Na samu daukaka ta dalilin waka — Ahmed Shanawa
Ahmed Abubakar Sa’idu, wanda aka fi sani da Ahmed Shanawa ko Baban Chakwai da ke zaune a garin Jos, yana daya daga cikin mawakan Hausa da suke tashe a Arewacin Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya shiga waka da irin daukakar da ya samu a wakar. Ga yadda […]
Ahmed Abubakar Sa’idu, wanda aka fi sani da Ahmed Shanawa ko Baban Chakwai da ke zaune a garin Jos, yana daya daga cikin mawakan Hausa da suke tashe a Arewacin Najeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda ya shiga waka da irin daukakar da ya samu a wakar. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Mene ne takaitatcen tarihin rayuwarka?
Ni dai an haife ni ne sama da shakara 30 da suka gabata, a Unguwar Gangare a nan garin Jos. Na yi makarantar Firamare a wannan unguwa, daga nan na yi makarantar Sakandire ta Islamiyya da ke Bauchi road a nan garin Jos.
- Ganduje ya nada Naburaska mai ba shi shawara a bangaren ‘farfaganda’
- Rikicin Rasha da Ukraine: Birtaniya za ta kara wa NATO sojoji
Ban sami kammalawa a wannan makaranta ba. Na yi makarantun sakandire guda uku kafin na kammala karatuna na sakandire. Kuma na yi karatun addinin Musulunci daidai gwargwado.
Mene ne ya sa ake kira ka da sunan Shanawa da Baban Chakwai?
Abin da ya sa ake kirana da Ahmed Shanawa, shi ne a shekarun baya, wato a lokacin da na fara waka, duk wakar da na yi ina yawan furta kalmar Shanawa. Magana daya da zan yi a cikin wakokina, za ka ji ina cewa ’yan mata da samari Shanawa ko kuma za ka ji ina cewa ni ne mai Shanawa. Haka ne ya sa mutane suka canza mani suna, suna kira na Shanawa.
Ni kuma na duba ne na gano ma’anar kalmar shanawa shi ne, haskawa da cinyewa da kuma burgewa. Daga lokacin na fara tunanin zama dan gaye, ta yadda duk inda zan shiga ko abin da zan yi, zan yi kokari na ga duk inda na shiga, ana cewa wannan Shanawa ne.
Sunan Baban Chakwai kuma, na samo shi ne a wata waka da na yi, mai suna Baby Chakwai. Daga wannan waka ce, mutane suka fara kira na Baban Chakwai.
A wanne lokaci ne ka fara shiga wannan waka?
Na fara shiga harkokin waka da finafinan Hausa ne, a shekara ta 2004 zuwa shekara ta 2005 a nan garin Jos. Tun daga wannan lokaci na fara zuwa wuraren wasan Kalankuwa da wasannin biki. Har Allah Ya sa a shekara ta 2007, aka bude wani Kamfani mai suna 3SP a nan Jos, na fara aiki da wannan kamfani. Kuma asali ba waka na fara yi ba.
Na fara da fitowa a finafinan Hausa ne. Da na ga abin ba zai yiwu ba, sai na koma koyon kida daga baya kuma na zo na koyi waka. Daga nan kuma na zo na fara fitowa a fim tare da ba da umarni.
Kamar wadanne finafinai ne ka fito?
Finafinan da na fito a cikinsu, sun hada da Azal da Matasa da Hanyar Kano da Ban ganb ta ba da Ummul Khairi, kuma duk finafinan kamfanin 3SP ne.
Zuwa yanzu akalla ka yi wakoki kamar guda nawa?
Gaskiya ban san yawan wakokin da na yi ba zuwa yanzu. Saboda na yi wakokin aure da wakokin siyasa da wakokin sarauta da wakokin radin suna da dai sauransu. Sannan kuma na yi wakoki da dama na soyayya da jin dadi.
Wace waka ce ka fara yi, kuma maye ya sa ka yi wannan waka?
Wakar da na fara yi waka ce wadda nake cewa zo ki tallafa mai sona, zo ki tallafa ruhuna. Wannan waka ba ni na yi ta ba, wakar wani mawaki ne da ya kasa hawa, na hau. Daga nan kuma waka ta gaba wadda na fara yi, tawa ta kaina ita ce Zabar zabar zabarin soyayyar ’yan karya, yau ga Ahmed ya sami masoyiya mai kima.
Wannan waka ita ce na fara yi, tawa ta kaina. Kuma dalilin da ya sa na yi wannan waka, shi ne soyayya nake yi da wata yarinya a lokacin, sai aka sami cin Amana wato irin soyayyar karya ta makaranta, a lokacin da nake makarantar sakandire. Wato sai na ga yarinyar kamar ta ci amanata, muka sami matsala sai kuma Allah Ya ba ni wata, shi ne da abin ya yi mani dadi sai na yi wannan waka.
A cikin wakokinka wacce ce Bakandamiyarka?
Gaskiya dukkan wakokina Bakandamaye ne. Amma Bakandamiyata ta farko a cikin wakokina ita ce wadda a ciki nake cewa, ‘A she gaskiya tana da dadi, Makaryaci ba za yi suna ba, ko da ya yi ma, ba za yi tasiri ba. Ni ba gida ni ba mota ba, ba mai tara dukiya masu yawa ba.’ Wannan waka ita ce na fi so a cikin wakokina.
Kuma abin da ya sa na fi son wannan waka shi ne, ita ce ta fara fito da ni duniya aka sanni. Domin duniya ba ta san ni ba, sai a lokacin da na yi wannan waka, a shekara ta 2016. Kuma da wannan waka na fara yin bidiyo.
Yaya kake ganin yanayin yadda harkokin waka ke tafiya, musamman a nan Arewa?
Gaskiya waka a Arewacin Najeriya an sami ci gaba kwarai da gaske. Saboda an sami hanyoyin da wakokin suke saurin shiga zuwa ga al’umma. Za ka yi waka yanzu-yanzun nan cikin minti 5 za ka sake ta, mutum miliyan kamar 5 su samu nan take. Maimakon a da idan ka yi waka kafin mutum 100 su samu sai an ji jiki.
Daga nan garin idan aka saki waka sai an saka a mota a kai wani gari. Sai an sa a jirgi kafin a kai wata kasa wata wakar ma sai ta yi shekara 1 ba ta je wani gurin ba. Amma yanzu cikin minti 5 da dora waka a Internet za ta tafi ko’ina a duniya. Babu shakka wannan wani babban ci gaba ne aka samu kan harkokin waka a Arewa da Najeriya da duniya baki daya.
Mene ne burinka kan wannan waka da kake yi?
Gaskiya ina buri kan wannan waka da nake yi, amma wannan buri na bar shi a zuciya ta, sai dai mutane su gani. Kana da mata da ‘yaya? Ina da mata da ‘yaya 2 duk mata ne, domin na yi aure tun a shekara ta 2016.
Wanne mawaki ne yake burge ka kuma kake kwaikwayon sa?
Gaskiya babu wani mawaki da nake kwakwayo. Ni dai ina kokari duk wani mawaki da yake dan zamani ni ma nakan yi kokari a ci zamanin da ni. Kuma gaskiya kowane mawaki yana burge ni ina kuma da kyakyawar alaka da dukkan mawakan da muke tare da su.
Don haka, gaskiya ba ni da wani mawaki da zan ce shi ne na fi so. Domin ina son dukkan mawaka, abokan sana’a ta kuma ina kaunarsu.
Wace waka ce ka taba ji wadda ka yi sha’awar ina ma kai ne ka yi ta?
Wata waka ce ta yabon Manzon Allah SAW da wani mawaki dan Kano ya yi, wadda yake cewa Madina. Wannan waka ji nake yi, dama a ce ni ne na yi ta.
A duk lokacin da na ji wannan waka, nakan yi kukan dadi. Ina cewa ina ma ni ne na yi wannan waka.
Wadanne irin nasarori ne kake ganin ka samu a wannan harka ta waka?
Gaskiya na sami nasarori da dama. Domin ta dalilin wannan waka, na sami dukiya da arziki mai tarin yawa da daukaka da farin ciki. Komai da na samu tun daga shekara ta 2005, har ya zuwa wannan lokaci, albarkacin waka ne.
Na ga manyan mutane, na ga maza da mata gaskiya na ci riba sosai kan wannan waka.
Kamar wadanne wurare ne ka je ta dalilin wannan waka?
Gaskiya ta sanadin wannan waka ne na fara fita daga cikin wannan gari na Jos. Kuma ta dalilin wannan waka, a nan Najeriya na fara zuwa Adamawa da Kano. Daga nan na je garuwa da dama a Najeriya, duk ta dalilin wannan waka.
Bayan haka na fita har kasashen Nijar da Chadi da Ghana da dai sauransu, duk ta dalilin wannan waka.
Wanne irin kalubale ne kake fuskanta a wannan harka ta waka?
Gaskiya babban kalubalen da nake fuskanta a wannan waka shi ne a duk lokacin da na ji ana kushe wani mawaki ba na jin dadi. Sannan kuma idan na kalli wasu mawaka, suna abin da bai dace ba, bana jin dadi. Wannan shi ne babban kalubalen da ke damuna a wannan harka. Mene ne ya fi damunka a wannan harka ta waka? Abin da ya fi damuna a wannan harka, shi ne na ga an karya dokar addini. Ina son a kowane lokaci na ga ana yin abubuwa da ba su saba wa addini ba a cikin wakokinmu,ta yadda za a kunna wadannan wakoki a ko’ina a gani ba tare da wata damuwa ba.
Mene ne sakonka ga masu wannan harka ta waka da masu sauraro da kallon ku?
Sakona ga mawaka shi ne mu kara zage damtse, mu kara kokari, mu rika bin dokoki mu guji abubuwan da za su bata mana wannan sana’a. Kuma ina yi wa masu sauraro da kallon wakokinmu fatan alheri. Muna rokon a duk lokacin da suka ga, mun yi wani abu wanda ba dai dai ba, su rika yi mana uzuri su bamu shawarwari.