Na yi dalilin hada aure fiye da dubu
Aminiya: Me ya ba ka sha’awa ko ya jawo hankalinka har ka shiga aikin hada aure da kuma lokacin da ka fara? Mai Dalilin Aure: Na fara yin dalilin aure tun a 1998 lokacin ina aikin tsaro a Jami’ar Bayero, Kano. Saboda yadda na ga al’amura suna kasancewa a tsakanin mutanen da ke shiga jami’ar […]

Aminiya: Me ya ba ka sha’awa ko ya jawo hankalinka har ka shiga aikin hada aure da kuma lokacin da ka fara?
Mai Dalilin Aure: Na fara yin dalilin aure tun a 1998 lokacin ina aikin tsaro a Jami’ar Bayero, Kano. Saboda yadda na ga al’amura suna kasancewa a tsakanin mutanen da ke shiga jami’ar tare da mata a motocinsu. Wannan ya sanya na rika kiransu ina tambayarsu dangantakarsu da matan, inda a karshe dai na gane cewa akwai bukatar in fara taimakawa wajen hada aure tsakanin ire-iren wadannan mutane da yawancin matan da suke zuwa da su.
Daga nan ne na ci gaba da wannan kokari kuma ina cimma nasara tun daga wancan lokaci har zuwa yau din nan, domin bayan na yi ritaya daga aiki sai na kama wannan aiki na hada aure tsakanin mata da maza inda akalla na hada aure sama da dubu daya. Kuma ina matukar jin dadin wannan aiki da nake yi wanda kuma nake fata in ci gaba da yi har iyakacin rayuwata.
Aminiya: Yanzu idan namiji ko mace suna bukatar samun aure ta hannunka, wace hanya za a bi a cimma nasara ke nan?
Mai Dalilin Aure: To, akwai hanyoyi guda biyu zuwa uku. Ko dai a tuntube ni a waya ko a je har gida a same ni ko kuma ta hanyar wani wanda ya san ni. Duk hanyar da mutum ya bi insha Allah zai samu biyan bukata, walau mace ko namiji. Amma fa ina da dokoki masu tsauri domin aiki nake yi na daukaka Sunnar Manzon Allah Annabin Muhammad (SAW).
Aminiya: Wadanne dokoki kake da su kuma ta yaya ake bin su tunda ka ce suna da tsauri?
Mai Dalilin Aure: Doka ta farko ita ce kada a kawo wasa cikin neman aure ta dalilina, sannan ba a zuwa da daddare domin ba zan kai mutum wurin macen da yake so ba, kuma ban a son a shigar da karya ko coge cikin harkar neman aure, saboda hakan yana hafar da zubewar daraja tsakanin ma’aurata.
Aminiya: Ko ka taba fuskantar wata matsala tsakaninka da wadansu ma’aurata tunda ka fara wannan dalili na aure?
Mai Dalilin Aure: Matsalar da nake fuskanta ita ce ta rashin sallama, domin akasarin mutanen da na yi wa hanyar aure ba sa kawo min sallamar da ake ba ni ta turmin zane daya tak, wanda hakan bai dace ba, amma lallai wadansu suna ba ni kuma su yi godiya bisa abin da na yi musu. Kuma ina fata duk wadanda na yi wa dalilin aure za su rika cika alkawarin da muka kulla na turmin zane.
Aminiya: Ta yaya mutum zai samu wadda yake so ta hannunka musamman ganin cewa ana zuwa wurinka ne daga sassa daban-daban na Jihar Kano dama wasu wurare da watakila za mu ji su nan gaba?
Mai Dalilin Aure: Idan mace ko namiji yana son aure ta hannuna, sai ya je ya same ni ya bayyana min irin matar da yake so. Ni kuma sai in karbi lambar wayarsa tunda yanzu Allah Ya kawo mana saukin sadarwa. Bayan dan lokaci kamar kwana biyu zuwa uku sai in tuntube shi idan har an samu irin wadda yake bukata, daga na sai in kai shi har gidansu su tattauna sannan idan Allah Ya yi, sai a yi aure a zauna. Haka ita ma mace idan ta zo wurina sai ta bayyana min irin mutumin da take so, sai in hada su. Idan suka shirya sai a yi aure kuma har yau babu wata matsala da ta taso.
Aminiya: Bayan karbar lambobin waya akwai wata hanya a kake bi wajen ganin an samu daidaito tsakain mace mai son a hada ta da mijn aure ko namijin da ke son matar da zai aura?
Mai Dalilin Aure: Wadansu suna ba ni hotunansu in nuna wa mazan domin tabbatar da cewa mutun ya samu wadda ta dace da shi. Haka su ma mazan sukan ba da hotuna domin gwada wa matan ko za a samu dacewa. Sai dai gaskiya wadansu ba sa iya yin hoto watakila saboda kunya ko wani dalili nasu. Amma dai al’amura suna ci gaba da tafiya cikin nasara kamar yadda na bayyana a baya.
Aminiya: Wasu lokutan kana gamuwa da ma’auratan da suka yi aure kuma suka rabu, idan hakan ta kasance kana sasanta ire-iren wadamnan ma’aurata don su koma su ci gaba da aurensu?
Mai Dalilin Aure: Babu shakka ina haduwa da ma’auratan da suka taba zama tare amma ba na yin sasanci domin a wasu lokutan sasanta ma’aurata yana da wahala matuka. Ni dai in tsaya ne kan yin dalilin aure kuma a koyaushe maza da mata suna zuwa neman abokan zama kuma ana dacewa kullum idan gari ya waye.
Aminiya: Masu bukatar samunka ta wace hanya za su hadu da kai ban da batun lambar waya?
Mai Dalilin Aure: Dukan masu son ganawa da ni sukan same ni a Unguwar Dorayi Babba Gidan Mahauta a Karamar Hukumar Gwale a birnin Kano. Sannan ina so a sani cewa akwai mutane musamman mata daga jihohi daban-daban da suka zo suna bukatar irin mazan da suke fatan samu, akwai mata daga Nijar da Kamaru da Sudan da ke son samun mazan aure da gaske a wajena a zancen nan da muke yi.