Na shafe shekara 47 ina sana’ar gwangwan – Baba
Alhaji Baba Lawal mazaunin garin Lafiya fadar Jihar Nasarawa mutum ne da ya kwashe kimanin shekara 47 yana sana’ar gwangwan, kamar yadda shaida wa wakilinmu. Ya bayyana yadda ya fara sana’ar da nasarori da ya cimma: Yaya sana’ar gwangwan take a jihar nan? A gaskiya alhamdulillah ba damuwa a sana’ar. Muna samun na abinci […]
Alhaji Baba Lawal mazaunin garin Lafiya fadar Jihar Nasarawa mutum ne da ya kwashe kimanin shekara 47 yana sana’ar gwangwan, kamar yadda shaida wa wakilinmu. Ya bayyana yadda ya fara sana’ar da nasarori da ya cimma:
Yaya sana’ar gwangwan take a jihar nan?
A gaskiya alhamdulillah ba damuwa a sana’ar. Muna samun na abinci a kullum ta sana’ar. Kuma kamar yadda ka sani muna da kungiyarmu ta kasa baki daya da kuma ta nan Jihar Nasarawa. Muna da shugaba wanda ke kula da harkokinmu da walwalarmu. Shi ma a nan yake zama.
Kamar tan nawa kake sayar wa a kullum?
Da farko dai ka ga kowace tirela tana daukar kimanin tan 30 ne, kuma a nan garin Lafiya kadai muna da sassa sama da 20 kuma muna loda kimanin tan 30 ne a duk mako.
Yaushe ka fara sana’ar?
Na fara sana’ar ce tun 1971. Ka ga idan ka yi lisafi za ga cewa na kwashe kusan shekara 48 ina sanar’ar nan. Kuma ta sana’ar nan ne na auri mata biyu kuma ina biyan bukatun ’ya’yana 7 duka daga ribar da nake samu da yardar Allah.
Kamar nawa kake samu a kullum?
Nakan samu kamar Naira 5,000, kullum kuma a ranar da akwai kasuwa nakan samu fiye da haka.
Kana da yara da ke aiki a karkashinka?
Ai ba zan iya yin komai ni kadai ba. A yanzu ina da yara 3 da ke aiki da ni. Koda yake akwai wadansu abokan sana’ata da ke da yara fiye da haka. Aikin wadannan yara shi ne su je su nemo kayayyakin gwangwan su kawo nan mu saya. Wasu lokuta kuma mu ba su kudi su je su sayo.
Yaya tsarin kayayyakin suke?
Wato yadda muke saya shi ne ka ga kowane kilo Naira 10 yake. Kuma a wasu lokuta nakan samu tirela guda a cike a lokaci guda. Kuma in saya in kuma sayar daga baya in samu nawa ribar da yardar Allah.
Kamar ribar nawa kake samu a tirela guda?
Ka ga babban matsala da ba ni kadai ba ne, har da sauran abokan sana’ata muke, shi ya sa wasu kudade da muke kashewa kafin mu samu ainihin ribarmu suke ciki. Ka ga za mu biya yara da ke nemo mana kayan, mu kuma biya kudin mota idan kayan sun yi yawa da sauransu. Amma a karshe dai alhamdulillah don a takaice ina iya samun riba mai tsoka kuma sirri ne bai kamata in fada ba.
Ko kuna fuskantar barazanar kora daga gwamnati?
A kwanakin baya dai gwamnati ta fada mana mu bar nan mu canja mazauni. Amma a yanzu mun dade ba mu gansu ba. Watakila za su iya zuwa wata rana su ce mu canja mazauni kamar yadda suka saba ko su tausaya mana mu ci gaba da sana’armu.
Wadansu na zargin yaran da ke nemo muku wadannan kaya da satar kayayyakin mutane a gidajensu su kawo muku. Yaya gaskiyar lamarin?
A gaskiya ni dai yarana ba sa satar kayan mutane. Idan wadansu suna yin haka, ni dai nawa ba sa yi. Don kamar yadda na bayyana maka nakan ba su isassun kudi wato hakkinsu, ina kuma gargadinsu su rika sayen duk abin da suka gani cewa kayan gwangwan ne ba kayan mutane da suke amfani da su ba. Kuma ba a ko’ina yarana suke tafiya nemo wadannan kayayyaki ba. Kuma ni kaina ba kowane irin kayan nake saya ba. Abin da ya kama daga janareto da sauransu idan aka kawo min, ba na saya. Amma mun sani wadansu yara suna sato kayan mutane kamar yadda lamarin yake a kowace irin sana’a don ba a rasa batagari. Kuma muna kira a kullum ta kungiyarmu ga duk masu irin wannan hali su daina.