Na yi nadamar soke zaɓen 1993 — Babangida
Babangida ya ce an soke zaɓen ne saboda Najeriya ba ta shirya karɓar mulkin dimokuraɗiyya ba.

Tsohon Shugaban Mulkin Soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce ya yi nadamar soke zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993.
Ya ce da zai samu wata dama da zai yanke wani hukunci daban.
- Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah
- Majalisa ta fara bincike kan zargin USAID na tallafa wa Boko Haram
Babangida ya bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘A Journey in Service’.
Yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ke nazarin littafin, Babangida ya amsa alhakin soke zaɓen da aka gudanar tsakanin Moshood Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) da Bashir Tofa na jam’iyyar National Republican Convention (NRC).
“Ina nadamar soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni. Na ɗauki alhakin matakin da aka ɗauka, domin hakan ya faru ne a ƙarƙashina ikona.
“Mun yi kuskure, kuma abubuwa sun faru cikin gaggawa,” in ji Babangida.
A baya, Babangida ya taɓa kare matakin soke zaɓen, inda ya ce an gudanar da shi cikin gaskiya da adalci, wanda a cewarsa Najeriya ba ta shirya karɓar mulkin dimokuraɗiyya ba a wancan lokaci.
“12 ga watan Yuni shi ne zaɓen mafi kyau a tarihin Najeriya—an yi shi cikin gaskiya da adalci. Amma abin takaici, dole muka soke shi.
“A lokacin, mun fahimci hatsarin miƙa mulki ga gwamnatin dimokuraɗiyya. Mun yi tsoron cewa idan muka miƙa mulki, cikin watanni shida, wani juyin mulki zai sake faruwa, kuma hakan zai zama gazawa a ɓangarenmu,” in ji shi.
Babangida, ya ƙara da cewa bayan soke zaɓen, gwamnatinsa ta shirya gudanar da wani sabon zaɓe a watan Nuwamban 1993.
Amma saboda tarzomar da ta biyo bayan soke zaɓen, ba a samu damar yin wani zaɓen ba.
A cewarsa a maimakon haka, sun kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, amma daga baya, Janar Sani Abacha ya hamɓarar da ita.