Na sanya gasar kwallon kafa ne don samar da zaman lafiya- Aki

Fitaccen jarumin fina-finan Barkwanci Chinedu Ikedieze ya ce ya sanya gasar kwallon kafa a Jiharsa ta Abiya ne don samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar jihar.  Gasar wadda aka kira da ‘Uzuakoli Peace Cup’ ta samu tagomashi a wurin al’ummar jihar, inda suka rika yabawa jarumin sakamakon namijin kokarin da ya yi wajen daukar nauyin […]

Na sanya gasar kwallon kafa ne don samar da zaman lafiya- Aki
Na sanya gasar kwallon kafa ne don samar da zaman lafiya- Aki

Fitaccen jarumin fina-finan Barkwanci Chinedu Ikedieze ya ce ya sanya gasar kwallon kafa a Jiharsa ta Abiya ne don samar da zaman lafiya tsakanin al’ummar jihar. 

Gasar wadda aka kira da ‘Uzuakoli Peace Cup’ ta samu tagomashi a wurin al’ummar jihar, inda suka rika yabawa jarumin sakamakon namijin kokarin da ya yi wajen daukar nauyin gasar.
“Na sanya wannan gasar ne don samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin al’ummata. Na kuma shirya gasar ne a matsayin ayyukan da na shirya zan yi sakamakon hutun wata daya da nake yi.
“Idan jama’a suka yi aiki tare, ko kuma idan suna buga wasa a kulob daya, sukan so junansu, hakan kuma kan sanya a samu zaman lafiya da kaunar juna. Hakan ya sanya na dauki nauyin shirya gasar.” Inji shi. Ya yi alkawarin sake shirya gasar a badi, inda ya ce zai fadada gasar don a samu kulob-kulob masu yawa da za su fafata a gasar.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa