Na shafe fiye da shekara 48 ina sana’ar figar kaji —Garba Adamu
A zantawarsa da Aminiya ya bayyana irin rufin asirin da ke cikinta da kuma fadi-tashin rayuwa da ake fama.
Malam Garba Adamu Dattijo ne da yake sana’ar gyaran kaji a birnin Maiduguri, wanda ya shafe kusan shekara 50 yana wannan sana’a, kuma har ta kai shi ga ya mallaki muhalli nasa na kansa.
A zantawarsa da Aminiya ya bayyana irin rufin asirin da ke cikinta da kuma fadi-tashin rayuwa da ake fama.
- Da sana’ar yankan farce na sauke farali —Abdulkadir
- Kwalin Digiri ba lasisin aiki ba ne – Mai digiri da ke sayar da dankali
Aminiya: Tun yaushe ka fara sana’ar gyaran kaji?
Malam Garba: Gaskiya na fara wannan sana’a ta gyaran kaji tun a shekara ta 1973, ka ga yau kusan shekaru 48 ke nan, kuma na zo nan Maiduguri tun a 1962, domin yin karatun Allo, kuma babu wanda ya koya min wannan sana’a, na ga a wancan lokaci babu wani mai yin ta, sai na ga ya dace in yi wani abu da bayan na tashi daga karatun Allo zai rika kawo min abin kashewa, duk da ka san mafi yawanci almajirai a nan Maiduguri ba ma yin bara.
A haka dai na fara sannu a hankali har wasu suka zo su ma suka fara koyo.
Akwai wadanda ka koya wa sana’ar daga lokacin da ka fara zuwa yanzu?
Na koya wa mutane da yawa da su ma suka dauke ta sana’ar da suke yi, wasu suna nan Maiduguri, wasu suna Kano wasu na Abuja, kai kusan ko’ina a kasar nan ina da wadanda na koya wa wannan sana’a.
Gaskiya suna da yawa ba zan iya tuna yawan wadanda na koya wa wannan sana’a ba.
Wani lokaci sai dai in ga mutum ya zo ya gaishe ni, ya ce shi ne wane da ya koyi sana’a a wajena.
Akwai wadanda sun yi arziki ta dalilin wannan sana’a, wasu kuma suna sayar da kajin da yin kiwon su.
Wanne irin rufin asiri ne a cikinta da kuma kalubalen sana’ar?
Ka ga sana’ar nan da ita na yi aure nake rike da iyalaina, na aurar, ina daukar nauyin karatun ’ya’yana da kuma taimaka wa jama’a.
A yanzu haka ina da ’ya’ya kusan 20 kuma da yawansu su ma sun yi aure duk ta hanyar wannan sana’a.
Ina kuma rike da sauran’yan uwa duk da sana’ar nake biya musu kudin Makaranta muke rufa wa junanmu asiri.
Sannan batun kalubale akwai shi domin wani lokacin mutum zai kawo kajinsa a gyara amma sai wani ya karba a matsayin nasa, wanda mun sha samun irin hakan karshe dai dole sai mun biya, wani kuma yakan yafe.
Idan aka kwatanta da shekarun baya za a iya cewa sana’ar ta fi yanzu ganin a wancan lokaci kusan kai kadai ne kake yin ta. Yaya lamarin yake a yanzu ganin kuna da yawa?
Ai ita wannan sana’a kamar yadda na fada maka a baya Allah Ya sa albarka a cikinta, kusan duk wand aka gani a nan yana wannan sana’a cikin daya ne ko biyu, ko dai a nan ya koya ko kuma namu ne, kuma idan ka duba a yanzu an fi sayen kajin da kuma cin su, to ka ga babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah, domin duk abin da sana’a take wa mutum ta yi mana.
Ganin karamar Sana’a ce masu manyan sana’oi suna iya fitowa wata rana su rasa na cefene. Hakan takan faru da kai?
Gaskiya yana da wahaIa a ce mun fito mun tashi ba a samu abin yin cefane ba, sai dai ka san yanayi na rayuwa, wata rana a samu da yawa wata rana kadan haka da ma rayuwar take don wani lokacin za ka iya gyaran kaji sama da 100 amma wani lokaci sai ka ga da kyar a samu goma, domin ko manyan ’yan kasuwa sukan iya fitowa ka ga ba su yi ciniki ba.
Sai dai ka san sana’ar hannu ba kamar kasuwanci ba ne.
Da wuya dai a fito a ce an rasa yadda za a yi da ikon Allah ana samun abin da za a sa a bakin salati.
Wanne kira kake da shi ga matasa da suka kashe zuciya suna zaman banza?
Zaman kashe wando ba abu ba ne mai kyau, dole ne matasa su tashi tsaye su kama sana’a kada a zauna a majalisa, wannan zamanin ya wuce.
Kamata ya yi kowa ya tashi ya kama sana’a, domin zaman banza ba shi da kyau.
Duk wanda ya tashi Allah zai taimake shi komai kankantar sana’a, a tashi a yi ta akwai samu a cikin ta idan kuwa mutum ya kashe zuciya abokin shawararsa shaidan zai jefa shi ga halaka.
Wacce shawara ko kira kake da shi ga gwamnati?
Kirana a taimaka mana mu masu karamar sana’a don inganta sana’ar saboda da ita muke gudanar da komai na rayuwarmu ba tare mun kashe zuciya ba.
Da fatan gwamnati za ta ji mu, ta taimaka mana.