Na samu tabbacin an kashe mini ‘ya – Mahaifin ’yar fim Brittany Murphy
Mahaifin ’yar fim din nan ta kasar Amurka, Brittany Murphy ya bayyana cewa ya samo hujjojin da suka tabbatar da cewa diyar tasa ba mutuwar Allah da annabi ta yi ba, kashe ta aka yi.Mahaifin nata, Angelo Bertolotti, wanda ya gudanar da bincike na musamman ta amfani da gashin kanta, ya ce ya samu nasarar […]
Film: Uptown Girls. (2004) Starring: Brittany Murphy Brittany Murphy died 20/12/2009…

Mahaifin ’yar fim din nan ta kasar Amurka, Brittany Murphy ya bayyana cewa ya samo hujjojin da suka tabbatar da cewa diyar tasa ba mutuwar Allah da annabi ta yi ba, kashe ta aka yi.
Mahaifin nata, Angelo Bertolotti, wanda ya gudanar da bincike na musamman ta amfani da gashin kanta, ya ce ya samu nasarar gano munakisar da aka yi wajen kashe ta, inda kuma ya maka hukumar ’yan sanda da kuma likita mai binciken sababin mutuwa na birnin Los Angeles game da batun.
A binciken da aka gudanar, an gano guggubin gubar bera a cikin marigayiyar, wanda haka ya sanya aka fara zargin cewa akwai yiwuwar an ba ta guba ne ta ci ta mutu.
“ ’yata ba ta shaye-shaye, kamar yadda a kullum nake nanatawa. Ba zan huta ba har sai gaskiya ta bayyana, sai na tabbatar da cewa an yi wa Brittany adalci.” Inji Angelo, a yayin da yake bayyana irin kokarin da yake na bankado asirin wadanda suka kashe masa diya.
Ita dai ’yar fim Brittany, a watan Disamba na shekarar 2009 ne aka samu gawarta a gidanta da ke birnin Los Angeles kuma likita ya ba da shaidar cewa ciwon Numoniya ne ya yi sanadiyyar mutuwarta. Tun daga lokacin ne mahaifinta ya fara shakku kuma ya kuduri aniyar bincike, domin gano hakikanin dalilin mutuwar tata.