Na yafe wa wadanda suka tsige ni – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Hammayero Nyako ya ce ya yafe wa masu hannu a tsige shi daga kujerar Gwamnan Jihar a bara. Admiral Murtala Nyako ya bayyana haka ne lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Yola a ranar Asabar din da ta gabata bayan gudun hijirar da ya yi ta kusan […]

Na yafe wa wadanda suka tsige ni – Nyako
Na yafe wa wadanda suka tsige ni – Nyako

Tsohon Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Hammayero Nyako ya ce ya yafe wa masu hannu a tsige shi daga kujerar Gwamnan Jihar a bara.

Admiral Murtala Nyako ya bayyana haka ne lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Yola a ranar Asabar din da ta gabata bayan gudun hijirar da ya yi ta kusan shekara daya.
Tsohon Gwamna ya bar kasar nan ne zuwa Turai a lokacin da ya samu labarin tsige shi da aka yi a ranar 15 ga watan Yulin bara.
“Na yafe wa duk wanda yake da hannu a tsige nin da aka yi, domin yin Allah ne. Don haka na manta da wannan a yanzu, sai mu hada kai da Jam’iyyar APC domin jam’iyya ce da za ta iya canza duk tabargazar da aka yi a kasar nan,” inji shi.
Ya ce ya gode da irin kaunar da jama’ar jihar suka nuna masa bayan an tsige shi. Ya ce tsigen shi da aka yi sanadiyar shawarar da ya bai wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne wanda ya ki jin shawararsa. “Mun ba su shawara amma sai suka fusata da mu. Na gaya wa tsohon Shugaban kasa Jonathan cewa ya kauce hanya, maimakon ya gyara sai ya tsige ni. Jonathan ya yi babban kuskure da ya ki bin shawarata,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Ina mika godiyata ga jama’ar Adamawa da suka kada Jam’iyyar PDP. Yanzu ya kamata mu mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya domin mutum ne mai amana.”
Mutane da dama ne suka tarbe shi a filin jirgin saman, inda wasu tun misalin karfe 8:00 suke je filin jirgin suna jiran isowarsa, inda yana fitowa daga jirgin da ya kai shi sai filin ya barke da sowa, “Sai Baba!”
Yana sauka ya wuce kai-tsaye zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Yola domin duba jikin wadanda harin bam ya rutsa da su, inda ya yi addu’ar Allah Ya kare na gaba.