Na tuba daga sana’ar karuwanci – Safiya Musa
Sakamakon tattaunawar da wakilin Aminiya na Bauchi ya yi da Safiya Musa, wadda take zaune a Unguwar Tudun Wadan Xan iya da ake kira bayan gari Bauchi a makon jiya, yanzu wani babban ma’aikacin gwamnati xan asalin Jihar Kaduna da ke da gida a Bauchi ya yi alqawarin sama wa Safiya Musa mijin aure, kamar […]
Sakamakon tattaunawar da wakilin Aminiya na Bauchi ya yi da Safiya Musa, wadda take zaune a Unguwar Tudun Wadan Xan iya da ake kira bayan gari Bauchi a makon jiya, yanzu wani babban ma’aikacin gwamnati xan asalin Jihar Kaduna da ke da gida a Bauchi ya yi alqawarin sama wa Safiya Musa mijin aure, kamar yadda ta bayyana wa wakilin namu a tattaunawarsu kamar haka:
Aminiya: Bayan labarin da aka buqa a makon jiya waxansu abubuwa sun biyo baya ne Safiya Musa?
Safiya: Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maxaukacin Sarki, abin da ya sa na sake nemanka domin mu tattaunawa shi ne, ranar juma’a bayan naUyi wanka ina zaune a qofar xakina a cikin unguwar bayan gari sai wata qawata mai suna Binta Musa, wadda ‘yar asalin jihar Kano ce, sai ta ce waxansu mutane suna kirana a qofar gida. Nan take sai na fita waje, da zuwana sai suka ce min ke ce Safiya Musa wanda wakilin Aminiya ya zanta da ke a jarida? sai na ce musu tabbas ni ce Safiya Musa, sai suka ce mun su jami’an tsaron farin kaya ne da suke aiki a wannan Unguwa na bayan gari, domin kowa ya san cewa a Unguwar bayan gari akwai jami’an tsaro na(SSS) da Sojoji, waxanda suke zuwa daga lokaci zuwa lokaci, sai kuma ‘yan sanda na(CID) da sauran hukumomin tsaro. Sai na tambaye su, shin lafiya kuka zo nemana? sai suka ce akwai wani mutum mai suna Alhaji Abubakar Usman wanda yake zaune a Unguwar turawa(GRA)Bauchi shi ne yake nemana, muna so za mu je wajensa tare idan kin amince. Sai na ce musu to don Allah su bari sai gobe asabar da yamma su zo muj e wajensa tare, tun da ban san abin da yake nufi ba.
Ranar asabar da misalin qarfe 5:00 na yamma sai suka zo a cikin wata baqar mota suka xauke ni zuwa gidansa da ke Unguwar GRA, da zuwanmu sai muka same shi yana zaune a cikin falonsa, muka yi sallama muka shiga. Bayan da muka gama gaisawa sai ya ce mun ke ce Safiya Musa wadda wakilin Aminiya ya zanta da ke game da sana’ar karuwanci? nan take sai na ce masa ni ce Safiya Musa kuma ni ‘yar asalin jihar Kaduna ce shekara ta 22 a duniya, kamar yadda aka rubuta a jaridar. Sai ya ce, Allah ya saka miki da alheri, na karanta jawabanki xaya bayan xaya, don haka na sa jami’an tsaro na farin kaya su nemo mun ke a duk inda kike a jihar Bauchi, ni mutumin jihar Kaduna ne amma ina da gida a Bauchi kuma ni ma’aikacin gwamnati ne, ina zaune ne a Unguwar Kawo Kaduna. Inaso zan fitar dake ne daga wannan mummunar sana’a ta karuwanci, za ki amince da haka? nan take na ce masa ko yanzu a shirye nake da in tuba daga wannan sana’a wadda take cike da wahala.
Daga nan sai ya ba ni Naira dubu goma sha biyar ya ce in je in kwaso kayayyakina sannan kuma in biya qananan bashin da ake bi na a Unguwar bayan gari Bauchi, kuma akwai xaki a gidansa wanda za a ba ni, sannan kuma yana da matarsa da ‘ya’yansa a gidan.
Ranar litinin da safe na kwashe dukkan kayayyakina daga Unguwar bayan gari na koma gidansa da ke GRA, an ba ni xaki wanda nake kwana a ciki, sannan kuma ana ba ni abinci mai qyau sau uku a rana daidai bakin gwargwado, kuma yanzu haka wannan tattaunawa da muke yi da kai a cikin gidansa muke yi ba a Unguwar bayan gari ba.
Aminiya:Yanzu za mu iya cewa kin tuba ke nan daga karuwanci ?
Safiya: Tabbas na tuba daga sana’ar karuwanci, sannan kuma ya yi alkawarin cewa zai sama mun mijin aure tare da biyan sadaki Naira dubu hamsin, zai kuma saya min kayan xaki, wanda kuma zai aure ni zai ba shi tallafi daidai bakin gwargwado, yanzu haka ina salloli sau biyar a kan lokaci a kowace rana, savanin zaman bayan gari. A gaskiya ma fi yawan matan da suke zaune a Unguwar Tudun Wada ba sa kula da sallah, yanzu haka na fi jin daxin jikina fiye da kowace lokaci a rayuwa, ina fata Allah Ya gafarta mana kura-kuranmu da sauran Musulmi baki xaya.
Aminiya: Kin saba cuxanya da maza iri-iri, anya za ki iya haqurin zaman aure kuwa?
Safiya: Ina so al’umma su fahimci cewa ni budurwa ce ban tava yin aure ba, sakamakon auren dole ne na samu kaina a cikin wannan yanayi, tabbas waxansu za su yi kokonto, amma ka sani cewa har abada babu wata alaqa da zan sake yi da wani namji a duniya in ba mijina ba, domin abin da mai wannan gidan ya yi mun har in mutu ba zan manta ba a rayuwa. Kuma a ranar Lahadi mai zuwa (jibi) zai xauke ni a motarsa tare da ‘ya’yansa da matarsa zuwa wajen mahaifina a garin Kaduna, za su tattauna da shi, kafin daga bisani mu dawo Bauchi tare, kuma ya ce bayan mun dawo daga Kaduna zai kai ni asibiti domin a duba lafiya ta a tabbatar ba ni da wata matsala, kafin daga bisani ya nema mun mijin aure.
Yanzu haka an xinka mun sabbin kaya kala goma, kuma matarsa tana xaya daga cikin waxanda suka ba shi shawarar da ya ceto rayuwa ta, har Allah Ya sa ya amince da haka, kuma idan muka kammala wannan tattaunawa za mu wajensa tare ku gaisa. Wannan jarida ta Aminiya ita ce sanadiyyar fitar da ni daga wannan sana’a ta karuwanci, domin da ba ku buga labarin ba da babu inda duniya za ta san halin da muke ciki a Unguwar bayan gari.
Aminiya: Lokacin da kika je kwashe kayayyakinki me kika faxa wa abokanan zamanki?
Safiya: Gaskiya tsakani da Allah, lokacin da na je kwashe kayayyakina mutane da dama sun yi mamakin cewa wai me ya faru Safiya take kwashe kayayyakinta ne, ko sun yi faxa ne da wata? Mafi yawan mutane abin da nake faxa musu shi ne, na samu mijin aure ne, kuma na tuba daga karuwanci don haka ba na buqatar cigaba da zama a Unguwar nan.
Bayan na fitar da kayayyakina daga xakin, nan take sai ga wata budurwa baquwa wadda ta fito daga Jihar Taraba saurayinta ya biya mata kuxin xakin na wata biyu, ita ma daga ganinta ba ta tava yin aure ba, sabuwar zuwa ce. Kamar yadda na faxa maka a baya, kusan kullum sai ka samu ‘yan mata sabbin zuwa a Unguwar bayan gari, muna fata waxanda suke cikin wannan sana’a Allah Ya kawo xauki, kamar yadda ta sanadiyyar Aminiya na tuba daga karuwanci.
Zamana a bayan gari ya sa na gano kaxan daga cikin abubuwan da ke sa waxansu maza neman mata a waje, mafi yawan matanmu na Hausawa ba sa kula da abubuwa, tsafta, yin lalle a hannu da qafa, waxansu matan ba sa wanke bakinsu, da amfani da kayayyakin sawa kamar su bireziya da makamantansu, sannan kuma mafi yawan matan hausawa ba sa iya gamsar da mazajensu yadda ya kamata a lokacin kwanciyar aure.
Aminiya: Daga qarshe, mene ne saqonki ga Alhaji Abubakar Usman?
Ba ni da wata kalma da zan faxa sai Allah Ya saka wa Alhaji Abubakar Usman da gidan aljanna, bayan haka sai kai kanka Hamza Aliyu wakilin Aminiya da sauran ma’aikatanku, Allah Ya saka muku da alheri da kuka zamo ta sanadiyyar aikinku ne na tuba daga wannan sana’a ta karuwanci, wadda babu wani alheri a ciki sai wahala. Yanzu haka ina tabbatar wa duniya cewa ina da zama ne a Unguwar turawa ta GRA Bauchi, ni da karuwanci har abada, na gode sosai.
To sai dai kuma da wakilimu ya tuntuvi Alhaji Abubakar Usman ko me zai faxa game da halin da Safiya Musa ta samu kanta a ciki, sai ya bayyana cewa, ‘’ni ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna ne kuma har yanzu ina aiki ban yi ritaya ba, amma ka bari idan na samu wanda zai aure Safiya Musa bayan an kammala komai game da hidimar aure zan yi tattaunawa ta musamman da Aminiya domin bayyana wa duniya abin da ya sa na ceto rayuwar wannan yarinya, amma yanzu babu abin da zan faxa. Zan xauke ta tare da iyalina domin zuwa wajen mahaifinta da ke Kaduna, kuma ni xan asalin jihar Kaduna ne, na fito ne daga qaramar hukumar Zariya.