Na samu biyan bukatuna da sana’ar sayar da kayan miya – Murtala

Murtala Muhammad dan garin Sabon garin Yahuza da ke karamar Hukumar batagarawa mai sana’ar sayar da kayan miya ne, ya bayyana sana’ar sayar da kayan miya ta biya masa dukkan bukatunsa na rayuwa: Aminiya: Ta yaya ka samu kanka cikin sana’ar sayar da kayan miya?Murtala: To zan iya cewa koyonta na yi a wajen yayana […]

Na samu biyan bukatuna da sana’ar sayar da kayan miya – Murtala
Na samu biyan bukatuna da sana’ar sayar da kayan miya – Murtala

Murtala Muhammad dan garin Sabon garin Yahuza da ke karamar Hukumar batagarawa mai sana’ar sayar da kayan miya ne, ya bayyana sana’ar sayar da kayan miya ta biya masa dukkan bukatunsa na rayuwa:

Aminiya: Ta yaya ka samu kanka cikin sana’ar sayar da kayan miya?
Murtala: To zan iya cewa koyonta na yi a wajen yayana Malam Lawal kimanin shekara 20 da ta wuce. Ka san mutumin Arewa ba shi da wata sana’ar da ta wuce noma da kiwo. To ita wannan sana’a tana da alaka da noma. Yayana Malam Lawal kamar yadda na gaya maka shi ne wanda ya janyo ni kan wannan sana’a. Amma fa ina so ka sani, rayuwa ta yarinta ka san ana shan daga kafin a aza yaro a kan irin wadannan sana’o’i, ba ma kamar a ce na zama wuri daya ba ne.
Farko na nemi in ki saboda wancan dalili da na gaya maka na kuruciya, amma a hankali da lallashi, wani lokaci kuma har da fada ya sa tun ba ni sha’awar abin har ta fara shiga zuciyata, inda har zuwa yau ana ta bugawa.
Aminiya: To yaya ita wannan sana’a ta sayar da kayan miya take?
Murtala: Hakika sana’a ce ta rufin asiri, domin idan dai har za ka tsare ta, to za ka iya samun komai. Sana’a ce da za ta hada ka da mutane iri-iri. Duk da ribar da ake samu a kanta ba irin wadda wasu sana’o’in ke kawowa ba ce, amma duk da haka akwai rufin asiri.
Aminiya: Yaya kayan yinta suke?
Murtala: To mu dai nan in cefane ko kayan miya, ana nufin tattasai da tumatir, da kabewa da albasa, sai attarugu da kubewa da Alayyafu, sai latus da kabeji da suka shigo daga baya. Amma da mutum ya zo ya ce, a ba shi cefane, to za mu hada masa kayan miya. Wani a sanya masa kabewa, wani kuma ya ce ba ya so. Kuma muna hada wadannan kayan da na ambata maka daidai adadin kudin da mutum ya bayar. Su kuwa kubewa da Alayyahu da attarugu da latas ko kabeji mutum yana sayensu ne daban. Kuma da zarar an hada su da sauran sun shiga layin cefane. Amma kada ka manta ana sayar da kowane daya daga cikin kayan da na lissafa maka daban. Sai dai wani abin sha’awa a nan shi ne, sai dai a ce na sayo tumatir ko tattasai da sauransu daga wajen masu sayar da kayan miya, amma sayan daya ba a cewa an yi cefane.
Aminiya: To yaya kuke samun kayan, ina nufin kai ke nomawa ko kuwa?
Murtala: To ka san ita kasuwa ba ka cewa komai sai kai, dole ne ka yi tarayya da wani. Saboda haka, kayan akwai masu kawo mana muna saye, kuma ko da can haka sana’ar take. Masu nomawa daban; masu sayarwa daban, kuma har yanzu a irin wannan tsarin ake. Wani ci gaban da za a iya cewa an samu a yanzu shi ne, samun masu fataucin kayan daga wasu sassan kasar nan, inda ake noman kayan lambu. A yanzu mun kasu kashi biyu a kan wannan sana’ar, wato mu masu zama waje daya da kuma masu zuwa nemo kayan suna kawo mana.
Aminiya: Ko akwai wata ribar da za ka iya cewa ka samu a wannan sana’ar?
Murtala: Akwai sosai, ka ga tun ina koyo ba ni rasa na kashewa, har ta kai ga na yi gida na yi aure, na sayi abin hawa duk a dalilin wannan sana’a, ashe kuwa na samu kowace irin ribar da ake nema a samu a sana’a. Ga kuma tallafawa da nake yi bakin gwargwado ga wadanda suke nema. Kamar yadda aka koyar da ni ni ma ina koyar da wasu. Ka ga dai a yanzu hakan nan tare nake da dan uwana muna yin sana’ar tare. Ga kuma wasu can da ke yi mini wasu ayyukan inda su ma suke samun abinci da ita. Akwai mai yi mani gyaran kayan ta hanyar fitar da marasa kyau daga ciki da kuma jerawa a cikin kwanuka domin masu bukatar hakan.
Aminiya: Lallai duk inda aka samu nasara to kuma ba a rasa matsala ta nan da can, ko ka fuskanci wadansu matsaloli?
Murtala: E, haka ne. Ba ma kamar ga harkar kasuwanci, kuma kayan da suka kunshi mafi yawansu suna tare da ruwa ne. To mu babbar matsalarmu ita ce, a kawo kaya su dauki wani dan lokaci ba a sayar ba, to a nan matsala take. Da ma an kawo maka wasu kayan da tun kafin ka bude akwai masu nakasu a ciki, misali, timatur za a kawo shi a cikin kwando da an bude sai a taras da wasu sun fara fashewa ko ma sun tsiyaye gaba daya. Amma fa ba wai laifin inda aka zubo shi ba ne, a’a, kafin ya zo inda kake ne hakan ke faruwa. Haka take faruwa ga kowane nau’i ka dauka na kayan. Ga su kuma wadanda suka kawo mana ba kowannensu ke hakuri da daukar irin wannan nauyin ba. Kasan mafi yawan kayan ana kawo mana ne sai mun sayar mu biya duk da cewa ba dukkanmu ba ne ke yin hakan. Wannan na daga ciki, kuma ita ce babbar matsalar wannan sana’a. Sai kuma wani lokaci rashin samun tsayayyar alkibla ga farashinta, domin yau yana iya tashi gobe kuma ya sauko
Aminiya: To me za ka cewa jama’a musamman masu ganin wannan sana’a ta sayar da kayan miya ba ta da wani tasirin a zo a gani?
Murtala: Rashin saninta ne yake sanya su ganin haka. Musamman matasanmu na yanzu, ba su iya rungumar kananan sana’o’i don rufa wa kansu asiri. Kullum tunaninsu ina za su samu ahaha. A nan nake kira na musamman ga matasan su rungumi sana’o’in hannu. Maganar ilmi daban, kuma ma ilmin zai kara taimaka masu wajen gudanar da sana’ar. Allah Ya yi mana jagora.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu