Na samu sama da Naira biliyan 9 a 2021 – Davido
Ana ganinsa a matsayin daya daga cikin manyan attajiran mawaka a Najeriya.
Fitaccen mawakin nan na Kudancin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya bayyana abin da ya samu a shekarar 2021 mai karewa.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Intagram ranar Juma’a, mawakin ya ce ya samu zunzurutun kudi har sama da Dalar Amurka miliyan 22, kwatankwacin sama da Naira biliyan tara.
Ya wallafa a shafin cewa, “A shekarar 2022, za mu dada sa iyalanmu su yi kudi. Na sami $22 a bana [2021]…”
Shi kuwa Manajan mawakin, Asa Asika, shi ma ya bazama shafin nasa na Instagram inda ya ce sun sami makudan kudade a shekarar.
“2021 za ta ci gaba da kasancewa shekarar da ba za mu manta da ita ba, mun sami kudi a cikinta sosai,” inji shi.
A watan Nuwamban da ya gabata dai, sunan mawaki Davido ya zama abin tattaunawa a shafukan sada zumunta na zamani lokacin da ya bukaci abokan arzikinsa su tura masa Naira miliyan daya kowannensu, wanda ya ce zai yi amfani da su ne wajen biyan kudin fiton motarsa daga tashar jiragen ruwa.
A cikin kasa da kwana biyu dai, Davido ya tara sama da Naira miliyan 200, inda daga bisani ya kara miliyan 50 a kai, sannan ya sadaukar da su ga gidajen marayu da ke fadin kasar nan.
Matakin dai ya janyo martani a ciki da wajen Najeriya.
Ana ganin Davido dai a matsayin daya daga cikin manyan attajiran mawaka a fadin Najeriya.