Na sadaukar da kyautar Grammy ga matan Afirka – Mawakiya Kidjo
Shahararriyar mawakiya kuma mai rajin kare ’yancin mata Angélikue Kidjo ta sadaukar da kyautar Grammy ga matan Afirka.An gudanar da bikin ne a dakin taro na Staples da ke Birnin Los Angeles da ke kasar Amurka a ranar Litinin.Mawakiyar ’yar kasar Benin ta lashe wannan kyautar ne da wakar ‘Ebe’ da ke cikin kundin wakokinta […]
Shahararriyar mawakiya kuma mai rajin kare ’yancin mata Angélikue Kidjo ta sadaukar da kyautar Grammy ga matan Afirka.
An gudanar da bikin ne a dakin taro na Staples da ke Birnin Los Angeles da ke kasar Amurka a ranar Litinin.
Mawakiyar ’yar kasar Benin ta lashe wannan kyautar ne da wakar ‘Ebe’ da ke cikin kundin wakokinta mai suna ‘Ebe’.
Wannan shi ne karo na biyu da mawakiyar mai kimanin shekara 54 ta lashe kyautar, inda ta lashe kyautar karo na farko a shekarar 2008 da wakarta mai suna ‘Djin-Djin’.
“Na sadaukar da wannan kundin wakokin ga matan Afirka, saboda kyawunsu da kuma juriyarsu.” Mawakiyar ta ce bayan ta karbi kyautar tata.
Kidjo ta shahara ne sakamakon wani shiri da ta yi na ilimantar da mutane a kan illar dumamar yanayi da kuma abubuwan da suka shafi harkokin lafiya.