Na samu rufin asiri da sana’ar gyaran agogo – Mustapha Usman
Ko za ka bayyana mana tun yaushe ne ka fara wannan sana’a?Kamar yadda na bayyana maka, sunana Mustapha Usman kuma na fara wannan sana’a ta gyaryan agogo, a bakin gwargwado tun ina makarantar allo. Na fara ta ne da karambanin kwance wannan, daure wancan. Da haka dai na fara, domin ba ma sana’ar agogo kawai […]
Ko za ka bayyana mana tun yaushe ne ka fara wannan sana’a?
Kamar yadda na bayyana maka, sunana Mustapha Usman kuma na fara wannan sana’a ta gyaryan agogo, a bakin gwargwado tun ina makarantar allo. Na fara ta ne da karambanin kwance wannan, daure wancan. Da haka dai na fara, domin ba ma sana’ar agogo kawai ba, haka dai gyare-gyare ko wanne bakin gwargwado haka dai ina dan yi, ina tattabawa.
Ka fara dai haka kamar da karambani ke nan kake nufi?
Yauwa, haka dai na fara har Allah Ya sa hanyar cin abincin ke nan, har yau ga shi ta zama sana’a a wurina.
To, kai kuwa mai ya jawo hankalinka har ka tsunduma ga sana’ar gyaran agogo?
To, yin haka shi na ga ya fi zama alheri gare ni, maimakon in tsaya kan zuwa wajen wani dan uwa ko dan siyasa ya taimaka mini ko kuma in ce zan je yin barance ko dai wasu abubuwa haka, har ma ya kawo zargin wasu abubuwa. Na ce kai, tun da dai Allah Ya sa ina da hikimar da zan rika yin abubuwa ko wane iri, shi ne sai na kama wannan sana’ar ta gyaran agogo.
Wannan sana’a kamar ta fi tasiri a Arewacin Najeriya, ga shi a nan Kalaba kudancin kasa kana yin wannan sana’a, shin yaya karbuwar sana’ar take a nan idan aka kwatanta da Arewa?
Kamar da na zo nan kasar Kudu, akwai Hausawanmu suna kawo gyara sannan ma ’yan asalin Kurosriba su ma suna kawowa; sun ma fi kawo gyaran agogon.
Wani zai iya yin mamaki, yaushe ’yan asalin Kurosriba za su damu da gyara agogo, ganin cewa zamani ya sauya, wani ka iya jefar da agogo idan ya lalace ya sayi wani?
Ya danganta da yanayin agogon. Wani idan yana son abinsa, yakan kawo a gyara, wani kuma idan yana ganin yana da wadata sai ya sayi sabo. Ya danganta da yanayin mai abu. Wani kuma idan ba bukatar gyaran yake yi ba sai ya ce ka canja mai inji kawai.
Ta yaya ma kake samun kayan gyaran, kai ma wani gari kake zuw sari ko ta ya kake samun su, ko da su kazo daga Arewa?
Na zo da wasu daga Arewa sai kuma da na zo nan Kalaba sai na tarar musamman Inyamurai suna kawowa sayarwa. Duk abin da nake bukata akwai shi wurinsu, sai in saya.
Wane kalubale ka fuskanta daga lokacin da ka fara wannan sana’a gadan-gadan?
Abin da nake fuskanta ko wasu matsaloli tsakanina da abokan hulda ko jama’a?
Gaya mana na tsakaninka da jama’a.
Tun da na fara sana’ar nan, Alhamdu lillahi. Gaskiya ba wani cin mutunci da na fuskanta da zan ce ga shi ya faru tsakanina da wani, don ya kawo mini gyaran wani abu nasa ya bace, ana ta sa-in-sa har ma wani ya zo ya gane. Gaskiya haka ba ta taba faruwa ba.
Na rayuwa a kan sana’ar fa?
kalubalen rayuwa ai ka san sai dan abin da ba a rasa ba amma dai matsala ta kan wannan gyara, kiyayewa ce ta. Allah idan ka kiyaye kanka da wasu abubuwa sai ka ga Allah Ya kiyaye ka.
Ko kwalliya ta biya kudin sabulunta kuwa tun daga lokacin da ka fara gyaran agogo?
Alhamdu lillahi, kwarai ta ma biya. Kai tun daga alama ma ya ka gani, tun da ga shi kana hira da ni a kan sana’ar. Saboda wannan sana’a tawa, Alhamdu lillahi, ta biya ni.
Kamar yadda ka ce ta rufa maka asiri ko ka fara tunanin neman tallafi matakin karamar hukumarku ko gwamnatin jiha don ka bunkasa sana’ar ka?
To abin ne yana da wuya, idan da za su bayar ai ka san duk mai sana’a irin wannan ta hannu yana bukatar tallafi. Amma idan ka duba kaga abin da ba zai samu ba, sai ka hakura.