Na yi nadamar shiga aikin soja – Dattijo Audu Kawo

Ibrahim Idris wanda ake fi sani da Manjo Ibrahim, wanda ya yi yakin duniya na biyu, mazaunin BC5, hanyar Zango Aya Road, Kawo da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ya ce ya yi nadamar shiga aikin soja karshin Birtaniya da kuma Najeriya. A lokacin da aka dauke shi aikin soja sai aka canza masa […]

Na yi nadamar shiga aikin soja – Dattijo Audu Kawo

Dattijo Audu KawoIbrahim Idris wanda ake fi sani da Manjo Ibrahim, wanda ya yi yakin duniya na biyu, mazaunin BC5, hanyar Zango Aya Road, Kawo da ke karamar Hukumar Kaduna ta Arewa ya ce ya yi nadamar shiga aikin soja karshin Birtaniya da kuma Najeriya.
A lokacin da aka dauke shi aikin soja sai aka canza masa suna zuwa Audu Kawo. An canja masa sunansa ne don kada ’yan uwa da abokan arziki su fahimci aikinsa domin za su iya hana shi. Ya ce ya yi aiki tukuru da gaskiya amma sai aka saka masa da hana sh fansho. Abin bakin ciki da takaicin shi ne gwamnatin Birtaniya da kuma na Najeriya su hana shi fansho.
Audu Kawo mai jikoki 88 ya ce ganin an hana shi fansho ne ya sa ya hana duk wani nasa shiga aikin soja.
Audu Kawo mai fiye da shekara dari ya ce ya ba zai iya tuna duka abubuwan da suka faru da shi lokacin samartakarsa ba, amma duk da haka zai iya tuna irin rikon da kishiyar mahaifiyarsa ta yi masa lokacin da aka saki mahaifiyarsa.
Ya ce ba zai manta Dabid Isabel, mutumin da ya koya masa walda da Kanar Colley sojan Birtaniya da kuma kwararriyar maharbiya ‘yar kasar Burmese ba.
Ya ce wannan maharbiya ta sa sun kwanta a gonar shinkafa tsawon kwana 9. Ya kuma ce zai ci gaba da tuna hana shi fansho da aka yi.
Ya ce ya kasa fahimtar me ya sa shi da wadanda suka yi yaki don dinkewa da samun zaman lafiyar duniya da Najeriya aka hana su fansho.
Ya ce ya je Legas sau bakwai, ya kuma je Abuja sau hudu a kan maganar fansho amma duk a banza. Ya ce yana matukar shan wahala inda kudin magani ma ya gagare shi.
Tijjani Ibrahim dan gidan Audu Kawu ya ce mahaifinsa ya yi ritaya a shekarar 1985, ya kuma kware a walda.
Ya ce, a yanzu haka yana fama da ciwon kafa, amma wani lokaci idan ya tuna lokacin da yake soja sai ya mike ya rika zaga harabar gidan yana kuma wakar sojoji.
Ya ce: “An ajiye mahaifinsa a daki tsawon shekara 8 har mutane suna tsammani ya mutu.”
Ya ce, mahaifinsa yana da ’ya’ya 15 da jikoki 88 da tattaba-kunne 36.  Kuma su ne suka fara zuwa Kawo, yawansu ya kai 146.