Na samar wa sama da mutum 15 sana’a – Bala Maigari Jos

Aminiya; A wanen lokaci ne ka fara wannan sana’a ta nika gari, kuma me ya karfafa maka gwiwar rungumar wannan sana’a? Bala Maigari; To,  a takaice dama duk abin da kake ciki dole sai ka samarwa kanka wata sana’a, wadda zaka rika samun taro da sisi, wanda zaka rika gudanar da al’amuranka. Don haka zan […]

Na samar wa sama da mutum 15 sana’a – Bala Maigari Jos

Aminiya; A wanen lokaci ne ka fara wannan sana’a ta nika gari, kuma me ya karfafa maka gwiwar rungumar wannan sana’a?

Bala Maigari; To,  a takaice dama duk abin da kake ciki dole sai ka samarwa kanka wata sana’a, wadda zaka rika samun taro da sisi, wanda zaka rika gudanar da al’amuranka. Don haka zan iya cewa na fara wannan sana’a ne kusan shekara 15 da suka gabata. Kuma na fara wannan sana’a da dan karamin wuri, amma a hankali muna zamanantar da wurin, har muka kai ga wannan bunkasa. Kuma na fara wannan sana’a ce saboda la’akarin da nayi da matsalar wutar lantarki da muke fama da shi a kasar nan, musamman a wancan lokacin.

Mutum ya je ya sayo masara, ya kai inji a nika ya zo ya tankade sannan a tuka a ci. Wani lokaci idan aka kai nika, za a samu babu wutar lantarki, sai a rasa yadda za ayi. Sai naga cewa wannan wata matsala ce da take damun mutane, don haka sai na bude wannan waje, idan aka sami wuta sai mu nika gari da yawa mu ajiye, mutane suna zuwa suna saye. Wato a takaice abin da ya zaburar dani na kama wannan sana’a ke nan. Kuma mun gode Allah domin duk abin da ka gyara shi da kyau, za ka ga mutane sun rungume shi.

Aminiya; Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu wadanne irin nasarori ne ka samu?

Bala Mai Gari; To, dama duk abin da kake yi babban burinka shi ne ya samar maka da muhalli da warware maka matsalar rayuwa da mallakar abubuwan da za su inganta maka abin da kake yi.

Don haka a gaskiya na yi wa Allah godiya kan wannan sana’a. Domin a yanzu ina da ma’aikata sun kai 15, wadanda a wannan wuri ne suke samun abin da suke ciyar da kansu da iyalansu. Sannan kuma mun sami nasarar samarwa mutane ingantatcen gari.

Domin duk wanda ya sayi garinmu zai ga bambanci wajen gyara da tsafta. Saboda matakan da muke dauka wajen fitar da garinmu. Muna da babban ofishinmu a nan kusa da babban masallacin juma’a da ke nan garin Jos. Kuma muna da ofisoshi a kasuwar tumatur da ke nan garin Jos. Kuma muna kai garinmu Bauchi da Nasarawa da Abuja  muna sayarwa. Akwai wanda ya ce ya kai garinmu har kasar Ingila.

Aminiya; Meye babban burinka kan wannan sana’a?

Bala Mai Gari; Ina da burin ganin na  koma wani babban waje, wanda zan sami damar gina manya manyan sito da zan rika sanya masara da garin da muke sarrafawa.

Aminiya; Wannan  kira ne kake da shi zuwa ga jama’a dangane da mahimmancin sana’o’i?

Bala Mai Gari; Sana’a tana samarwa da mutane ayyukan yi. Sana’a tafi aiki domin idan mutum ya kama sana’a zai iya bai wa wani aiki. Mai sana’a yana tanadin gaba ne, mai aiki kuma yana tanadin yanzu ne. Don haka ya kamata jama’a su sani cewa sana’a tafi aikin gwamnati.

Aminiya; Kana da wani kira ko sako zuwa ga gwamnati dangane da tallafawa harkokin sana’o’ a kasar nan?

Bala Mai Gari; Gwamnati ta rika neman shawarwarin masu sana’o’i wajen tallafa masu. Domin rashin neman shawarwarin masu sana’o’i a kan sami matsala wajen sanya ka’idoji masu tsauri wadanda masu sana’o’in suke kasa cikawa. Don haka gwamnati ta rika neman shawarwarin masu sana’o’i da kungiyoyinsu wajen tallafa masu.