‘Na taba yin gyaran farce aka biya ni Naira dubu 50’

Aminiya ta samu ganawa da wani matashi mai gyaran farce a Kaduna, inda ya yi karin haske game da sana’ar da kuma irin nasarorin da ya samu, da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?Da farko dai sunana Surajo Idris, an haife ni a Sabon Garin Argungu […]

‘Na taba yin gyaran farce aka biya ni Naira dubu 50’
‘Na taba yin gyaran farce aka biya ni Naira dubu 50’

Aminiya ta samu ganawa da wani matashi mai gyaran farce a Kaduna, inda ya yi karin haske game da sana’ar da kuma irin nasarorin da ya samu, da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihinka?
Da farko dai sunana Surajo Idris, an haife ni a Sabon Garin Argungu da ke Jihar Kebbi a shekarar 1985. A gaskiya na fara sana’ar yankan farce ne tun a shekarar 2000 kuma na koye ta ne daga wani mutum da ake kira Abdullahi Zahiri da ke zaune a Zariya.
Aminiya: Kamar me ye ya ja hankalinka zuwa wannan sana’ar?
A lokacin da na koyi sana’ar ina karatu ne. A lokacin ba wata sana’ar yi. Idan na ce zan yi kasuwanci zai hana ni karatu. Ita ko wannan sana’ar a kodayaushe za ka iya fita ka je ka nemi na abinci ka dawo. Da farko ba mun damu da mu tara abin duniya ba ne, muna yi ne domin mu dauki nauyin karatunmu kawai.
Aminiya: Kamar ka kai wane mataki na karatu?
Na yi karatun Islamiyya dai dai gwargwado. Har ila yau, a karatun boko na tsaya ne daga matakin sakandare.
Aminiya: Ta wace hanya kake tsaftace kayan aikinka?
A gaskiya a yanzu dai galibin wadanda nake wa aiki suna da nasu. Kodayake, nawa kayan aikin a kullum kafin in baro gida ina wanke su da magunguna kamar ruwan Dettol da Spirit da sauransu. Kuma duk lokacin da zan yi wa mutum zan wanke da ruwan Spirit, hakazalika, idan na kammala.
Aminiya: Bayan yankan farce akwai wata sana’ar da kake yi?
A’a, wannan ita ce sana’a da nake yi kawai.
Aminiya: Meye gaskiyar batun da ake cewa manyan mutane kawai kake wa yankan farce?
A gaskiya ina yi wa manyan mutane aiki daidai gwargwado. Hakazalika, ina yi wa sauran mutane.
Aminiya: Kamar nawa kake cajan manyan mutane?
A gaskiya ba ni da wani kayyadadjen farashi ga manyan mutane. Amma sauran mutane marasa karfi kamar ni, ina karbar Naira 100 ne kawai.
Aminiya: Kamar misalin nawa ne mayan mutane suke biyanka?
Akwai wanda duk lokacin da na yanke masa zai ba ni Naira dubu biyu. Akwai masu ba ni Naira dubu biyar, kai har zuwa Naira dubu 10.
Aminiya: Ko akwai biyan da aka taba yi maka da ba za ka manta da shi ba?
Eh, na taba yi wa, Daraktan Tsare-Tsare na tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, gyaran farce, inda bayan na kammala ya dauki Naira dubu 50 ya ba ni. Baya ga wannan kuma ya yi mini alherai da dama wadanda ba na iya lissafawa.
Aminiya: Bayan shi akwai wasu manyan mutane da ka taba wa gyara kuma ba za ka manta da su ba?
Eh, akwai Alhaji Garzali Mai Motoci wanda shi ne mutumin farko da ya yi mini kyautar Naira dubu 10 bayan na yi masa gyara. Da irinsu Alhaji Sani Pilot da Alhaji Sule Aliyu da kuma Alhaji Lawal Mijinyawa. Har ila yau, a bangaren mata akwai Hajiya Sa’adatu Abakwa da sauransu.
Aminiya: Ko akwai wani kalubale da kake fuskanta ta bangaren sana’arka?
Gaskiya sai dai hamdalah.
Aminiya: Ba ka taba tunanin sauya sana’a ba?
A’a, saboda ko da aiki za a daukeni na gwamnati idan dai don a biya ni Naira dubu 50 ne a wata, gaskiya ba na bukata.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu albarkacin wannan sana’ar?
Gaskiya sai son barka. Da wannan sana’ar na gina gida, na yi aure da sauransu.
Aminiya:Ko akwai wadanda ka taba koyawa wannan sana’ar?
Eh, na koya wa akalla mutum hudu zuwa biyar.
Aminiya:Ko akwai wasu garuruwa da ka taba zuwa don yin yankan farce?
Na taba zuwa aiki Jihar Kano da Abuja da Katsina da kuma Zariya.
Aminiya: A fahimtarka me ya sa manyan mutane suke bukatar aikinka?
Farko dai Allah ne ya daukaka ni. Abu na biyu kuma galibin kunbar mutane musamman ta kafa akwai wadanda suke shigewa ciki. Galibi saboda haka za ka ji an ce a kirani na gyarata.
Aminiya: Ta yaya kake haduwa da manyan mutanen?
Dalilin ba ya rasa nasaba da irin wannan kunbar da take shigewa cikin yatsa sosai wadda ba kowane mai gyaran farce ba ne ya iya gyara ta. Za ka ga ji an ce idan mutum yana fama da ita, ya nemi ni don na iya gyara ta.
Aminiya: Kana da wani buri?
Ina fatan Allah Ya kara daukaka ni a kan sana’ata.
Aminiya: Ya batun iyali fa?
Ina da mata daya da ’ya’ya uku.