Na yarda Musa dana ne – Janar Gowon

Shari’ar shekara da shekaru da aka tafka game da wane ne mahaifin Jack Musa Gowon, ta kawo karshe bayan da tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya amince cewa shi ne mahaifin Musan.Musa Gowon, wanda ya dawo Najeriya kwanakin baya, bayan ya shafe shekara 20 a kurkukun Amurka mahaifiyarsa ita ce  Misis Edith Ike-Okongwu.A cikin […]

Na yarda Musa dana ne – Janar Gowon
Na yarda Musa dana ne – Janar Gowon

Shari’ar shekara da shekaru da aka tafka game da wane ne mahaifin Jack Musa Gowon, ta kawo karshe bayan da tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya amince cewa shi ne mahaifin Musan.
Musa Gowon, wanda ya dawo Najeriya kwanakin baya, bayan ya shafe shekara 20 a kurkukun Amurka mahaifiyarsa ita ce  Misis Edith Ike-Okongwu.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu Janar Yakubu Gowon ya ce:  “Bayan shekaru ana tababa, gwajin kwayar halitta (DNA) da aka gudanar a baya-bayan nan domin gano mahaifin Musa Gowon wanda ya dawo kasar nan kwanakin baya. Mu iyalansa muna kokarin taimaka masa ya dawo cikin hayyacinsa sakamakon samun kansa a cikin mawuyacin hali na dogon lokaci a rayuwarsa. Kuma a daidai lokacin da muke tunkarar gaba bisa imani da Ubangiji, muna rokon a girmama martabarmu ta mutumtaka. Mun gode muku.”
Musa Gowon, now wanda yanzu ya cika shekara 48 da marigayiyar mahaifiyarsa sun kai kara kotu na tsawon shekaru suna bukatar a bayyana wane ne mahaifinsa. Misis Edith ta haife shi ne a daidai lokacin da ake tsakiyar Yakin Basasar Najeriya a shekarar 1968 lokacin da Janar Gowon yake Shugaban Gwamnatin Mulkin Soja kuma Babban Kwamandan Askarawar Najeriya.  Miss Edith Ike-Okongwu ta rasu ne sakamakon cutar daji a shekarun baya. Kuma an nuna Janar Gowon ya kai mata ziyara a gadonta na sibit kafin rasuwarta.