… ‘Na yi kokarin tsayar da motar maharan da suka so halaka Buhari’
Ibrahim Abubakar daya ne daga cikin masu tsaron lafiyar Janar Muhammadu Buhari da ya shafe shekara 15 tare da shi. Yana tare da Janar din a lokacin da aka kai masa harin kunar bakin wake a makon jiya, ya bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya faru a gadon asibitin da yake kwance a Kaduna:Aminiya: Yaya […]
Ibrahim Abubakar daya ne daga cikin masu tsaron lafiyar Janar Muhammadu Buhari da ya shafe shekara 15 tare da shi. Yana tare da Janar din a lokacin da aka kai masa harin kunar bakin wake a makon jiya, ya bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya faru a gadon asibitin da yake kwance a Kaduna:
Aminiya: Yaya za ka bayyana harin da aka kai wa Janar Buhari makon jiya?
A ranar da wannan al’amari ya faru muna tare da Janar Muhammadu Buhari a hanyarmu ta zuwa Daura don bubukuwan karamar Sallah. Lokacin da muka kama hanya, mun tadda dimbin ababen hawa da jama’ar da ke hanyar komawa garuruwansu bayan halartar bikin rufe tafsirin Sheikh dahiru Usman Bauchi.
Muna isa kusa da Unguwar Hayin Banki, sai muka lura da wata mota na gudu sosai tana yunkurin shan gabanmu daga bangaren dama. Ina zaune ne daga baya ta bangaren. Na yi kokarin dakatar da direban motar saboda irin gudun da yake yi, tsorona kada ya buge masu tafiya a kafa. Mun nufo daura da gadar kawo ke nan, sai bam din da motar ke dauke da shi ya fashe. Motar farko daga cikin jerin motocin da muke tafiya da su tana dauke ne da ’yan sanda, ta tsakiya ita ce ke dauke da Janar Buhari. Mota ta uku kuma ta karshe, na dauke ne da ni da abokan aikina.
A wane lokaci ne bam din ya fashe?
A lokacin da nake kokarin tsayar da direban motar da hannu, sai na ji wata kara. Sai na tsinkayi wani bakin hayaki ya rufe baki dayan wurin. Duk gilasan tagogin motarmu sun tarwatse, tayoyin motar duk sun sace ga jama’a suna ta kururuwar neman agaji. Na yi kokarin na sauko daga mota amma sai kofa ta ki buduwa, daga bisani sai muka fice ta tagar bangaren hagu. Mun tarar da gawawwaki da dama amma cikin hanzari muka nufi wajen motar Janar. Abin mamaki, kafin karasowarmu har Janar ya sauko da kansa yana duba gawarwakin da ke warwatse a kan kwalta. Yana cikin daga wa jama’a hannu ne sai muka kewaye shi. Daga nan sai wasu daga cikin mutane suka fahimci cewa ai Janar ne, sai wasu suka fara shewa. Yana da kyau a fahimci cewa Janar Buhari ya hana mu amfani da jiniya a lokacin da muke kan hanya.
Da muka fahimci cewa bam din ya lalata motocin sosai, mun yi kira ta waya a kawo mana wasu motocin da za mu maida shi gida. Sai muka kaurace wa wurin gudun wani hari da ka iya biyo baya. Muka tsallaka da shi daya bangaren titin, inda muka yi katarin samun wata mota kirar Golf 3 da da ita muka koma da shi gida. Daga bisani ne kuma muka samu taimakon wasu motocin domin kwashe sauran kayayyakinsa. Mu kuma mutum uku da muka samu raunuka, muka wuce asibiti don neman magani.
Kamar daidai wane lokaci ne abin ya faru?
Da misalin karfe 2:00 da wasu mintoci na rana.
Tun yaushe ka lura cewa motar na biye da ku?
Ba zan iya tunawa ba, saboda dimbin ababen hawan da suka halarci bikin rufe karatun.
Ko kun samu labarin harin bam din da aka kai wa Sheikh dahiru Bauchi?
Mun samu labarin harin wanda ya faru da azahar. Amma ba mu taba tunanin cewa bayan nasa mu ma namu na tafe ba.
Ko za ka iya fada mana sunayen wadanda suka samu raunuka?
Akwai ni kaina, Abubakar Ibrahim da Ya’u Abdullahi da kuma Sufeto Mike Reuben.
Wadanne irin raunuka kuka samu?
Yatsata ce ta samu karaya. Kuma saboda bam din ya fashe ne daga bangaren da nake zaune, jina ya ragu sosai. Sufeton ya samu rauni ne aka da yanka a hannu. Shi kuma Ya’u yana da rauni ne a gwiwar hannu. Kodayake dukkanmu ba mu jima ba aka sallame mu daga asibitin.
Me ya sa yanzu ka dawo asibiti?
Na dawo ne saboda karayar da ke yatsata. Har ila yau, dimbin jama’a da ke zuwa gidana don jajanta min tare da wasu da dama da ke kirana ta waya da kuma tasirin harin a gare ni, saboda wadannan abubuwan da lissafa ne nakan kasa runtsawa a gida kuma su ne suka sa ni dawo asibiti.
Yaya batun cewa an cafke wani a wurin sanye da Hijabi?
Ba ni da masaniya saboda ba zan iya tuna abin da yake faruwa ba, a wurin saboda yadda hankulanmu suka ta’allaka wajen kokarin kare Janar bayan kai harin.
Tsawon wane lokaci kake tare da Janar Buhari?
Yanzu kimanin shekara 15 ke nan. Kuma ina farin ciki cewa Janar da mu da muke tare da shi duk mun tsira.