Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda
Ɗan Bilki ya ce ya yi nadamar yadda ya sadaukar da lokacinsa da dukiyar wajen mara wa Tinubu baya.
![Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/07/IMG_20240718_213327-scaled-e1721378176696.jpg)
Abdulmajid Danbilki Kwamanda. (Hoto: Aminiya).
Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya ce ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023.
Yayin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Kwamanda ya ce Shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu.
- Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi
- Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta
Ya bayyana cewa, a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba.
“Da ciwo, amma dole a faɗi gaskiya. Ni cikakken ɗan jam’iyyar APC ne, amma dole na amince cewa gwamnatin APC ta gaza a wajen ‘yan Najeriya.
“Na sadaukar da lokaci da dukiyata wajen shawo kan mutane su zaɓi jam’iyyar, amma a yau ina nadamar hakan,” in ji shi.
Kwamanda, ya kuma nemi afuwar jama’a, inda ya bayyana cewa abubuwan da ya musu alƙawari a kai za a musu, gwamnatin APC ba ta cika ba.
“’Yan Najeriya na cikin yunwa kuma suna cikin fushi. Ba su da tabbas kan tsaro, kuma mulki ba ya tafiya daidai.
“Yawancin mutane ba sa iya cin abinci sau biyu a rana,” in ji shi.
Ɗan Bilki Kwamanda ya yi ƙaurin suna wajen suka da yin adawa mai zafi a tsakanin abokan hamayyar jam’iyyarsa a Jihar Kano.