Na yi nadamar zama a Jam’iyyar PDP – Kyaftin Ningi

Wani fitaccen dan Jam’iyyar PDP da ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC Alhaji Abdulmalik Muhammed wanda aka fi sani da Kyaftin Ningi ya ce ya yi nadamar kasancewa a tsohuwar jam’iyyar tasa. Kyaftin Ningi wanda ya bayyana sauya shekarsa daga PDP zuwa APC, ya ce ya fahimci cewa Janar Muhammadu Buhari ne makaniken da zai […]

Na yi nadamar zama a Jam’iyyar PDP – Kyaftin Ningi
Na yi nadamar zama a Jam’iyyar PDP – Kyaftin Ningi

Wani fitaccen dan Jam’iyyar PDP da ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC Alhaji Abdulmalik Muhammed wanda aka fi sani da Kyaftin Ningi ya ce ya yi nadamar kasancewa a tsohuwar jam’iyyar tasa.

Kyaftin Ningi wanda ya bayyana sauya shekarsa daga PDP zuwa APC, ya ce ya fahimci cewa Janar Muhammadu Buhari ne makaniken da zai iya gyara Najeriya cikin kankanen lokaci idan aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa.
Kyaftin Ningi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Dandalin Ibrahim Badamasi Babangida da ke garin Bauchi a ranar Asabar da ta gabata, lokacin kaddamar da yaki neman zaben Janar Buhari.
Ya ce, “Na dauki tsawon lokaci a Jam’iyyar PDP amma sakamakon matsalolin tsaro da tashe-tashen hankula da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, daga yanzu ina sanar da al’ummar Jihar Bauchi cewa zan ci gaba da yayata manufofin Janar Buhari.”