa a sakamakon ambaliyar, wadda ta gurbata ruwan sha.

Gwamna Babagana Zulum ya ce kimanin mutane miliyan daya ne abin ya shafa.

A halin da ake  ciki kuma yunwa na addabar su, bayan sun rasa gidajensu da dukiyoyi a Ambaliyar.

Aikin ceto

A yayin da ake ci gaba da aikin ceto, Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar ta ce an yi nasarar ceto mutane 3,164 a wurare daban-daban Maiduguri.

Shugaban hukumar, Mohammed Barkindo, ya ce unguwanni masu wuyar isa da ake aikin a Maiduguri sun hada da Gamboru, Lagos Street, Abbaganaram, Gwange, Customs, Ferube, 505 Abbagana Terab Housing Estate da sauransu.

Kungiyoyin agaji na rokon a kai ɗauki da kayan agaji, a yayin da mutane ke tururuwa zuwa sansanonin gudun hijira.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano