Na shafe kusan shekara 40 a harkar dambe – Ali Zuma
Fitaccen mai harkar damben gargajiyar nan da ke Abuja, Ali Zuma ya bayyana wa Aminiya yadda ya fara shiga dambe damben gargajiya kusan shekara 40 baya da kuma nasarorin da ya samu: Yaya ka fara harkar damben gargajiya? Ali Zuma: Sunana Ali Zuma, na Bala Shagari na Altine Shehu Kajiji. Ni haifaffen garin Shagari […]
Fitaccen mai harkar damben gargajiyar nan da ke Abuja, Ali Zuma ya bayyana wa Aminiya yadda ya fara shiga dambe damben gargajiya kusan shekara 40 baya da kuma nasarorin da ya samu:
Yaya ka fara harkar damben gargajiya?
Ali Zuma: Sunana Ali Zuma, na Bala Shagari na Altine Shehu Kajiji. Ni haifaffen garin Shagari ne a Jihar Sakkwato, ina da shekara 50 a duniya.
Na je makaranta ce a Sakkwato, ina daukar wa wani dan dambe mai suna Balan Bakoji kaya zuwa gidan dambe; daga nan ni ma sai na fada harkar dambe. Idan maraice ya yi sai in fakaici malamina in tafi gidan dambe ana ba ni ’yan kudi haka. To daga nan sai na ce me zai hana ni ma in fara damben.
Saboda haka sai na je har Legas inda na shekara biyu ina dambe a can, ba tare da ko gidanmu sun san inda nake ba. A lokacin da na dawo Sakkwato, duk wani matashi da ya goge a harkar dambe a Sakkwato ba mai iya buge ni.
Wadanne nasarori ka samu a dambe?
Ali Zuma: Duk wani abu da dan Adam zai samu, Allah Ya hore mini shi a harkar dambe. Na yi damben da na samu Naira dubu 500 bayan na buge wani. Na gina gida na yi aure, na yi motoci na ci na sha kuma har yanzu ina harka ta dalilin dambe. Sunana ya yi shahara sosai a duk fadin Najeriya a fagen dambe.
Zan iya ce maka ka je ko’ina a Najeriya ka tambaya wane ne Ali Zuma? Za a gaya maka. Kai duk wani abu da mutum ka iya samu a duniya to in ka gan ni da shi duk a harkar dambe na same shi. Na hadu da manyan mutanen gwamnati, kamar tsohon Gwamnan Jihar Legas, Janar Buba Marwa, saboda dambe.
Ko kana da wata sana’a ban da dambe?
Ali Zuma: Ba ni da wata sana’a koma bayan dambe. Bayan na yi ritaya daga dambe. Sai aka nada ni a matsayin Kocin ’Yan Damben Gargajiya na Jihar Edo; inda ake biyana kusan Naira dubu 100 a wata. Kuma yanzu haka ni ne Kocin Kasa na ’Yan Damben Gargajiya na Najeriya tun kimanin shekara 11 da suka wuce.
Ko akwai wani abin da ke ci maka tuwo a kwarya a yanzu a harkar dambe?
Ali Zuma: Babban abin bakin cikina duk da yadda muka shahara a dambe, amma har yanzu gwamnati ba ta dauke mu zuwa kasashen waje mu buga dambe ba kamar Nijar. In ka lura kusan dukkan ma’aikatan gwamnati, manyan attajirai kowa na sonmu kuma suna zuwa kallon wasan dambe, amma kash! Har yanzu ba a bai wa sana’ar muhimmanci ba.
Mene ne burinka a wannan harka ta dambe?
Ali Zuma: Idan aka ce an fara kai ’yan dambe kasashen waje domin dambe, to burina a duniya ya cika.
Ta yaya ka fara kafa gidan dambe?
Ali Zuma: A Shagamu ta Jihar Ogun na fara kafa gidan dambe, sai na dawo Kwantagora daga nan sai gida Sakkwato daga nan sai na dawo Tafa, to daga can sai na kafa wannan gidan dambe na Dei-Dei a nan Abuja. Na karanci duk wani sirrin dan dambe da kuma damben kansa.
Me kake nufi da sirrin dambe?
Ali Zuma: Lallai ne dan dambe sai ya rike malamai masu taimaka masa wajen addu’a da asiri domin samun nasara; amma duk riko da malamai da ka yi ko da sun kai 100 ne, duk wani asirinka in dai har ba ka shiri da iyayenka, to wallahi ba in da dan dambe zai kai. Kai duk wata harkar duniya ma lallai ne ka yi riko da iyayenka.
Ko ka san yawan ’yan damben da ke gidanka?
Ali Zuma: Ban san adadinsu ba. 20 na iya zuwa ko 40 ko ma 50, wadansu kuma na iya tafiya.
Wadanne kalubale kake fuskanta a yanzu?
Ali Zuma: Akwai ’yan sa ido wadanda suke ganin kyashin abin da muke samu. A gaskiya muna fama da ’yan uba; sai dai Allah Yana tsare mu. Kuma muna ta addu’a, muna dogara ga Allah. Akwai masu yi mana sharri, amma Allah Ya tsare mu.Ina fata Allah Ya raba ni da dambe lafiya. Kuma duk mai yi shi ma Allah Ya ba shi sa’a Ya taimake shi.
Mene ne kisa a dambe?
Ali Zuma: Abin da ake nufi da wannan shi ne idan ka yi dambe da abokin wasanka ka samu nasara a kansa wato dai ka buge shi ya fadi kasa ko ya dafa kasa, shi ne sai a ce ka yi kisa; ba wai ana nufin kisa na mutuwa ba ne. Idan kuma kuka kara kuka buga aka kasa samun wanda ya buge dan uwansa shi ne sai a ce an yi turmi daya. Sannan idan kuka komo kuka sake kwamawa har alkalin wasa ya raba ku sai a ce an yi turmi biyu. In dai har aka kasa samun wanda ya yi kisa a dambe to sai a ce an yi turmi kaza.
Wane kira gare ka ga gwamnati?
Ali Zuma: Babu wasan da ’yan Najeriya suke matukar kauna kamar wasan dambe, talaka na biyan Naira dubu ya shiga bai ji ciwon kudinsa ba. Don haka ya kamata shugabanninmu su habaka mana harkar dambe ta fi yadda take a yanzu. Kamar hukumomin Nijar sun bunkasa harkar wasanninsu na gargajiya; ba su da wasan da ya fi musu kokawa, amma a nan Najeriya gwamanti ba ta kula da harkar dambe.
Haka ina kira ga masu kudinmu su shiga harkar bunkasa damben gargajiya. Ya kamata gwamnati ta saka shi cikin wasannin kasa (Festibal) da ake yi shekara-shekara. In dai gwamnati ba ta saka hannunta ga kowane al’amari ba to ba ya zuwa ko’ina.
Yaya za ka kwatanta yawan masu cin arziki a gidan dambenka?
Ali Zuma: Akalla mutum dubu suke cin arziki a karkashin wannan sana’a ta dambe a nan gidan dambe na Dei-Dei, musamman a ranar Lahadi. Da masu sana’a da ma’aikata da masu samar da tsaro da sauran jama’a suna samun rufin asiri a nan; kai sun ma fi ni samu daga wannan harkar saboda ni yanzu ba dambatawa nake yi ba.