Na tsaya, na zauna

Na tsaya, na zaunaWani Inyamuri ya je Sakkwato yana kasuwanci kuma yana takamar ya iya Hausa sosai. Wata rana ya je kotu kallon shari’a, ana cikin yi sai ya ji alkali yana cewa: ‘’Haba malam, kai yanzu duk wanga gari na jama’a, a ce ka rasa bido ko mutum guda wanga zai tsaya maka?” Alkali […]

Na tsaya, na zauna
Na tsaya, na zauna

Na tsaya, na zauna
Wani Inyamuri ya je Sakkwato yana kasuwanci kuma yana takamar ya iya Hausa sosai. Wata rana ya je kotu kallon shari’a, ana cikin yi sai ya ji alkali yana cewa: ‘’Haba malam, kai yanzu duk wanga gari na jama’a, a ce ka rasa bido ko mutum guda wanga zai tsaya maka?” Alkali ya kara da tambaya: “Ko a nan babu wanda zai tsaya wa wannan? (Ya nuna wani mutumin a tsaye a wajen tuhuma). Inyamuri da ya ga babu wanda ya daga hannu, sai a zuciyarsa ya ce: ‘’Ah, to don dai tsayuwa kawai, bari na taimaka masa.’’  Sai ya tashi ya ce: “Ranka ya dade, na tsaya masa.” Alkali ya ce: ‘’Yauwa, shari’a ta kare.” Ya kara da cewa: ‘’To, aradu wallah nan ga kwana uku idan bai bido kudi ya kawo har Naira dubu 200 ba, to kai za mu damke wallah bisa shari’a tai.” Da jin haka sai Inyamuri ya tashi figit, ya ce: “To, yallabai yanzu ‘’Na zauna masa.’’

Alayen Bagobiri
Na je wani gidan abinci, bayan an kawo mini na fara ci ke nan sai ga wani attajiri ya shigo shi ma, yana sanye da babbar riga da wata jaka a hannunsa; ya nemi waje ya kame. Can, sai ga wata mata ta shigo, ta je ta durkusa a gabansa tana kuka, tana cewa: “Don Allah Alhaji ka taimake ni, mahaifina ne bai da lafiya, ga shi ba mu da kudin da za mu kai shi asibiti. Sai ya bude jakarsa ya dauko Naira miliyan daya ya ba ta. Ta yi masa godiya ta tafi. Can, Sai ga wani mutum shi ma ya zo ya durkusa ya ce: “Alhaji don Allah ka taimake ni kamar yadda Allah Ya taimake ka. An kore ni ne a gidan da nake haya, ga shi ba ni da kudin da zan kama wani gidan, ga iyali, ga kudin makarantar yara.” Sai ya bude jaka ya dauko Naira miliyan biyu ya ba shi, shi ma ya tashi ya tafi. Ganin haka sai wani Bagobiri da ke zaune kusa da ni ya ce bari ya je ya yi wata karya, ko Allah zai sa ya sami rabonsa. Nan take ya tashi ya je ya durkusa a gabansa, ya fara kuka, har zai fara fadin matsalolinsa, sai wani ya zo ya taba shi, ya ce masa: “Malam, dan matsa, muna daukar fim ne!” Nan take na ga Bagobirinka ya yi tsuru-tsuru da idanu.