Na rika yi wa Shata kyauta ne don ya yi wa shugabanmu waka amma ya yi mini waka – Magaji Mainama

“Wa ke sayen nama? Ina mai sayen nama?Alhaji Nafaki Mainama,Ga Alhaji Magaji Mainama.-Ni fa da fa a nan nakan zauna,Ku kun san ban sayen nama,Saboda Nafaki Magaji ke nama.Ku ce wa Magaji Nafaki nagode,” Alhaji Magaji Mainama Nafaki na daya daga cikin wadanda Shata ya yi wa waka, ya bayyana wa Aminiya tarihinsa da dalilin […]

Na rika yi wa Shata kyauta ne don ya yi wa shugabanmu waka amma ya yi mini waka – Magaji Mainama

“Wa ke sayen nama?

Ina mai sayen nama?
Alhaji Nafaki Mainama,
Ga Alhaji Magaji Mainama.
-Ni fa da fa a nan nakan zauna,
Ku kun san ban sayen nama,
Saboda Nafaki Magaji ke nama.
Ku ce wa Magaji Nafaki nagode,”

Alhaji Magaji Mainama Nafaki na daya daga cikin wadanda Shata ya yi wa waka, ya bayyana wa Aminiya tarihinsa da dalilin da ya sa Shata ya yi masa waka:

 

Mene ne takaitaccen tarihinka?
Sunana Musa, amma idan ka zo nemana ka ce kana neman Musa sai ka yi ta yawo ba ka same ni ba, don mutane ba su san ni da Musa ba sai ka ce Alhaji Magaji Mainama Faki. An haife ni a garin Faki da ke karamar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna. Na haura shekara 60 a duniya. Na yi karatun allo a garin kiru da ke Jihar Kano. Daga bisani sai na dawo garin Faki na ci gaba da karatun allo. A nan garinmu na sauka. Ana nan sai Allah Ya kawo tsayawar karatun lokacin da mahaifina ya rasu. Sai na koma kasuwa na kama sana’ar Pawa wacce gadon gidanmu ne. Na yi aure har zuwa matan aure hudu inda na haifi ’ya’ya biyar, amma biyu sun mutu uku suna da rai a yanzu. Gadar sana’ar Pawa na yi tun iyaye da kakanni kuma a 1979 na zo Legas na fara sana’ar Pawa, kuma kafin na zo sai da na zauna a Kaduna da Enugu da Anaca da Shagamu da Minna ta Jihar Neja. Tun kafin a yi kasuwar Mil 12 nake harkar nama.

Shin gaskiya ne Shata ya yi maka waka?
Eh, marigayi Mamman Shata ya yi mini waka kuma wakar ta kayatar sosai don ya wasa ni kuma ya wasa sana’ata ta Pawa. Wakar ta fito da sunana ko’ina an san ni, Sunana ya yadu a duniya, ya je inda ban je ba. Mutane da dama suna tambayata kuma idan na je wani wuri mutane suna nuna ni ana cewa ga Magaji Mainama wanda Shata ya yi wa waka.

Me ya sa Shata ya yi maka waka?
kaddara ce ta sa Shata ya yi mini waka. Ka san duk abin da Allah Ya ce zai faru, sai ya faru. Ni dai ban nemi Shata ya yi mini waka ba, ba kuma na kai kaina don na fito ya gan ni ya yi mini waka ba ne. Yadda abin ya faru shi ne, wata rana Shata ya zo Legas yana wasa sai mutanen suka rika ba shi kudi don ya yi wa shugaban jama’ar garinmu Alhaji Habu Faki waka amma bai yi ba, ni kuwa da na je na yi masa liki, sai wani maroki mai suna Alhaji Sama’ila Nagambo ya ce wa Shata wannan shi ne Alhaji Magaji Mainama Nafaki, sai kawai Shata ya kama yi mini waka. Kuma akwai wani otel da yake sauka idan ya zo nan Mil 12 wasa. Na manta sunan otel din, yana nan bene ne hawa uku. Nakan je gidan na kai masa nama a dakin da ya sauka kafin ya fito wasa. To, ina ganin hakan ma ya taimaka wajen yi mini waka. To ina ganin dalilin wannan maimakon ya yi wa Alhaji Habu waka sai ya yi mini waka.

Me ya sa ka ce kaddara ta sa Shata ya yi maka waka ba kyautar da kake ba shi ba?
Dalili shi ne ban kai masa nama don ya yi mani waka ba, na kai masa ne don ya yi wa wani, amma sai Allah Ya kaddara ni zai yi wa, kamar yadda na yi maka bayani a baya.

Lokacin da Shata ya yi maka waka yaya ka ji a ranka?
Ban ji komai ba saboda tun farko ban nemi ya yi mini wakar ba, kuma abubuwan da na rika yi masa ban yi masa don ya yi mini waka ba. Saboda haka ban ji komai ba a raina. Ko lokacin da na je yi masa kari, na je ne ba da niyar ya yi min waka ba.