‘Na yi gunduwa-gunduwa da Cif Odunukwe ne don in mallake gidansa na Naira miliyan 900’
Babban wanda ake zargi da kashe fitaccen dan kasuwar nan na Legas, Cif Hyginus Odunukwe, mai suna Daniel Bob Ibeaji ya ce ya hada baki da wadansu mutum uku ne suka kashe attajirin domin su mallaki wani gidansa na Naira miliyan 900. Daniel wanda ya ce ya karanci likitanci a Edinburgh da ke Birtaniya, ya […]
Babban wanda ake zargi da kashe fitaccen dan kasuwar nan na Legas, Cif Hyginus Odunukwe, mai suna Daniel Bob Ibeaji ya ce ya hada baki da wadansu mutum uku ne suka kashe attajirin domin su mallaki wani gidansa na Naira miliyan 900.
Daniel wanda ya ce ya karanci likitanci a Edinburgh da ke Birtaniya, ya ce sun kashe attajirin ne ta hanyar sararsa da gatari da kuma yi masa allurar kashe jiki, sannan suka gunduwa-gunduwarsa.
An gano gawar mamacin ne a dajin Ogombo da ke Ajah, a Jihar Legas.
Daniel ya hada baki ne da Arinze Igwe mai shekara 26 da Solomon Cletus mai shekara 30 da Israel Obigaremu mai shekara 35.
Rahotanni sun ce babban wanda ake zargin ya bukaci dan kasuwar wanda ke harkar gidaje da gwal cewa yana son gida. Attajirin ya baro Ikoyi ne a ranar 1 ga Disamban bara, bayan ya shaida wa iyalansa cewa zai je wajen wanda ake zargin, amma tun ranar bai dawo ba.
Daga baya an tsinci gawarsa bayan an yi gunduwa-gunduwa da ita, sannan ka gano motarsa kirar SUB a Aritisan Beach Resort.
Da yake bayyana dalilinsa na kashe attajirin, lokacin da Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sanda mai kula da Shiyya ta 2, Ahmed Iliyasu ya gabatar da su, ya ce, “Na kashe shi ne saboda ina son in mallaki gidansa na Naira miliyan 900. Neman duniya ya sa na kashe shi. Mun hadu ne a watan Satumban bara a Abuja ta hanyar tallar gidan. Sai na kira shi na ce ina son gidan, sai ya ce in zo Legas. A ranar Lahadi bayan ya sanya hannu a takardar yarjejeniyar gidan, sai na ce masa ya shigo cikin dakina a otel domin ya karbi kudinsa. Bayan ya shigo sai na ce masa ya ban takardun, sai ya ce ba zai ba ni ba sai na biya. A wannan lokacin ne daya daga cikinmu ya shigo da jakar kudi, da ya tsuguna ya duba, sai na buga sara gatari a kai. Sai muka ja shi cikin ban-daki, muka yi masa allurar diazepam da ta sa shi barci. Burina shi ne in yi amfani da takardun da ya sanya wa hannu in mallaki gidan, in sayar da shi,” inji shi.
Daya daga cikin wadanda suka hada baki da shi, Solomon Cletus ya bayyana wa ’yan sanda cewa an yi masa alkawarin Naira miliyan 2 idan aka samu nasara.
“Mu ne muka fitar da gawar attajirin daga otel tare da taimakon wani ma’aikacin otel din, Arinze Igwe a cikin buhu.”
A jawabin Alhaji Ahmed Iliyasu ya gargadi mutane su kiyaye wajen saka bayanansu a shafukan sada zamunta, inda ya ce mugayen mutane suna amfani da bayanan. “Ina gargadi ga dukkan baragurbi a duk fadin jihohin Legas da Ogun cewa Shiyya ta Biyu ta ’yan sanda ba za ta aminta da ayyukan baragurbi ba. Ba za su samu sauki ba ko kadan,” inji shi.