Na samu nasara ba da cuwa-cuwa ba – Priyanka Chopra
Daya daga cikin shahararrun ’yan fim mata na Indiya, Priyanka Chopra ta tabbatar wa duniya cewa ta samu daukaka a duniyar fina-finai ba tare da ta biyo hannun ubangida ko kuma ta hanyar cuwa-cuwa ba. Haka kuma, ta kara da cewa, a yanzu ne ta kara fahimtar duniyar fina-finan Indiya.’Yar wasan, wacce a bana ta […]

Daya daga cikin shahararrun ’yan fim mata na Indiya, Priyanka Chopra ta tabbatar wa duniya cewa ta samu daukaka a duniyar fina-finai ba tare da ta biyo hannun ubangida ko kuma ta hanyar cuwa-cuwa ba. Haka kuma, ta kara da cewa, a yanzu ne ta kara fahimtar duniyar fina-finan Indiya.
’Yar wasan, wacce a bana ta cika shekara 31 a duniya, wacce kuma ta taba cin gasar Sarauniyar Kyau Ta Duniya, ta ce, ba kamar yadda ake tsegumin cewa babu dan fim mace ko namiji da zai samu nasara ko ya rika samu shiga manyan fina-finai ba tare da ya samu daurin gindin ubangida ba, ita ta samu nasara ne bisa sa’a da jajircewa.
Priyanka, wacce ta taka rawa a manyan fina-finai kamar ‘Zanjeer’ da ‘Krrish 3’ da ‘Gunday’ da ‘Mary Kom Biopic,’ ta ce ta fahimci masana’antar fina-finan Indiya (Bollywood) ciki da waje. “Ban taba shiga makarantar koyon wasan kwaikwayo ba kuma ba ni da wata masaniyar yadda ake aikin fim kafin in shiga sana’ar.” Inji ta.
Ta kara da cewa: “Ba ni da ubangida ko saurayi a ma’aikatar fim. Na shiga sana’ar fim ina ’yar shekara 18, amma cikin kankanen lokaci na samu fahimtar al’amuran masana’antar ta fim. Na samu babbar sa’a, inda cikin ’yan shekaru na kai mukamin da ake lissafa ni cikin ’yan fim da ke iya taka kowane matsayi a fim. A yanzu haka, na fito cikin fina-finai mabambanta.” Abin da ta fada wa ’yan jarida ke nan, a lokacin da take bayani game da fina-finanta na ‘Krrish 3’ da ‘Zanjeer.’