Na yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadu — Gwamnan Kano

Gwamnan Kano ya ce ya yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadu.

Na yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadu — Gwamnan Kano

Gwamna Abba tare da Nuhu Ribadu

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu a Abuja.

Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya yi muhimmiyar ganawa da Nuhu Ribadun.

Kawo yanzu dai ba a san abin da mutanen biyu suka tattauna ba, sai dai wasu na ganin ganawar ba za ta rasa nasaba da rikicin masarautu da ake yi a Kanon ba.

A ƙarshen makon da ya gabata ne mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam ya zargi Nuhu Ribadun da kitsa komawar Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero zuwa birnin, kwana biyu bayan da gwamnan jihar ya sanar da tuɓe shi daga sarauta.

Sai dai ofishin Ribadun ya musanta zargin tare da barazanar maka mataimakin gwamnan a kotu idan bai janye kalaman nasa ba.

Daga bisani dai mataimakin gwamnan ya janye kalaman nasa tare da bai wa Ribadu haƙuri, yana mai cewa da farko ba su fahimci yadda batun yake ba.