Na shirya biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 — Gwamnan Kebbi
NLC ta ce gwamnan shi ne mafi soyuwa a wurin ma’aikata a duk fadin Nijeriya.
Gwamna Nasiru Idris na Jihar Kebbi ya ce a shirye yake ya soma biyan ma’aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin karɓar baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) reshen jihar.
- An ba iyalan DPO ɗin da aka harbe N1m su soma rage raɗaɗi
- Yadda aka daƙile shirinmu na sayar da buhun siminti N3,500 — BUA
Da yake jawabi a Fadar Gwamnatin da ke Birnin Kebbi, Gwamnan ya yi Allah wadai da masu yaɗa jita-jitar cewa gwamnatinsa ba za ta biya sabon mafi ƙarancin albashin ba.
Ya yi bayanin cewa, la’akari da riƙo da duk wani tanadi na doka mai tsari, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen inganta rayuwar mutanen Kebbi.
Sai dai a cewar gwamnan, “ita kanta Gwamnatin Tarayya da ta sahale wa sabon albashin mafi ƙaranci ba ta soma aiwatar da dokar ba har sai ta kammala shimfiɗa duk wasu tsare-tsare.”
Nasiru ya yi ma’aikata alƙawarin cewa zai soma biyan sabon albashin mafi ƙaranci da zarar an kammala fitar da tsare-tsaren aiwatarwa.
“A shirye muke. Ƙungiyar Ƙwadago da gwamnatina za su zauna domin fitar da tsare-tsare masu inganci wajen aiwatar da dokar sabon albashin.”
Ya ƙara da cewa, har yanzu N500 kacal gwamnatinsa ke cirewa daga albashin ma’aikatan duk shekara a matsayin haraji wanda doka ta tanadar.
“Idan aka lissafa abin da muke cirewa daga albashin ma’aikatan gaba ɗaya bai wuce Naira miliyan 11 ba a shekara.”
A nasa ɓangaren, Shugaban NLC na jihar, Kwamared Murtala Usman, ya ce sun ziyarci gwamnan ne domin jinjina masa kasancewar shi ne mafi soyuwa a wurin ma’aikata a duk cikin gwamnonin Nijeriya.