Na yi biyayya ga umarnin Majalisar Malamai – Maitala

dan takarar Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a karkashin Jam’iyyar PDM, Alhaji Haruna Maitala Jingir ya musanta zargin da aka yi masa cewa ya ki bin umarnin da Majalisar Malaman Musulunci ta Jihar Filato ta ba su na su janye daga takarar da suka yi kan wannan kujera a zaben shekarar […]

Na yi biyayya ga umarnin Majalisar Malamai – Maitala
Na yi biyayya ga umarnin Majalisar Malamai – Maitala

dan takarar Majalisar Tarayya daga mazabar Jos ta Arewa da Bassa a karkashin Jam’iyyar PDM, Alhaji Haruna Maitala Jingir ya musanta zargin da aka yi masa cewa ya ki bin umarnin da Majalisar Malaman Musulunci ta Jihar Filato ta ba su na su janye daga takarar da suka yi kan wannan kujera a zaben shekarar 2011, su bar wa Alhaji Suleiman Yahaya Kwande.

Alhaji Haruna Maitala ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Jos a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce lokacin da Majalisar Malaman ta ce a zabi Alhaji Sulaiman Kwande, mu kuma mu yi hakuri. “Ni ne na fara mikewa na nuna goyon bayana kan matakin da aka dauka. Na kira ma’aikatana da sauran mutanena na ce musu mu yi hakuri mu dauki kaddara kan wannan mataki da aka dauka. To, amma hakan bai hana wasu da ba su samu wannan labari su jefa wa jam’iyyata kuri’a a yankinmu na Pengana a lokacin ba,” inji shi.
Dangane da dalilin fitowarsa takara a Jam’iyyar PDM a wannan karo ya ce, duk da cewa su ne suka kafa Jam’iyyar PDP a Jihar Filato, amma rashin adalci a jam’iyyar musamman a lokacin Gwamna Jonah Jang na rashin tafiya da al’ummarsu ya sanya ya koma PDM.
“Lokacin da na fara fitowa takara a PDP a shekarar 2003 jam’iyyar ta karbe ni. Amma a fitowar da na yi a shekarar 2007 lokacin Jonah Jang an nuna mini rashin adalci domin wanda muka yi takara da shi wato Mista James Yakubu, bayan da ya fadi a babban zabe, sai aka ba shi Kwamishina. Kakakin Jam’iyyar PDP a lokacin, Mista Nuhu Gagara shi ma an ba shi kwamishina, amma ni da na yi takara kuma Ma’ajin Jam’iyyar PDP na Jihar Filato ba a ba ni komai ba, saboda rashin adalcin da ake nuna wa al’umarmu. Saboda wannan dalili ya sa a shekarar 2011 na fita daga PDP na fito takara a CAN, a wannan karo kuma na fito takara a PDM,” inji shi.
Ya ce ya bayar da gudunmawa sakamakon shigarsa siyasa. “Misali a zaben dan Majalisar Tarayya na Mazabar Jos ta Arewa da Bassa na shekarar 2003 da aka yi takara tsakanin Alhaji Shehu Sale Hassan da Lumambah Da Adeh, an so a murde zaben, amma na gaya wa Gwamna Dariye na roke shi alfarma take ya bayar da umarni aka sanar da cewa Alhaji Shehu Sale Hassan ne ya lashe zaben,” inji shi. Ya ce a karamar hukumarsa ta Bassa, ya taimaka wa mutane da dama suka samu nasara a zabe da suka hada da tsohon shugaban karamar hukumar Mista Jonathan Dabo da tsohon dan majalisar jihar Mista Wanga Limaro da dan majalisar jihar a yanzu Musa Gonduna.