Na tafka kuskure a rikicin Libya – Obama
Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya ce rashin shiryawa abin da ya biyo bayan hambarar da Shugaban Kasar Libya Mu’ammar Gaddafi, shi ne kuskure mafi muni da gwamnatinsa ta yi. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da Gidan talabijin na Fox da ke Amurka, bayan an yi masa tambaya a kan abubuwan […]

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya ce rashin shiryawa abin da ya biyo bayan hambarar da Shugaban Kasar Libya Mu’ammar Gaddafi, shi ne kuskure mafi muni da gwamnatinsa ta yi.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da Gidan talabijin na Fox da ke Amurka, bayan an yi masa tambaya a kan abubuwan da gwamnatinsa ta yi mafi muni da kuma abu mafi alheri.
Ya ce, “duk da haka shiga tsakani a rikicin Libya da kasar ta yi abu ne da ya dace.”