Na taba gargadin Zakzaky game da tare titi – Shaikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa sai da ya gargadi shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky a kan hadarin da ke cikin tare kan titi lokacin muzahararsu. Dokta Ahmadu Gumi0 ya kuma zargi ’yan Shi’ar da gudanar da  gwamnatinsu daban a shekara kusan 40 da suka […]

Na taba gargadin Zakzaky game da tare titi – Shaikh Gumi
Na taba gargadin Zakzaky game da tare titi – Shaikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa sai da ya gargadi shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim Zakzaky a kan hadarin da ke cikin tare kan titi lokacin muzahararsu.

Dokta Ahmadu Gumi0 ya kuma zargi ’yan Shi’ar da gudanar da  gwamnatinsu daban a shekara kusan 40 da suka yi.
Da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna, Shaikh Gumi ya ce ’yan Shi’a sun dade suna koyon faretin soja da lakantar dabarun yaki.
“Suna tafiyar da gwamnatinsu daban da gwamnatin kasa. ’Yan Shi’a ba su yarda da Gwamnatin Najeriya ba kuma ga shi kungiya ce da ba ta da rajista. Suna ganin sun fi karfin bin dokar kasa, sannan suna samun kudin shiga daga kasar waje,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Tsohon Shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa ya fada min irin yawan makaman da aka shigo da su daga kasashen waje, inda ya ambaci kasar Iran da cewa tana samar wa ’yan Shi’a makamai.Rikicin ’yan Shi’a da sojoji, Allah ne Ya amshi addu’armu cewa kada a sake kirkiro da sabuwar Boko Haram. Wannan ya taimaka wajen karya manufar kungiyar wajen cimma nufinsu.”
Dokta Gumi ya ce “Sai da na aika wa Zakzaky da wasika kusan shekara daya da ta wuce, inda na gargade shi a kan tare titi a lokacin tattakinsu zuwa Zariya, inda mabiyansa ke tafiya da kafa zuwa Zariya daga sassan kasar nan amma ya ki saurarena.”
Malamin ya ce Arewa za ta ci gaba da ci baya, muddin ba a kawar da da akidun Shi’a da Boko Haram ba.