Na yi murabus a harkokin siyasa – Bamanga Tukur
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa, Alhaji Bamanga Tukur Tafidan Adamawa ya ce ya daina harkokin siyasa.Alhaji Bamanga Tukur ya bayyana haka ne a wani taron lacca da aka gudanar a kan cikarsa shekara 80 a duniya.A cewarsa, yanzu lokaci ne da ya kamata ya huta domin bai wa sababbin jini damar taka tasu rawar […]
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa, Alhaji Bamanga Tukur Tafidan Adamawa ya ce ya daina harkokin siyasa.
Alhaji Bamanga Tukur ya bayyana haka ne a wani taron lacca da aka gudanar a kan cikarsa shekara 80 a duniya.
A cewarsa, yanzu lokaci ne da ya kamata ya huta domin bai wa sababbin jini damar taka tasu rawar a harkokin siyasar kasar nan.
Alhaji Bamanga Tukur ya rike mukamai da dama a shekarun da ya kwashe yana siyasa, ciki har da Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola da kuma tsayawa takarar Shugaban kasa.
A shekarar 2014 ne ya sauka daga shugabancin Jam’iyyar PDP bayan ya sha matsin-lamba daga wajen gwamnoni da wasu manyan ’ya’yan jam’iyyar.