Na shekara 30 ina rayuwa da facin hanyoyi – Malami Bukkuyum

Malami Bukkuyum dan jihar Zamfara ne, wanda ya shaida wa  Aminiya cewa ya kwashe shekara 30 yana facin hanya, inda yake hako kasa ya cike ramukan da ke manyan tituna kasar nan.Wannan bawan Allah ya fara yin irin wannan aikin ne daga jiharsu ta Zamfara, amma ya wuce har zuwa kudancin kasar nan, misali, garurruwan […]

Na shekara 30 ina rayuwa da facin hanyoyi – Malami Bukkuyum
Na shekara 30 ina rayuwa da facin hanyoyi – Malami Bukkuyum

Malami Bukkuyum dan jihar Zamfara ne, wanda ya shaida wa  Aminiya cewa ya kwashe shekara 30 yana facin hanya, inda yake hako kasa ya cike ramukan da ke manyan tituna kasar nan.
Wannan bawan Allah ya fara yin irin wannan aikin ne daga jiharsu ta Zamfara, amma ya wuce har zuwa kudancin kasar nan, misali, garurruwan Jebba da Alata da ke jihar Oyo. Aminiya ta yi kicibis da shi ne a lokaci ya yi zango a kauyen Dauda da ke cikin karamar hukumar Gurara a jihar Neja, inda yake gudanar da wannan aiki.
 Malami Bukkuyum Zamfara, ya ce ya shafe shekaru talatin yana wannan aiki, wanda da farko shi kadai yake yi, amma dalilin samun amfani da yake yi, ya sa yana da mutane  biyar da yake jagoranta wajen gudanar da wannan aiki na cike ramukan da suke kan tituna.
 Malami ya ce ba da rani kadai yake yin wanna aiki ba. Domin idan ya yi shuka yakan fito ya ci gaba da wannan aiki nasa domin ya samu abin  sayen taki, daga kuma sai ya dawo ya nufi wata hanyar da ya ji labari ba ta da kyau. Ya ce ya kan samu labarin hanyar da ta fi lalacewa ne a wurin mutanen gari, sai  ya tafi wurin ya rika cike ramuka masu ababen hawa kuma su rika taimaka masa da kudi.
 Malami Bukkuyum ya ce, wannan ne karo na farko da ya zo wannan hanya da ta yi matukar lalewa, watau hanyar Suleja zuwa Minna, wacce ta shige har babban birnin tarayya Abuja.
 A dangane da samun amfani kuwa, ya fadi cewa, ta wanna aiki ya samu ya yi aure, yana da mata da ‘ya’ya bakwai. Kuma abin da yake samu yana kamawa nN daga naira dubu biyu zuwa Naira dubu hudu a rana.
 Ya ce direbobi da fasinjoji ne suke ba shi daga Naira hamsin zuwa sama, har a wani lokaci ana tsayawa a ba su Naira  dubu daya. Sai dai ya bayyana cewa, manyan mutane masu wucewa a guje ana yi musu jiniya ba su taba ba su ko kobo ba, balle su ce an gaishe ku.
 Malami ya  gode wa Allah da masu tuki, don kamar yadda ya ce,a tsawon wannan lokacin bai taba samun hadari ba. Ya kara da cewa, suna yin dabarar sanya jajeyen riguna, sannan suna dasa jajeyen tutoci a gefen tituna don zama alama ga masu ababen hawa ta yadda tun daga nesa masu ababen hawa za su san ana gyaran hanya a gaba, sai su rage gudu.
 Wannan bawan Allah ya ci gaba da cewa, ganin yana samun amfani ne ya sa wadansu mutanen kauyensu su ke binsa domin su ma su amfana. Inda suke rarrabuwa tsakaninsu, shi  kuma Malami yake tsayawa yana lura da yadda sauran suke yin aikin.
 Ya ci gaba da cewa, suna yin aikin ne daga safe zuwa yamma, sannan sai su je su huta sai kuma gobe, domin aiki ne mai gajiyarwa matuka.
Da Aminya ta tambaye shi ko yana son ganin an gyara titunan kasar nan ganin cewa ta nan ne yake samun na abinci, sai ya ce yana matukar son ganin an gyara tituna, sai dai ya yi nuni da cewa ko an gyara hanyoyin sai  an samu inda za a samu ramuka.
Masu lura da yadda al’amura ke gudana na ganin wannan lalacewar tituna bai rasa nasaba da yawan motocin kaukar kaya da ke bin hanyoyin tunda  jirgin kasa ba sa zirga-zirga kamar da, sannan kuma ba a yin magudanan ruwa a gefen titunan, kuma hukumomi ba sa gyaran titunan  tun lokacin da rami yake karama har sai ya zama wagege.