Na samu daukaka a harkar fim ba tare da tallafin wani ubangida ba – Priyanka Chopra

Wace ce Priyanka Chopra?Priyanka Chopra ta kasance daya daga cikin shahararrun ’yan fim mata da suka sama wa kansu suna a duniyar fina-finan Indiya. Baya ga kasancewarta ’yar wasa kuma mawakiya ce da ta fara shahara a wakokin zamani.An haife ta ne a ranar 18 ga watan Yuli na shekarar 1982 a birnin Jamshedpur na […]

Na samu daukaka a harkar fim ba tare da tallafin wani ubangida ba – Priyanka Chopra

Wace ce Priyanka Chopra?
Priyanka Chopra ta kasance daya daga cikin shahararrun ’yan fim mata da suka sama wa kansu suna a duniyar fina-finan Indiya. Baya ga kasancewarta ’yar wasa kuma mawakiya ce da ta fara shahara a wakokin zamani.
An haife ta ne a ranar 18 ga watan Yuli na shekarar 1982 a birnin Jamshedpur na kasar Indiya. Iyayenta dukkansu likitoci ne kuma sojoji ne a rundunar sojan Indiya. Ita ce aka zaba a matsayin mace mafi kyau a duniya a shekarar 2000. Daga bisani ne a shekarar 2002 ta samu kanta cikin masu gudanar da harkar fim, inda ta fito cikin fim din ‘Thamizhan;’ ga shi a yau ta samu nasarar zama ’yar wasa mafi tsada a fina-finan Indiya.
A shekarar 2003, ta fito cikin fim din ‘The Hero,’ daga bisani kuma ta biyo da ‘Andaaz’ wanda da shi ne ta samu kyautar yabo daga mujallar ‘Filmfare.’ A 2004 ma ta samu yabo daga fim din Aitraaz. Haka ma a 2006, ta yi fice da manyan fina-finai, kamar ‘Krrish’ da ‘Don.’
A shekarun baya, a masana’antar fina-fiunan Indiya babu sunan da ake ji sai na wane Khan ko wacce Khan, sai wane Kapoor ko wance Kapoor, to ta yaya aka yi har Priyanka Chopra ta sama wa kanta gurbi a ma’aikatar?
Ni dai na shiga harkar fim ne ba tare da tallafin wani ubangida ba, ba tare da wani ya yi mani jagora ba. Ina alfaharin cewa ni da kashin kaina na yi kokarin keta sansanin ’yan wasa na samu suna. Na ci gasar sarauniyar kyau ta duniya a 2000. Na samu shahara a fim ne a shekarar 2003, da fim din ‘Andaaz.’ A yanzu haka na kwashe sama da shekara goma cikin sana’ar fim kuma na samu nasarori da yawa, amma har yanzu ina da sauran aiki a gabana. A duk lokacin da masu kallon fina-finaina suna nan, to kuwa ina da bukatar in ci gaba da nishadantar da su. Ni ’yar wasa ce kuma na kuduri aniyar ci gaba da kayatar da masu kallona. Wadanda suka kalli fina-finaina na ‘Kaminey’ da ‘7 Khoon Maaf’ da ‘Barfi’ za su shaida haka.
Priyanka mawakiya ce, yaya haka ta faro?
Ban shiga harkar waka ba sai da na shiga makaranta aka koya mani. Ya zuwa yanzu na fitar da faya-fayai guda biyu, ‘In my City’ da kuma ‘Edotic.’ Zan ci gaba da hada harkar fim da kuma rera wakoki. A rayuwata, ba na son in saki wani abu domin kama wani. Ina ganin cewa mu mata za mu iya tarbar kowane kalubale da ya tarbe mana gaba. Ni dai na kuduri aniyar yin haka a fagen nishadantarwa a Indiya.
Bayan harkar fim da waka ko akwai wani fage da Priyanka za ta shiga?
Ina son ka gane cewa harkar fim a Indiya ba abu ne mai sauki ba, haka ma harkar wakar zamani. Ni kaina ban san iya inda zan dosa ba. Ni dai na san ina turzawa kuma zan ci gaba da turzawa. Yanzu dai shekaruna 31 a duniya.