Na san inda aka boye kudinmu da aka sace – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana matsa kaimi don kwato kudaden Najeriya da aka sace ta hanyar gano bakuna da cibiyoyin kudi da kasashen da aka ajiye wadancan satattun kudin danyen man Najeriya ke ajiye.Shugaban kasar ya bayyana haka ne a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa tana matsa kaimi don kwato kudaden Najeriya da aka sace ta hanyar gano bakuna da cibiyoyin kudi da kasashen da aka ajiye wadancan satattun kudin danyen man Najeriya ke ajiye.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne a fadar Shugaban kasa a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake maraba da wasu ’yan Majalisar Dokokin kasar Amurka a karkashin jagorancin dan majalisa Darrel Issa.
Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Shugaban kasa kan Harkokin Watsa Labarai Mista Femi Adesina, ta ruwaito Buhari yana cewa wasu daga cikin kudin da aka sace an sanya su ne a asusun wasu daidaikun mutane.
Adesina ya ce Shugaban kasa ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa tana gano cibiyoyin kudi da kasashen da suke da hannu a cikin lamarin.
Ya ce, Buhari ya yaba hadin kai da goyon bayan da gwamnatinsa ke samu daga manyan kasashen duniya wajen samar da bayanan sirri don ganowa da kuma kwato dukiyar albarkatun kasa da aka sace.
“Muna samun hadin kai daga manyan kasashen duniya, ciki har da bayar da bayanai kan jiragen ruwa da ke daukar mai daga Najeriya amma su sauya alkibla ko su juye abin da suka dauka a wasu jirage a tsakiyar teku. Wasu kudaden an sanya su a asusun ajiyar wadansu daidaikun jama’a kuma muna gano cibiyoyin kudi da kasashen da lamarin ya shafa.”
Ya kara da cewa: “An ba ni tabbacin cewa idan muka gama samun bayanai, Amurka da sauaran kasashen duniya za su dubi batun da idon rahama.”