Na sha matsin lamba kan garambawul din majalisata-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi ta fama da matsin lamba yayin da yake kokarin fadada majalisarsa. Yayin da yake jawabi a babban dakin taron da aka karrama shi a garin Abakiliki da ke jihar Ebonyi, shugaban kasa ya ce har sai da ta kai ya ajiye wayarsa don kaucewa kiraye-kirayen jama’a da sakon […]

Na sha matsin lamba kan garambawul din majalisata-Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi ta fama da matsin lamba yayin da yake kokarin fadada majalisarsa.
Yayin da yake jawabi a babban dakin taron da aka karrama shi a garin Abakiliki da ke jihar Ebonyi, shugaban kasa ya ce har sai da ta kai ya ajiye wayarsa don kaucewa kiraye-kirayen jama’a da sakon tes daga mutanen da suke da sha’awa kan batun.
“Ya ce “Na rika yin alkawarin zan yi wa majalisar ministocina garambawul amma sai mutane suka rika tambayata yaushe ne zan yi sauye-sauyen saboda haka na sanya dukkan wayoyina uku a dirowa na kulle. Don duk yadda ka yi ba za ka taba samu na ba ta waya. Dole ka bi ta wajen wanda ke kusa da ni ka yi magana da ni”.