Na yi mamakin yadda Isra’ila ta hana mu makaman yakar Rasha – Shugaban Ukraine
Zelenskyy ya ce matakin ya daure masa kai matuka
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya ce ya cika da mamakin yadda Isra’ila ta ki ba kasarsa na’urorin kakkabo makaman yaki domin mayar da martani kan hare-haren Rasha a kan kasarsa.
Zelenskyy dai ya yi ta tambaya Isra’ila makaman tun da aka fara yakin a watan Fabrairu, amma ya ce sun kekashe kasa sun hana su.
- APC za ta bude yakin neman zaben Shugaban Kasa da addu’o’i na musamman
- Gwamnati ta tafka asarar N280bn a kudaden shigarta na watan Agusta
“Gaskiya ba san me yake faruwa da Isra’ila ba. Ina cikin mamaki, ban san dalilin ya sa suka hana mu makaman yaki ba,” inji shi.
Kalaman na shugaban dai sun fi wadanda ya taba amfani da su a watan Maris zafi, inda a nan ma ya caccaki isra’ilar kan jan kafar da take yi wajen ba su tallafin makaman.
Shugaban na Ukraine ya yi kalaman ne a wata tattaunawarsa da wani dan jaridar Faransa a ranar Laraba, wacce kuma ofishinsa ya fitar ranar Asabar.
Kasar Isra’ila dai wacce ta yi Allah-wadai da matakin Rasha na mamaye Ukraine, na taka-tsan-tsan da lalata alakarta da Rasha, wacce babbar jigo ce a yakin da ake gwabzawa a Siriya.
Kazalika, Isra’ilan ta kuma aike wa Ukraine da kayan tallafi sannan ta bayyana goyon bayanta ga mutanen kasar, kodayake ta ki yarda ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen kakaba mata takunkumi.
A baya dai Rasha ta zargi Isra’ila da mara wa masu burbushin akidar Nazi baya a kasar ta Ukraine.
Amma Zelenskyy ya ce, “Na fahimci [Isra’ila] suna cikin tsaka mai wuya a alakarsu da Siriya da kuma Rasha, amma ba zarginsu nake yi ba.
“Gaskiya kawai nake fada, duk wata tattaunawar da na yi da shugabannin Isra’ila babu wani abin da za ta tsinana wa mutanen Ukraine,” inji Shugaba Zelenskyy.