‘Na saci yaro ne don in sayar in sayi kayan daki’

Wata mata mai suna A’isha Sani wacce ke dauke da goyon jariri daga Karamar Hukumar Giyade a Jihar Bauchi ta ce ta saci wani yaro dan shekara takwas ne domin ta sayar da shi ta sayi kayan dakinta da gobara ta kone. A’isha ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da manema labarai bayan […]

‘Na saci yaro ne don in sayar in sayi kayan daki’

Wata mata mai suna A’isha Sani wacce ke dauke da goyon jariri daga Karamar Hukumar Giyade a Jihar Bauchi ta ce ta saci wani yaro dan shekara takwas ne domin ta sayar da shi ta sayi kayan dakinta da gobara ta kone.

A’isha ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da manema labarai bayan da ’yan sintiri na Garu Security da ke Bauchi sun kamata da yaron a Unguwar Fadamar Mada da ke cikin garin Bauchi.

“Damuwa ce ta same ni sai zuciya ta debe ni na sace yaron don in je in sayar da shi in sayi kayan daki tunda ba ni da uwa ba ni da uba, kuma mijina ba yi da shi,” inji ta.

A’isha ta ce yaron ta dauke shi ne a cikin gidan makwabtansu da dare, ta ce wannan ne karo na farko da ta taba aikata haka, ta kuma roki ’yan sintirin su yi hakuri su bar ta koma gida.

Shi kuma yaron da aka sato mai suna Nura ya ce yana barci ne a gida da dare sai matar ta je ta dauke shi daga nan bai san inda yake ba sai da ya ga shi a nan.

Shugaban ’yan sintirin Aliyu Ibrahim ya ce yaransu ne da aka tura sintiri suka ga yaron yana kuka, sai yaron ya ce ba mahaifiyarsa ba ce, shi ne suka fara tambayarta shi ne ta ce ta dauko shi ne don ta sayar da shi a Bauchi.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika su ga ’yan sanda don a ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.

Kakain Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Kamal Datti Abubakar ya ce ba ya Bauchi, amma zai bincika domin karin bayani.