Na shafe shekaru 72 ina waka – Mawakin gargajiya Alin Maliki

Mashahurin mawakin gargajiya na kasar Nijar, Alin Maliki na cikin jerin makada da mawakan da suka halarci bikin wankan sarautar Sarkin Abzinawan Teni-iya (Tenhya), wanda aka gudanar a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Maris 2014, inda ya wake manyan mutanen da ke babar rumfar baki. Don haka wakilin Aminiya ya tattauna da shi, inda […]

Na shafe shekaru 72 ina waka – Mawakin gargajiya Alin Maliki

Mashahurin mawakin gargajiya na kasar Nijar, Alin Maliki na cikin jerin makada da mawakan da suka halarci bikin wankan sarautar Sarkin Abzinawan Teni-iya (Tenhya), wanda aka gudanar a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Maris 2014, inda ya wake manyan mutanen da ke babar rumfar baki. Don haka wakilin Aminiya ya tattauna da shi, inda ya yi bayani kan wakokinsa da kyaututtukan da aka yi masa na ban mamakia tsawon shekaru 72 da ya shafe yana waka.
Wani ma’aikacin gidan Rediyo da Talabijin na kasar Nijar, ORTN, Mamman Sanusi, ya bayyana wa Aminiya cewa, Alin Maliki mashahurin mawaki ne da ake yawan sanya wakokinsa a talabijin. “Kuma asali su biyu ne ke yin wakar, wato da Ali da Maliki, sai Allah Ya yi wa Maliki rasuwa, shi kuwa Ali tun da shi ne jagora sai ya ci gaba da wakarsa, tare da jan  yaransa duk inda za su je  biki,” inji shi.
Su ma yaran Alin Maliki da ke kada masa ganguna da amshin waka, sun bayyana cewa azancin Alin Maliki, sai dai a kwatantan shi da mawakan Najeriya irin su Shata da Narambada. Jin amsar yaransa, sai ya yi caraf ya ce: “Sai dai na rambada da Shata.” Ga dai yadda hirarmu da mawakin ta kasance:
Wane ne Alhaji Alin Maliki?
Yau shekarata dari ba daya a duniya, kuma na shafe shekara saba’in da biyu ina waka. Sannan ni dan gadon gado ne, domin kakana ya yi waka, babana ma mawaki ne.
Rukunin mutanen da yake wa waka:
Na fi wake sarakunan gargajiya amma kwanan nan na wake Shugaban kasar Nijar, Alhaji Muhammadu Issufu, har ma ya yi mini kyautar mota kitika. Ka ganta ma can. Ina ma so in shiga cikinta don a dauki hotona, saboda yau kwananta goma sha daya. Kuma Mataimakinsa, Zilli, na yi masa waka ya ba ni tarakata motar noma.
Me yasa yake ta maimaita wakar Annabi ne kakanta?
Wannan waka ta Tambari Sauro ce, shi jikan Annabi ne. Ya kuma yi mini kyaututtuka kuma ta wurinsa, a wajen Shugaban kasar Nijar aka gayyato ni zuwa bikin wankan sarautar Ahmad Aghali. An ba ni rakumi da Jikka 300 goron gayyata. Kuma inda Ahmad Aghali ne kai ma (dan jarida) in ka tsaya zai ba ka rakumi.
Wace kyauta ta fi ba ka mamaki a rayuwarka?
A gaskiya arna ne suka yi mini babbar kyauta. Arnan noma masu noma dammai. Magajin Sarkin Urafa da na yi masa waka, sai ya ba ni saniya talatin da rakumi biyar da doki a lokaci guda. Sai kuma kyaututtukan da nike samu daga Tambari Sauro da Shugaban kasar Nijar da Sarkin Bugaje Ahmad Aghali.