Na yi sha’awar karatun aikin jinya a asibiti – Hajiya Hafsat

Hajiya Hafsat Liman, ita ce shugabar sashen biyan albashi na Kwalejin Kimiyya d aFasaha da ke Jihar Nasarawa, kuma ita ce uwargidan Farfesa I.M. Haruna na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. A hirar da ta yi da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta tare da shawarwari ga ’yan uwanta mata. TarihintaSunana Hajiya Hafsat Usman Liman. […]

Na yi sha’awar karatun aikin jinya a asibiti – Hajiya Hafsat

Hajiya Hafsat Liman, ita ce shugabar sashen biyan albashi na Kwalejin Kimiyya d aFasaha da ke Jihar Nasarawa, kuma ita ce uwargidan Farfesa I.M. Haruna na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi. A hirar da ta yi da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta tare da shawarwari ga ’yan uwanta mata.

Tarihinta
Sunana Hajiya Hafsat Usman Liman. Iyayena sun fito daga karamar Hukumar Nasarawa ne, a nan Jihar Nasarawa, amma an haife ni a garin Jos da ke  Jihar Filato a shekarar 1973.  A takaice, rayuwa na nagode Allah don ya taimaka dukkanmu ‘ya’yan mahaifin mu guda 18, mun yi makaranta. Sunan mahaifin mu marigayi Alhaji Liman Usman. Ya yi aiki da ma’aikatar Filaye da raya birane a jihar nan kafin ya rasu. Ya samu a makaranta. Ni makarantar da na yi ita ce Township Primary School da ke garin Jos. Da na kammala sai ya kai ni makarantar sakandare da ke karamar Hukumar Wamba a jihar nan, inda na samu horo kan malanta. Da na kammala sai na ci gaba da karatuna a makarantar Kimiyya da Fasaha da ke Kaduna, inda na so in karanta aikin jinya a asibiti (Nursing), amma da yake Allah bai nufe ni da haka ba, sai na karanta fannin kasuwanci, wato ‘Business Administration’. Sai dai ban ci gaba da karatu a makarantar ba, na dawo na kammala a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya da ke garin Nasarawa a a shekarar 1991. A makarantan ne Allah ya taimake ni na gama na samu difuloma dina a shekarar 2004. Daga nan sai na sake komawa makarantar, inda na ci gaba da karatu na na samu babbar difuloma, wato HND. Bayan na yi wa kasa hidima a shekarar 2007 a Kalaba. Na auri maigidana mai suna Dokta I.M. Haruna a shekarar 2001. Farfesa ne yana aiki da Jami’ar Jihar nan da ke garin Keffi, Tsangayar Nazarin Aikin Gona (Faculty of Agriculture). Ina da ‘ya’ya biyu Khadijat Ibrahim da AbdulRahman Ibrahim, wadanda duk suna makarantar sakandare a nan Lafiya.
A shekarar da aka kirkiro jihar nan ne, wato 1996 na samu aiki da ma’aikatar kudi ta jiha. Da aka kirkiro da wannan kwaleji ta Kimiyya da Fasaha na jihar nan, sai na sake samun aiki da su, inda aka ba ni mukamin shugabar sashen hada-hadar kudi  (head of finance account). Daga nan sai aka ba ni mukamin shugabar sashen biyan albashi (head of salary,) wanda yanzu haka ina rike da shi. Ofishin nan da kake gani,  a nan muke biyan albashin ma’aikatan wannan kwaleji.
Darussan rayuwa da na koya daga iyayena
A takaice dai halayen da na koya gun iyaye na sai dai in ce nagode Allah da irin iyaye da ya bamu. Kodayake mahaifiyata iliminta bai kai na mahaifi na ba, amma a  gaskiya ita ma ta taimaka mana wajen dawainiyar harkokin karatun mu. Shi dai mahaifin mu ya yi rayuwarsa ne da Bature ba da iyayen sa ba. Shi ya sa ya koyi halayen su, ya kuma koya mana. Idan da abin da ya kamata ya gaya maka, sai ya gaya maka. Ka gane ko? Ya ba mu kyakkyawar tarbiya, har muka girma, muka yi aure a hannunsa. Mahaifina kuma yana da wata akida da ke burge ni, wato ba zai yi wa ’yarsa auren dole ba,ita za ta zabi wanda takeson aura; kuma ba za ki kawo masa mutum sau biyu ba. Saboda haka dole ne ki tabbatar da mutumin da za ki aura kafin ki kawo shi gunsa. Abu na biyu kuma shi ne ba ki isa ki yi yaji ba a gidan mijin ki. Shi dai a rayuwarsa har ya koma ga Allah, ban ga wata ‘yarsa da ta taba yin yaji daga gidan mijinta, ta zo gida ba. Idan maganar abinci ce, idan kika zo zai diba abin da yake da shi ya ba ki, ya ce ki koma gidan mijin ki, amma idan shi mijin naki ya dawo ki ce masa ina son ganinsa. Haka muka tashi. A gaskiya iyayen mu sun yi mana tarbiya mai kyau, da muke tare dasu, kuma har girmanmu muna amfana da ita.

Daga John D. Wada, Lafiya

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi