Na shekara 44 ina sana’ar yankan farce – Mamman Dokayal
Malam Muhammadu Mamman Dokayal, dattijo ne mai shekara 70 da yake yawon sana’ar yankan farce.Ya ce, ya zauna garuruwan jihohin Anambra da Bayelsa kuma ba zai taba mancewa da kudin da ya samu a Anaca wata shekara ya je gida Dokayal da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi da Naira dubu 4 da 500. […]
Malam Muhammadu Mamman Dokayal, dattijo ne mai shekara 70 da yake yawon sana’ar yankan farce.Ya ce, ya zauna garuruwan jihohin Anambra da Bayelsa kuma ba zai taba mancewa da kudin da ya samu a Anaca wata shekara ya je gida Dokayal da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi da Naira dubu 4 da 500. Ya ce bayyana wa Aminiya cewa bana shekararsa 44 yana wannan sana’a:
Aminiya: Mai ya kawo ka Kalaba?
Muhammadu Mamman: Sana’ar yankan farce.
Aminiya: Yaushe ka fara wannan sana’a ta yankan farce?
Muhamamdu Mamman: Tun Janar Yakubu Gowon yana Shugaban Kasa, an yi Yakin Basasa an gama, na shiga garin Anaca muka je Anaca gidan Sarkin Hausawan Anaca muka zauna a nan muka yi aiki muka dawo lokacin Murtala Ramat Muhammed, ya yi mulki na ci gaba da yankan farce har zuwa wannan lokaci da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo karo na biyu bayan mulkin soja da ya yi. Tun daga Gowon zuwa Buhari nake wannan sana’a ban daina ba.
Aminiya: Mai ya jawo hankalinka kake sana’ar yankan farce?
Muhammad Mamman: Eh abin da ya jawo hankalina nake wannan sana’a a nan Kalaba na zo neman kudi ne kuma ranar Talata nake son komawa gida wurin iyalina a can Bauchi. Da na zo neman kudi na duba na ga yankan farce ya fiye mini to shi ne sai na kama.
Aminiya: A wace shekara ka fara sana’ar yankan farce?
Muhammadu Mamman: A shekarar da nayi aure na haifi dana Dahiru daga nan na fara, kiamar shekara 44 .
Aminiya: Tsawon wadannan shekaru kana yankan farce ko kwalliya ta biya kudin sabulu?
Mahammdu Mamman: Ta biya! Ta biya! Kwalliya ta biya kudin sabulu, don har yanzu ina cin abin da na samu a Anaca, yana nan har yanzu da sauransa.
Aminiya: Da yake ka shafe shekara 44 kana yankan farce ko ka taba yi wa daya ko wasu daga cikin manyan ’yan siyasa ko masu mulki yankan farce?
Muhammadu Mamman: A’a ban taba yi wa kowa yankan farce ba a cikin shugabanni da manya ba. Amma akwai uwargidana ita tana siyasa ita ce ma Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta Toro.
Aminiya: Ka ce kwalliya ta biya kudin sabulu wani zai yi tunanin tunda shekaru sun mika kamata ya yi ka hakura a koma gefe a ci abin da aka tara kana da yunkurin haka?
Muhammadu Mamman: Nakan ga dan yawon da nake yi ina dan kokarin nan saboda jikina ya dan washe tunda ina da lafiya, ba zan zauna a gida ba sai dai yanzu idan na koma gida zan hakura in kama noma.
Aminiya: Yanzu idan ka koma me za ka yi ?
Muhammadu Mamman: Idan na koma gida ai ni manomi ne, ina noman gero da dawa da kuma tumatir da waken soya da wake.
Aminiya: Wato za ka ajiye yankan farce ka rungumi noma?
Muhammadu Mamman: Eh, zan rungumi noma gadan-gadan.
Aminiya: Za ka iya tuna ranar da kayi wa wani yankan farce ka samu alherin da ba za ka taba mancewa ba?
Muhammadu Mamman: Wanda ba zan taba mantawa ba akwai shekarar da na yi yankan farce a Anaca na dawo da kudi gida har Naira dubu 4 da 500 na sayi akuya, akuyar nan ta yadu har na sayi saniya tana can a ruga yanzu haka.