Na taba yi wa Shata kida ya jefar da abin magana – Sasuwai Makadin Shata
Kalangu wanda aka fi sanin tasirinsa a wajen wasan mahauta da wasan fage na samari da ’yan mata, ya zamo babban abin da ya tallafa wa Shata a rayuwarsa ta wakoki inda har Shatan ya kai kalangu Fada maimakon makadan Fada da aka sani. Alhaji Sa’idu Sasuwai na daya daga cikin makadan da Shata ya […]

Kalangu wanda aka fi sanin tasirinsa a wajen wasan mahauta da wasan fage na samari da ’yan mata, ya zamo babban abin da ya tallafa wa Shata a rayuwarsa ta wakoki inda har Shatan ya kai kalangu Fada maimakon makadan Fada da aka sani. Alhaji Sa’idu Sasuwai na daya daga cikin makadan da Shata ya yi zamani da su, ta hanyar sarrafa kalangu. Aminiya ta tattaunawa da Sasuwai a garin Katsina a Gidan Kayan Tarihi da Al’adu lokacin wani wasa da Sanusi Mamman Shata ya gabatar kwanakin baya:
Aminiya: Za mu so jin cikkaken sunanka da yadda kuka hadu da Shata har ka shiga cikin makadansa.
Sasuwai: To, sunana Alhaji Sa’idu, amma sunan da aka fi sanina da shi a duniya wanda nake ganin ba a samu mai irinsa ba shi ne, Sasuwai. Kakata ce kuma ta sanya mini wannan suna, kuma ban san dalilin da ya sa ta sanya min wannan suna ba. An kuma haife ni ne a garin Jos, Jihar Filato. Abin da ya hada ni da Shata shi ne, idan ya je Jos gidanmu gidan kakana Sarkin Kida yake sauka. dakinsa na nan cikin gida.
Aminiya: Ke nan kai mutumin Jos ne?
Sasuwai: Eh! Amma iyayena mutanen kasar Kano ne.
Aminiya: Ka yi gadon kida ke nan?
Sasuwai: Babana Inuwa Bahago, shaharren makadin mahauta ne da sauran wasanni da ake yi na wancan lokaci. Lokacin muna yara idan Sahat ya zo ni ake aike in kai masa abinci. Kuma tun daga wancan lokaci yake kaunata. In na zo da ’yan uwa sai ya dauko kwabbai haka sababbi ya ba ni. Sai ya ce wa Babana “Ga dan gidana.” Har ta kai ga na yi wayo ina ’yan kade-kade na ’yan mata. To kawai wata rana da ya zo sai ya ce, “Bari in tafi da wannan. Sai babana ya ce masa ai dama Muhammadu danka ne. Shi ne muka tashi zuwa Bauchi sai Damaturu zuwa Maiduguri. To da muka dawo Funtuwa zan tafi gida sai ya ce in na je gida Baba ya ba ni kalangu in taho da shi domin kuntukuru nake kadawa a lokacin. To tun daga wancan lokacin sai na fara bin su iyayen gidana su Alhaji Kuntuku su Galadima Rumtum su Mani da sauransu har Allah Ya sa na koya. Kuma ko a wancan lokacin ni dan gata ne a wajensu, domin dukkansu yaran Shatan babu wanda ba ya sona.
Aminiya: Za ka iya tuna ranar da ka fara yi masa kidi?
Sasuwai: Eh, zan tuna ranar da na fara daukar kalangu na yi kida a Maiduguri. Akwai wani Kwamishinan ’Yan sanda dan Alhaji Sabo Ringim lokacin yana Maiduguri, za a dauka masa a rikoda sai (Shata) ya ce Alhaji Kuntuku ya ba ni kalangun. To a lokacin Shata in ya yi maka haka da ido muna jin tsoro. Sai ya ce, “Babu komai daina kallon idona.” Shi ne na ci gaba da kida a wannan rana. Wato da Shata ya dube mu a wannan lokaci mun san akwai magana, duk wanda yake bin Shata in ya waiwaya ya kalle ka ka san manufa ba sai yayi magana ba.
Aminiya: Da wakar wa ka fara kidan?
Sasuwai: Wakar Alhaji Ibrahim Babankowa, wani Kwamishinan ’yan sanda ne dan gidan Alhaji Sabo Ringim.
Aminiya: Kana kamar yaya a wancan lokaci?
Sasuwai: To ina dai dan saurayi haka, amma lokacin ni wasan kwallo ne ya fi daukar mini hankali. Ka san mu ’yan Jos akwai mu da wasan kwallo. To in na koma gida sai Babana ya dauki bulala ya kora ni in koma saboda na wuce kwanaki bakwai da na ce zan yi in koma. Da na ga Ummaru Ba’ale (ya rasu) ya zo, to sai Babana ya ce maza in dauko kayana mu tafi, sai Funtuwa
Aminiya: Acikin yawace-yawacen da kuka yi da Shata ko akwai wani kidan da za ka ce ka yi wa Shata da ya zuga shi har ya ji wani abu daban?
Sasuwai: Wanda na sani, akwai wata rana na dauki kalangu na girgiza shi har ya jefar da makarafon (abin magana) a wajen wakar Bakandamiya. Lokacin ina jin yarinta, na ja kidan ya yi sama sai ya yi wuf ya tashi har ya jefar da makarafon din da ke hannunsa ya ce da lokacin da yake cikin yarinta ne ya same ni da mun zama shaidanu. Ya ce, in sassauta kidan kuma a wakar Bakandamiya ce hakan ya faru.
Aminiya: To kai ne ka kirkiro kidan?

Sasuwai: Eh to! Kidan Bakandamiya yana da yawa, ba ni mantawa a otel din Palace na Funtuwa ni na juya wannan kidan, ni kuma na dauko wannan kida ne daga wajen wani makadin ’yan dambe na kuma dauko shi da dadewa ina kuma so in sanya shi a cikin kidan amma ina tsoron kada a samu kuskure, to sai a wannan otel. Ina daukowa sai kawai na ji yace, “eh! eh!!, ya yi!” Sai ya mike inda ya jefar da abin maganar ya tafi yana takawa daidai yana murmushi. To bayan an tashi daga wannan wasa sai ya ce, kada in je in kwanta domin za a yi dauka don kada in manta da wannan kidan, na ce ba zan manta ba amma ya sa sai dai a yi wannan dauka.
Aminiya: Jama’a suna maganganu a kan Shata, wasu su ce Ibilishi ne ko ma aljani, kai da ka zauna tare da shi yaya ka fahimce shi?
Sasuwai: Ni ina kukan masu yin bayani kan Shata. Mun sani kauna ce ke sa mutun ya rika tarihin mutum, amma ni ina fata masu bada tarihin Shata don Allah su daina siffanta shi da ba mutun ba ne ko a rika fadin abin da ba a yi da su ba. Mafi yawan abubuwan da wasu ke cewa a kansa karairayi ne kawai. Amma wallahi duk abin da ka ji na fada maka a kan Shata an yi da ni ne, domin ba ni fadin abin da na san ba a yi da ni ba. Misali in na tafi gida in aka yi wani abu ai ka ga ban sani ba, saboda haka masu ba da tarihin Shata su daina fadin abubuwan da ba a yi da su ba ko ba su da cikakkiyar masaniya a kan abin da suke fadi domin ba a yi da su ba. A kuma sani tarihin Shata daji ne, amma wata baiwa ce da Allah Ya ba shi. Wasu ma har cewa suke yi wai lokacin da aka haife shi an ji kida daga sama, to wa ya ji kidan ko wa ya yi kidan? Kuma yaya za ka siffanta wanda ka sani ka san ’ya’yansa ko iyayensa da sauransu sannan ka ce masa shi ba mutum ba ne?
Aminiya: To amma kuma marokinsa yana cewa, “Mai suffa ta mutane mai tada ta aljannu…
Sasuwai: Yauwa! Kamar yadda Alhaji Tsangaya yake cewa, ai wannan kirari ne. Hakika yana yin wani abu na waibuwa da za ka yi mamakinsa. Wani abin idan ya yi sai dai ka yi kallo ka yi dariya ko ka yi shiru. Amma yadda ake juya shi a mayar da shi kamar ba mutum ba, ina fata masu yin wannan za su bari. Yana dai da wata baiwar da ba kowane maroki ko mawaki ke da irinta ba, misali yanzu kuna zaune tare da shi in ya sabi babbar rigarsa zai ce ina Adamisayawa? (Yadda yake kiranmu ke nan) sai tafiya kawai ba tare da an shirya ko an yi bankwana ba. Kuma duk wanda ya ce maka Shata yana da wani malami ko bokan da yake ce masa ya yi, ko ya bar wani abu karyata shi nan take domin babu.
Aminiya: Akwai inda shi da kansa yake cewa duk irin yadda ka ga Shata a yanzu kana iya juyowa ka same shi ya canza…
Sasuwai: Eh, yana da wannan, dalilin da ya sa na ce maka wani lokaci yana da waibuwa don kana zaune tare da shi zai ba ka mamaki. Wani lokaci za ka gan shi yana zaune shi kadai yana kallon wani abu wanda kai da ka ga yanayin ka san abin da yake kallon ba na kusa ba ne. In ma ka gaishe shi ka ga ya daga hannu wuce kawai kada ka tsaya, amma kuma wani lokacin za ka same shi cikin nishadi.
Aminiya: Ko ku makadan nasa akwai wani abin da kuke yi masa wanda shi ma sai dai ya gani babu zato kamar misalin irin kidan da ka yi?
Sasuwai: Eh to, su ’yan amshi mu ne a gabansu saboda waka ko sabuwa zai yi kalmarta kamar sau biyu ko uku wadda hakan ya nuna ita ce amshin. Mu kuwa yana buda baki mun san inda za mu nufa da kidan ba sai ya ce wani abu ba.
Aminiya: A tsawon tarayyarka da shi ko akwai wani abu da ka gani a gare shi wanda har yanzu yana daure maka kai?
Sasuwai: Abin al’ajabin da ya taba yi wanda na gani, akwai lokacin da ya taba ce mana in yana barcin gaskiya (idanunsa duka a rufe) kada a zo inda yake. Dalili shi ne, kai nan ke ganin barcin yake yi amma a wannan lokacin ba barcin ba ne, sai dai in ka ga yana irin barcin zomaye (rabin ido a bude) to wannan lokacin ne yake barcin da ni da kai muke yin irinsa. Akwai wani lokaci da Iro kanensa, Shata ya shimfida katifa a tsakar gida yana kwance shi kuma Iron zai sauko daga gidan sama (bene) sai ya ga wasu mutane su hudu jikinsu duk gashi sun zagaye Shata, sai Iron ya taho wai ya tayar da Shata don ganin abin da ke faruwa, ai bai kai gare shi ba, nan ya fadi sumamme jini na zubowa daga hancinsa, shi kuma Alhajin bai sani ba har sai da gari ya yi sha safiya ta yi, Uwargidan Shata ta fito ta ga halin da Iro yake ciki, sai bayan da aka samu ya farfado sannan Shata ya farka ya tambayi abin da ke faruwa. Iro ya ba shi labari, sai ya ce, “Ai na gaya muku in ina barci ku bar zuwa inda nake.” To na san an yi wannan domin ina nan Funtuwa haka ta faru
Aminiya: Wane dadi ne ka ji da har yanzu ba ka manta da shi ba a tarayyarku da Shata?
Sasuwai: Dadin da na ji, na farko a nan Katsina, Allah Ya jikansa da gafara Alhaji Sani Audi muna kida a otel din Sa’i (Nasara Club) sai ya dakatar da Shata ya ce, zai rage masa aiki domin zai kai ni Makka a shekarar. Sani Audi ya fara kai ni aikin Hajji ka ga wannan dadi ba zan taba mantawa da shi ba. Bayan haka, shi kana Shata a duk lokacin da za ni ganin gida yakan dauki manyan riguna irin na sarakuna ya kawo biyu ko uku ya ce in kai wa mahaifina. Kadan ne daga cikin abubuwan da ban mantawa da su.
Aminiya: Ko akwai wani gurbi da kake ganin Shata ya bari wanda zai yi wuyar cikewa?
Sasuwai: To, ko kai yanzu dubi dansa da ya haifa sai dai ya kwatanta waka irin tasa amma maimaita waka irin ta Shata akwai wahala. Kuma batun cewa wai in ya mutu wasu wakokinsa za su bace wannan wata sharholiya ce da wasu ke cewa kawai, amma duk wakar da ya yi aka dauka tana nan sai dai in ba ka ajiye ba, ko ka nema za ka ce ta bace. Akwai wasu wakokin da mutane da yawa ba su taba jin irinsu ba kuma suna nan hannu wadanda suke da su, domin ko ni nan ina da wakokinsa sun fi dubu. Batun mawaka a yanzu dai sai a ce babu su sai dai na zamani wadanda babu wani shaukin da suke kawowa wadanda ake yi wa wakar, mawakan na sosai sai nadiran-nadiran ba a cewa babu baki daya, amma mayar da irin su Shata da wuya yanzu.