Na samu baiwa
Na samu baiwa Wani Basakwace ne ya je ya yi bahaya a jeji, yana sanye da jallabiya. Bayan ya gama sai ya ga babu kashi a kasa. Da ya zo cikin jama’a sai ya ce: “Allah Ya yi mini baiwa!” Aka tambaye shi cewa wace irin baiwa ce, sai ya ce da su: “Wallahi na […]
Na samu baiwa
Wani Basakwace ne ya je ya yi bahaya a jeji, yana sanye da jallabiya. Bayan ya gama sai ya ga babu kashi a kasa. Da ya zo cikin jama’a sai ya ce: “Allah Ya yi mini baiwa!” Aka tambaye shi cewa wace irin baiwa ce, sai ya ce da su: “Wallahi na yi tutu ga fili amma ban gane shi ba.” Ashe kashi yana nan a makale cikin jallabiyar Basakwace, sai daya daga cikin mutanen ya kalli rigarsa ya ce: “Kai ar takwalli, ga tutu nan na biyarka a riga, har za ka raina mana wayo?”
Daga Garba Sabiyola Gashuwa, 07066581437
Ya gano ni
Wani mutun ne da dansa suna cin abinci sai yaron ya ga katon nama a gaban uban, sai ya ce: “Bari na yi wa baba wayo.” Sai ya ce: “Baba malaminmu na Geography ya ce mana haka duniya take zagayawa.” Sai ya zagaya kwanon tuwan, naman ya dawo gabansa. Sai uban ya gane nufinsa, sai ya ce: “Ai malaminku bai fada muku daidai ba, domin sau biyu take zagayawa.” Shi ma sai ya sa hannu ya juya kwanon tuwan, sai yaro ya ce: “Ashe baba ya gano ni.
Daga Nurah Ahmad Gandiroba, 07068907968
Sakamakon rowa
Wani magidanci ne yana cin nama a boye, da ganin matarsa ta fito daga daki sai ya tura naman karkashin benci, ya kama wankin karya saboda kada matarsa ta ga abin da yake ci. Ashe akwai wani kare a bayansa, shi kuma ya samu nama sai da ya cinye duka. Ashe matarsa ta gani, sai da ta tabbatar karen ya cinye sai ta ce masa: “A gama wanki lafiya maigida.” Ya ce: “To, Allah Ya sa.” Yana jawo takarda sai ya ga ba komai, sai ya fara salati.
Daga mai lamba, 07062159736
Agajin lissafi
Wani magidanci ne ya dawo gida sai ya tarar yara suna lissafi, aikin gida da aka ba su a makaranta, lissafi suna cewa: “4+1=5, 4+2=6, 4+3 =7, 4+4, sai suka yi shiru, wato sun manta; sai baban nasu ya ce wa babba a cikinsu: “Yanzu 4+4 ba ka sani ba? Wawa, jaki!” Sai mahaifiyar yaron ta ce: “Alhaji a gaya masu mana, ka san yara.” Sai ya ce: “To, a saurara…” Ya dan karkata hula ya ce: “4+4 amsa biyu ce, in dai ba 40 ba to 44.”
Daga Mudassir Meshayi Ningi