Na yi shekara 15 ina ba da hannu ga motoci don taimako – Maidoya

Cinkoson ababen hawa ba sabon abu ba ne ga mutanen da ke zaune a birane inda kusan kowa ke da mota ko Keke Napep ko babur da na masu haya da za a ga ana ta guje-guje don zuwa wurin aiki ko gida, inda a kokarin yin haka ake yi dokokin hanya karan-tsaye.A tsakiyar birnin […]

Na yi shekara 15 ina ba da hannu ga motoci don taimako – Maidoya
Na yi shekara 15 ina ba da hannu ga motoci don taimako – Maidoya

Cinkoson ababen hawa ba sabon abu ba ne ga mutanen da ke zaune a birane inda kusan kowa ke da mota ko Keke Napep ko babur da na masu haya da za a ga ana ta guje-guje don zuwa wurin aiki ko gida, inda a kokarin yin haka ake yi dokokin hanya karan-tsaye.
A tsakiyar birnin Kaduna musamman ma ranakun aiki ana samun cinkoso daga shatetalen kamfanin buga jaridun  New Nigerian, zuwa yankin Mogadishu da Titin Muhammadu Buhari zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN) zuwa filin wasa na Ahmadu Bello zuwa mahadar Titin bashama da ya dangana da Tudun Wada da kuma yankin Kasuwar Sheikh Abubakar Gumi. Duk tsakiyar birnin Kaduna na cikin wahala saboda rufe titin Bidda inda hedkwatar ’yan sanda take saboda da dalilan tsaro.
Yakubu Maidoya mutum ne da ya saba barin barin wurin harkar kasuwancinsa domin bayar da hannu ga masu ababen hawa a kokrinsa na magance irin wannan cinkoso a hanya.
Duk da cewa Yakubu ya ce ba ya da mota ko babur, ya ce ba ya jin dadi ya ga cinkoson abubuwan hawa a kan hanyoyin Kaduna, wannan ne ya sanya ya ga ya kamata ya taimaka.
Hanyar da Maidoya ke ba da hannu wato mahadar Titin Muhammadu Buhari da na Bidda Road a kusa da Cibiyar ’Yan jarida ta Kaduna, hanya ce da manyan mutane kamar Gwamna da masu rakiyar motocin bankuna da sauransu ke bi. Kuma wannan bawan Allah ya yi shekara 15 yana ba da hannun ne saboda Allah ba don albashi ba.
Lokacin da wakilinmu ya hadu da shi yana ba da hannu rike da sanda a hannunsa, sai ya shaida masa cewa, saboda ba ya da kayan sarki na gwmanati ne ya sa a yanzu mahaya abin hawa ba sa tsayawa idan ya tsayar da su. “Musamman a yanzu da yaran masu hannu da shuni ke gudun wuce tsara a cikin gari.”
Ya ce saboda yana rike da sanda, ya sa wasu suke bin umarninsa don gudun kada ya yi musu barna ta hanyar fasa musu gilashi. Amma ya ce sandar barazana ce kawai.
Yakubu Maidoya ya ce yana yin wannan aikin ne kyauta ba wanda ya taba ba shi sisin kwabo balle gwamnati ta ce masa ta gode.
Yanzu dai akwai matasa da ke bayar da hannu a kan tituna da dama da ke garin Kaduna, musamman a mahadar Amigo da mahadar titin Katuru inda wani matashi ke bada hannu da tocila da daddare.
Idan za a iya tunawa a Tudun Wada, Hajiya Maimuna Gwarzo ta rika taimakwa wajen tsallaka titi da yara ’yan makaranta a shekarun baya, lamarin da ya jawo aka ba ta lambar yabo ta kasa ta MON a zamanin mulkin Shugaba Shehu Shagari, aka kuma sa wa makaranta sunanta aka kuma yi gadar tsallaka titi a wurin.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi