Na warkar da mashaya fiye da dubu – Malam Niga

Cibiyar Malam Niga da ke garin Rigasa Kaduna cibiya ce da ta shahara wajen tsugunarwa da warkar da mashaya kayen maye maza da mata don su zamo ’yan kasa nagari. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ya warkar da mashaya sama da dubu daya cikin shekara 10 da kafa cibiyar: Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana […]

Na warkar da mashaya fiye da dubu – Malam Niga
Na warkar da mashaya fiye da dubu – Malam Niga

Cibiyar Malam Niga da ke garin Rigasa Kaduna cibiya ce da ta shahara wajen tsugunarwa da warkar da mashaya kayen maye maza da mata don su zamo ’yan kasa nagari. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce ya warkar da mashaya sama da dubu daya cikin shekara 10 da kafa cibiyar:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Alhaji Lawal Yusuf Muduru wanda aka fi sani da suna Malamin Nigogi a takaice ana kirana Malam Niga. Dalilin da ya sa ake yi min lakabi da Malam Niga ya faro ne daga yadda na fara tsugunar da mashaya da koya musu sana’o’i. Idan za a yi kwatance, sai a ce Malamin Nigogi. Daga nan sunan ya koma Malam Niga.
Mene ne dalilin kafa wannan cibiya?
Burina shi ne matasa su zama na kwarai, ba lalatattu ba.
Wannan shi ne dalilin kafa cibiyar da Ingilishi ana kiranta da “Niggas Rehabilitation and Skills Ackuisition Training Centre” kuma burinta shi ne hana shan kwaya. A yanzu haka cibiyar tana da matasa 250 wadanda a cikinsu akwai mata 12.
Yaran talakawa kadai ne ko da na manya?
Abin mamaki shi ne a cikin daliban nawa Nigogi akwai ’ya’yan manyan mutane. Har da dan wani Gwamna mai ci wanda bai dade da gama samun horo ba.
Me ya sa ake sa wa maza mari a nan cibiyar?
A wannan cibiya ana sa wa maza mari ne a kafa don kada su je su nemi rigima ko su gudu ko kuma su nemi abin maye su sha. Don in an sa wa mutum mari ana iya kula da shi sosai don ba zai iya gudu daga cibiyar ya koma ruwa ba. Amma ba a sa wa mata komai, sai ana yi musu fada cewa bai kamata su bi halin lalatatttu ba.
Su wa ake ba mukamai a cikin dalibai?
Wadanda suka dawo cikin hankalinsu ne ake yi wa haka. Sannan wadanda suka kusa kammala horo su ma ana ba su mukaman shugabannin dalibai.
Mene ne ma’anar Bigi ko Big-Gal da na ji ana kira wasu a cikin daliban cibiyar?
Yaran ne ke sanya wa kansu suna da lakabin “Bigi” a fannin maza da kuma “Big Gal” a fannin mata.
Bigi su suke tsawata wa sababbin shigowa wannan cibiya, in sun yi sanyin jiki wajen aiki, ko sun yi magana da wanda yake wucewa. Bigi suna da tsabta, kayansu ja ne kamar na kowa, sai dai su Bigi suna da wandon jins kuma kayan sawansu a wanke kuma a goge yake. Sannan wasu daga cikin matan suna sa nikabi don kare fuskokinsu.
Don me ake yi musu yunifom ja?
Ana haka ne don bambance ’yan wannan cibiya da wadanda suke wasu daban. Domin da ba a sa kaya na bai-daya.
Wacce gata suke da ita?
Ranar Lahadi ne ake ziyartar ’ya’yan wannan cibiya. Domin wasu ana ziyartar su koyaushe saboda ’yan gata ne. Sai muka hana, aka mayar da ziyarar sai ranar Lahadi kadai.
Yaya tarbiyya take gudana a cibiyar?
Tilas ne kowa ya tashi ya yi Sallah, ya yi wanka, ya gyara kumba, ya yi aski, sannan a yi jerin gwano a fito, a fitar da kayan aiki sannan a koyi sana’a. A yanzu na yi musu gata don an sa musu talabijin da satilayit don su wala.
Wadanne sana’o’i ake koyarwa a cibiyar?
Sana’o’in da ake koyarwa sun hada da dinkib da saka da aski da walda da gyaran janareto da gyaran farce da sarrafa holoko (tinka) da ilimin kwamfuta da aikin kafinta da rini da kasuwancin man gyada da manja da kuma kayan gwanjo.
Shin ko ka taba samun tallafin gwamnati?
Ban taba samun gudunmuwar ko kwabo daya ba daga gwamnati.

Tattaunawa da wasu daga cikin masu samun horo

Me ya kawo nan?
Sunana Ibrahim Mukhtar ni mutumin Zariya ne. Ina da digiri a fannin ilimin gudanarwa (Public Administration) daga Jami’ar American da ke kasar Masar. Kuma tabuwa ce ta sa aka kawo ni gun Malam Niga. Na fara ne da shan sigari da wiwi da koken inda abokan banza suka sa ni a hanya a kasar Masar. Bayan na dawo Najeriya ne na yi hidimar kasa na fara aiki, na yi aure na samu ’ya’ya biyu, babban nasa masa suna Khalifa don sunan mahaifina yake da shi. Da na fara tabuwa saboda shaye-shaye ne aka kama ni aka kawo ni nan. Yanzu na dawo hankalina bayan na yi wata tara ban hambudi kayan maye ba. Kuma ina fannin koyon ilimin kwamfuta ne. Ina kira ga matasa su guji shan kayan maye musamman da zabe ya kawo jiki inda ’yan siyasa ke samar wa matasa abubuwan maye don su yi musu banga.
Kai me ya kawo nan?
Sunana Muhammad Abubakar na je karatu kasar Malaysiya don yin karatun digiri a Jami’ar Canada da ke can, (Canadian-Malaysian Unibersity), amma na bi gayyar mashaya bayan na fara da tabawa a nan gida.
Muna zuwa cikin gari ne mu sayo sannan mu dawo cikin jami’a mu shiga makaranta mu yi mankas. Tabuwa ce ta bude mini kofa aka dawo da ni Najeriya aka sanya ni a wannan cibiya. Yanzu na shafe wata hudu a cibiyar
’Yan mata me ya kawo nan?
Sunana Sumayya Mu’azu na kammala karatun sakandare ne a makarantar Adeyemo da ke Kaduna, kawayen banza suka jefa ni cikin wannan harkar ta shaye-shaye kamar kodin da shisha. Sannan ina sa samarina suna kawo mini. Amma da iyayena suka lura na fara kauce hanya sai suka kawo ni nan. Bayan watanni yanzu iya koyon dinki da saka da yin turaren kanshi da sauransu. Ina kuma horon matasa su guji kayan maye, su zamo masu biyayya ga iyayensu.
Ke kuma me ya kawo ki?
Sunana Maryam Muhammad na fara ne da koyon shan taba da kwaya. Kuma in an bata min rai sai in sha, sai inji “shiru.” Iyayena suka lura na sauya, sai suka yi min tarbe ni, suka kawo nan inda nake koyon dinki da saka da yin sabulu. Ina horon matasa su guji harkar ababe masu sa maye. Ina matukar bakin cikin yadda na tsinci kaina a ciki, don ba abin kwarai ba ne.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya