‘Na shekara 7 ina sayar da naman kare a Kano’

Wani mutum da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke shi yana yanka karnuka yana soya namansu yana sayarwa a Kano, mai suna Uche Aled Mbu ya tabbatar da cewa ya shafe shekaru bakwai cur yana sana’ar sayar da soyayyen naman karen tare da farfasunsa yana sayarwa.Uche Mbu wanda dakarun na HIsbah suka kama tare […]

‘Na shekara 7 ina sayar da naman kare a Kano’

Wani mutum da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke shi yana yanka karnuka yana soya namansu yana sayarwa a Kano, mai suna Uche Aled Mbu ya tabbatar da cewa ya shafe shekaru bakwai cur yana sana’ar sayar da soyayyen naman karen tare da farfasunsa yana sayarwa.
Uche Mbu wanda dakarun na HIsbah suka kama tare da sauran karnukan da bai yanka su ba da kuma irin naman karen da suka kama shi yana gyara wa kafin ya soya, ya bayyana wa ‘yan jarida a farfajiyar hukumar ta Hisbah cewa, ya san da cewa jihar tana aiki da dokokin Shari’a amma bai san cewa sayarwa da cin naman kare ya saba wa dokar jihar ba.
Ya ce shi haifaffen Sabon Garin Kano ne, inda galibin bakin kabilu suke da zama. Ya kara da cewa. “Yaran
Hausawa ne suke kawo min karnunkan ina saya ina yankawa kuma ‘yan kabilunmu ne suke saya, sai dai su masu sayar min ba s  cin naman Karen.”
Mbu ya kara da cewa, ‘yansanda ne suka fara cafke shi yana gyara naman karen a lokacin da ake gudanar da aikin tsaftar muhalli na wata-wata, suka kai shi kotu aka ci tararsa. Daga nan ne kuma ‘yansanda suka danka shi ga ‘yan Hisbah don ya fuskanci tuhumarsu.
Mutumin kuma ya bayyana nadamarsa. Ya ce, “daga yanzu na gane kuskurena kuma na yi
alkawarin zan sauya wata sana’ar a maimakon ta sayar da naman kare.”
A yayin da Babban Daraktan hukumar ta Hisbah, Alhaji Abba Sa’idu Sufi yake jawabi ga ‘yan jarida, ya ce suna ci gaba da bincike a kan lamarin. Ya ce za su ja kunnensa ko su zartar da hukuncin da ya dace a kansa.
Haka nan ya yi kira ga mutane da su kai rahoton duk wanda suka gani yana yanka kare yana sayarwa a jihar. Ya kara da cewa za su sanya jami’ansu su shiga cikin lunguna da kasuwanni don kama masu aikata wannan aikin.